💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫_(Ni da Yarima)_😭
_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''
*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️M. W. A
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne
'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukar ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️*PAGE* 1️⃣0️⃣↪️2️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
"Kinga bani da lokacin ki in bazaki tafi ba Kinga tafiya ta"Khadija tayi tafiyar ta, ta barta a tsaye a gun, Habiba kallon bayan ta ta tsaya yi kana ganinta kasan tana cikin b'acin raai, sai Tace "zamu gani" a bayyane, ita ma ta bi bayanta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨Husnah tunda ta Fara gudu Bata tsaya har sai da ta Isa gida tana Isa gida ta nemi wuri ta zauna ta na maida numfashin gajiya, mahaifin ta ne ta fito da sauri don ya ji motsin mutum, ya na ganin ta yace "Husnah ta, Kece ba ko Sallama"
Shiru bata ce Masa komai ba kallon sa kawai take ta kasa magana da sauri ya karasa inda take, sai ta nuna Masa alamun ruwa, da Sauri ya debo Mata ruwa cike da kwanun Sha tunda ta kafa a kanta bata d'aga kanta ba har sai da taji kishin da take Ji ya gushe.Ajiye ruwan tayi sannan Tace "Abba mun dawo Amma an samu matsala"
"Matsala Kuma tame?" Ya samu wuri ya zauna.
"Abba Yarima fa Wai Ni ya zab'a"
Murmushi yayi har da Yar karamar dariya yace "Masha Allah kice Zan Zama surkin sarki Nan gaba""Oh Abba maganar Nan fa babba ne Kar Kaso ganin yanda sarkin ya Mana" Nan ta Sanar dashi, ransa yayi mugun b'ace yace "Basu wanda suka tab'o ba Ni sarkin yakin Kuri ne har yau ba a samu kamata ba, Kar Suga tsufa yazo min" Adda ya d'auka tana Masa magana Amma Ina yaki sauraron ta, bai tsaya ko Ina ba sai da ya Isa Deba, fadar sarki ya nufa, dake shi d'in sananne ne ba a Hana shi Shiga ba, Rai a b'ace yake magana "anci mutuncin mu sabida kawaii sun Zo taya Ku murna"
D'aya daga cikin fadawan yace "Kayi hakuri muma ba a son ranmu hakan ya faru ba"
Wani ma yace "Hakane yanzu duk Laifin murtala ake gani, gani ake kamar sun had'a Baki da Yar ka"Sarki da tun d'azu suke magana baice komai ba yayi gyaran murya sannan yace "dama ai bakin su a had'e" sai ya nuna d'aya daga cikin Yan yakin sa yace "aje a kawo min Murtala yazo ya rantse da sandan tsafin mu tun na iyaye da kakanni"
Cikin girmamawa ya amsa sannan ya wuce don ya kamo murtala, d'aya daga cikin fadawan yace "Ranka shi dad'e, dukkan mu nan mun San yanda sandan Nan yake kana da gaskiya ma ya aka Kare bare ace baka dashi Ni a ganina na a kyale shi tunda ya ce bai sanda hakan ba" sarki yace "Ai dama bazai fad'a ba ko don gudun Kar a hukunta shi yin hakan shine kad'ai zai say na hakura da abinda ya aikata"