💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫
_(Ni da Yarima)_😭
(_A love & a Sympetic story_)
'''Story and written'''
*By*
'''Fadeelah Yakub''' *(Milhaat)*
Wattpad @Milhaat🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION📚🖊️*
*M.W.A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu.💪🏻
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________
'''Wannan labari kirkirarren Labarine, ba yi shi don wata ko want ba, idan Labarin yazo dai dai da naka to akasi ne'''
'''Ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ba ta ko wani siga yin hakan babban kuskure ne.''' *don haka a kiyayye*_Ina godiya ga Allah daya bani iko da na fara littafin Nan, yadda na fara Lafiya ya Allah kasa na karasa shi Lafiya Ameen._
'''Wannan labarin Sadaukarwa ne ga masoyana,Allah ya bar kauna'''❤️
*PAGE* 1️⃣2️⃣0️⃣↪️1️⃣3️⃣0️⃣
Cikin tsawa bokanya Tace "Ke" Hafsah ji tayi kamar ta arce da gudu, Tace "Kin San Allah Kika Zo Nan? Kar ki sake Kiran sunan sa anan, Zan barki ne sabida wannan Ne zuwan ki na farko"
Kai a kasa Hafsah Tace "Godiya nake, dama so nake a zubar da cikin matar Yarima a Hana ta haihuwa, in so samu ne a lalata Mata mahaifa"Dariya bokanya tayi, ta Fara bubbuga kwaryar dake gaban ta.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Hafsah kallon bokanyar take, wasu Abubuwa take yi da hannun ta tana zazzaro idonunta waje tana magana ita kad'ai, bayan ta gama a tsawace Tace "Ke Yariinya"
Hafsah ta tsorata, sai ta kyalkyale da dariya sannan tace, "Bukatan ki baza ta biya ba"
A razane Hafsah tace "Amma meyasa?"
"Dalili kuwa shine dole sai ta haifi abinda ke cikin ta wannan ba haramin mu bane, duk Wanda yayi Kuskuren cutar da su babu gargada zai mutu tashi ki tafi"
Hafsah tace "Amma ya ka......"
Katsata bokanya tayi a tsawace tace "Nace ki Tashi ki tafi, ki dawo Nan da wata d'aya"
Hafsah bata so hakan ba ta tashi ta nufi gida Rai a b'ace.
Yarima na gani tsaye shi da Bello, Bello yace "Wannan labari ne Mai dad'i Ranka shi dad'e Allah ya sauke ta lafiya"
Yarima yace "Ameen ya rabbi, kaga na manta me kake ganin ya kamata a bawa Lantana?"
Bello yace "Yallab'ai ai matar Nan tana wahala sosai da ita da yaranta abinci Wannan da kyar suke Samu, ga ta da marayu,naji ance wataran haka suke kwana sai dai su Sha ruwa su kwanta,a gani na da abinci ya kamata a Kai musu"
"Allah Sarki har naji ba dad'i, daga yanzu ja tabbar basu kwana da yunwa ba, Amma yanzu ka Kai musu kayan abinci dayawa Wanda zasu shekara suna ci"
"Toh yallab'ai" sai yayi tafiyar sa don ya aiwatar da abin da yarima ya sashi yi.
Mama na gani zaune tana daka, sallamar Hafsah ne yasa ta d'ago kanta tace "Hafsah sai yanzu?Ya Yar uwar taki?" da gudu Hafsah ta karaso inda Mama take ta rungumeta Tace "Mama Albishirin ki" Mama Tace "Goro"
"Fari ko jaa?"
"Fari tass"
Murmushi Hafsah tayi tace "Toh Adda Husnah na da ciki har na tsawon wata biyu"
"Dan Allah dagaske kike?"
"Eh Mama da gaske nake tana chan ma tana kwance bata Jin dad'i"
"Allah Sarki ai dama wasu cikin tun yana karami yake wahalar wa, inshallah zata ji sauki"
"Allah yasa Mama don Ina so tamin takwara" Dariya Mama tayi tace "Kowa dai da damuwar sa,insha Allah gobe zanje na duba jikin nata"
"Allah ya kaimu,Mama barina watsa ruwa jikina duk ba d'adi"
"Toh shikenan sai kin fito" sai ta Shiga ban d'aki Mama Kuma ta cigaba da dakanta.
Yarima da Husnah na zaune a parlor, Ummi tayi sallama suka Mata izini ta shigo tace "Yarima Sarki ne yake neman ku da Kai da gimbiya"
Kallon juna Husnah da Yarima sukayi Yarima yace "Lafiya kuwa? Me ya faru?"
"Wallahi ban sani ba kawaii dai yace na Kira ku ne , suna tare da Sarauniya a fada"
Husnah Tace "Tashi kawaii muje muji ko lafiya" ta riko hannun sa suna tafiya suna hirar su har Saida suka Isa kofar fada ta sake hannun , Dariya yayi yace "Meyasa kika sake? dan Allah ki rike mu Shiga" Yana kokarin riko hannun ta, ta jaa da baya, hararar sa tayi ta yi murgud'a Masa d'an karamin bakin ta, yace "Ni kike murgud'a wa baki ko? Kar ki damu bashi Kika d'auka" tayi dariya, suna Shiga abba ya Fara Murmushi yace "Bismillah ku zauna" hakan suka yi bayan sun gaida shi Abba yace "Husnah ya jikin naki?"
Kai a kasa tace "da sauki Abba"
Yace "Masha Allah, Allah ya Kara sauki"
Duk suka amsa da Amin, Umma tace "Husnah yanzu kin daina jin komai ko?"
"Eh Umma"
"Ki fad'a min gaskiya Husnah in dai da kwai abinda kike ji ki sanar dani"
Abba yace "Sa'ah kenan Dan Allah ki bar yarinyar Nan tunda tace Miki taji sauki shikenan"
Murmushi Umma tayi tace "Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne fa rankashi dad'e, na ta'ba Shiga Irin wannan yanayin Kuma Husnah 'yatace Kar ka manta amanar muce Dole mu kula da ita"
Abba yace "naji naji" sai ya Maida kallon sa ga Yarima yace "Khaleed dalilin da yasa nace a kirawo ku shine, Ina so na sauka akan kujerar Nan, kaga lokaci yayi da yakamata ace nima na huta ko?"
Jiki a sanyaye Yarima yace "Abba tun yanzu? Dan Allah a karamin lokaci Ni ban shirya Zama Sarki ba" Murmushi Abba yayi yace "Khaleed kennan wani shiru kuma?"
"Abba ina ganin yanda kakeyi da mutane da ga Wannan matsalar sai waccan ka Zama tamkara alkali"
"Kar ka damu zan koya maka duk Abubuwan da ya dace, Kar ka damu"
Jiki a sanyaye Yarima yace "To Abba"
"Da yardan Allah Wata nai kamawa za'a nad'a ka,Allah ya muku Albarka tashi ku tafi"
Tashi sukayi suka nufi part d'in su, bayan sun Shiga d'aki suka zauna Husnah tace "Mijina" juyowa yayi ya kafa Mata Ido ko kifta su baya yi, idanun sa sunyi jajawur riko hannun sa tayi tace "Na lura tun sanda Abba ya fad'a maka cewar zaka Zama Sarki Naga duk yanayin ka ya canza, a tunani na wannan abun farin ciki ne gare ka da duk wani masoyin ka ko zan iya sanin dalilin da yasa yanayin ka ya canza"
Murmushin gefen baki Yarima yayi yace "Husnah baza ki gane ba, wannan kujeran da za'a bani zai Zama wani katangane a tsakani na dake" cikin Rashin fahimta take kallon sa girgiza Kan sa yayi sai yace "Husnah in dai na Zama Sarki bani da lokacin kaina bare naki,yanzu ne ya kamata na baki dukkanin lokacina, Amma bazaiyu ba kina gani Abba wuni yake a fada sai dare yake Shiga d'akin sa"
Ajiyar zuciya Husnah tayi ta Tashi ta zauna sannan tace "Ko kad'an banyi tunanin hakan ba, har naji ba dad'i Amma Yarima ya kamata ka sani sarautar Nan fa aikin lada ne in dai ka rike kujerar da zuciya d'aya Insha Allah komai zai tafi dai dai, sannan kasa a Ranka Husnah taka ce Kai kad'ai yanzu dai ba takara kake da wani ba bare kace za a Zo a kwace maka ni"
Murmushi yayi ya jaa hancinta yace "Ke dai kina da abin dariya, takara kam ba sai Nasa a b'alla Masa hakuri d'aya ba,Amma kinsan bana iya awa d'aya ba tare da na jiki akusa dani ba ko?"
"Na sani Ni kaina zai Zame min abu Mai wahala don na Riga na Saba da Jin ka a jikina, Amma ya kamata daga Ni har Kai musa a ranmu aikin lada ne"
Rungumar tayi yace "Ina Kaunar ki matata, Ina Kaunar ki kece Rayuwata da duk wani Jin dad'in da ke cikin ta, ya zanyi da Raina idan na rasa ki?"
Janye jikin ta tayi tace "Ya kuwa zakayi sai hakuri kasan idan ba tsufa akwai mutuwa ko?"
Yatsar shin ya sa abakin ta yace "Shhhuush Dan Allah Kar na Kuma jin irin maganar Nan a bakin ki"
Murmushi tayi tace "Amma kasan mutuwa fa dole ne ko?"
Hard'a hannayen sa yayi yace "Na sani Amma Dan Allah na roke ki ki daina"
Riko hannayen sa ta yi tace "Shikenan na daina Insha Allah bazan sake ba tunda farin cikin rayuwa ta baya so"
Murmushi yayi ya shafa fuskanta sai ya Kwanta a cinyar ta Yana shafa cikin ta, ta na shafo gashin kansa yace "Ya Babyna take?"
Dariya Husnah tayi tace "Take? Wa ya fad'a maka cewar mace ce?"
Dariya Shima yayi yace "Ina just jiki na mace zaki haifa mana, kyakkyawa kamar ki, Zan sonta fiye da yanda nake son Kai na"
Murmushi tayi tace "Kaga Ni Kuma na Miji nake so na Haifa na samu d'a Mai kamar uban sa,gwarzon na Miji son kowa kin Wanda ya rasa"
Dariya yayi yace "Husnah na dad'e Ina rokon Allah ya baki 'ya mace Insha Allah zai karb'a addu'a ta Kuma bazan daina ba"
"Ko ma dai mene ne Allah ya bamu na gari" ya amsa da "Ameen, Amma fa mace yauwa don so nake na sa Mata Suna *Nihaal* "
"Masha Allah Mijina har kasa naji Ina son na haifi mace sabida sunan yayi min dad'i sosai, ko da yake duk abinda zaka furta Mai dad'i ne"
" Ke dai kina son zugani"
"Ba zuga bane maganar gaskiya ce" sai ya riko kanta ya sumbace a goshi.
Nan suka cigaba da hiran su.
Hafsah tunda ta Shiga ban d'aki sai sake sake take taya zata b'ullo wa al'amarin Husnah a fili Tace "Wai ya ma za'ayi ace baza'a iya cutar da ita da abinda ke cikin ta ba, gaskiya dole nasan abinyi, Amma Bari na jira har sai na koma naji abinda rabaka zata ce in dai bata nema min mafita ba Wallahi Guba Zan sa Mata su mutu da ita da abinda ke cikin ta kowa ma ya huta" ta cigaba da wankan ta.
A yaune ake nad'in sarauta baki nesa da na kusa duk sunzo da yan uwa da abokanaN arziki aciki harda Khairat da mijin ta,Salma da mansur, Khairat ganin Husnah da ciki ba karamin murna tayi ba, Masha Allah komai ya tafi daidai yanda ya kamata anci an Sha, bayan an gama kowa ya koma gida.Husnah da Yarima Soyayyar su suke ci basu da wani tashin hankali Asali ma Soyayyar da sukeyi wa juna sai karuwa take, duk da baya samun lokaci sosai hakan bai hanshi kula da ita da abinda ke cikin ta ba. Wannan Kenan
Yaune ranar da ya kamata Hafsah ta koma gun rabaka tana ankare don bata manta ba a matse take hakan yasa tun safe tayi wa Mama karyar zata ganin Husnah, bayan ta Isa rabaka tace "na duba na gani ko da akwai abinda Zan iya yi Amma Babu, sabida yarinyar tana kula da ibadan ta bata Wasa da sallah da azkar sannan kullum cikin addu'a take wa d'an cikinta , ko ban fad'a Miki ba nasan kin San yanda addu'an uwa take ga 'ya 'yan ta"*SHAWARA GA IYAYE MATA DA MAZA YA KAMATA MU SANI ADDU'A SHINE MAKAMIN MUMUNI, IDAN KIKA KASANCE MAI IBADA SAI KI GA DUKKANIN SHARRIN DA AKE BINKI DA SHI BAZAI KAMA KI MU DAURE MU RIKA YIWA 'YA 'YAN KU ADDU'A TUN SUNA CIKI, SANNAN CIKI BA KOWA AKE FAD'AWA BA YA KAMATA MU SAN WANDA ZAMU FAD'WA WANDA YA ZAMA DOLE SU SANI, MISALI, MAHAIFAN KI DA NA MIJIN KI HAKAN MA YA WADATAR SAURAN MUTANE KUMA ZASU GANEWA KAN SU,ALLAH UBANGIJI YASA MU DACE.*
*AMEEN*Hafsah Tace "Hakan na nufin yanzu bukata ta baza ta biya ba?"
"Eh bazan iya ba"
Shiru Hafsah tayi a ranta tace "Ai akwai sauran gubar Nan da muka sawa Yarima ya saura, duk yanda zanyi sai na sa Mata a abinci taci ta mutu"
Wata iriyar dariya Rabaka tayi tace "Nasan abinda kike tsaka wa a ranki, idan Kika kuskura Kika ce Zaki aikata abinda kikey tunani yanzu asirin ki zai tonu ko Kuma ki mutu zab'i ya rage gare ki"
Hafsah tace "Dan Allah...."
Wani Irin kallo rabaka tayi wa Hafsah hakan yasa ta yin shiru ba shiri, cikin Rawar murya Hafsah tace "Kiyi hakuri so nake ki taimaka min"
Gyaran murya tayi tace "Zan taimaka Miki, Amma ki bani Nan da watanni shida"
Zaro Ido Hafsah tayi tace "Watanni shida? a lokacin fa cikin ya Kai na haihuwa, yanzu tana cikin wata uku"
Dariya rabaka ta yi Tace "Nasan da hakan, kije gida ki zauna ki jira lokacin yayi mahakurci mawadaci"
Ta amsa da toh, sannan ta Tashi ta tafi rai a b'ace.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Please comment and vote 🙏
