💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫_(Ni da Yarima)_😭
_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺
'''Story and Written'''
*By*
'''Fadeelah Yakub''' *Milhat*
08111791471
Wattpad @Milhaat
Please follow and votehttps://my.w.tt/JiNHZz9Y5bb?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''
*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️M. W. A
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne
'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️'''PAGE''' 1️⃣1️⃣0️⃣↪️1️⃣2️⃣0️⃣
Yace "Sannu Husnah me kike ji yanzu?Allah ya Baki lafiya, Bari nasa a Kira Miki Mai magani"
Kai kawaii ta d'aga Masa,Maii magani aka Kira don ta duba ta, da murmushi ta fito, ta kalli Yarima tace "Ranka ya dad'e Albishirin ka"
Yace "Goro"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Tace "Gimbiya Husnah tana da ciki har na tsawon Wata biyu"
Cikin rawar murya yace "Dan Allah dagaske kike? Kin tabbatar da hakan?"Tana Murmushi Tace "Eh Yarima"
Yace "Nagode Nagode insha Allah Zaki samu kyauta Mai tsoka sabida kin bani labari Mai dad'i"
"Godiya nake Yarima"
Yarima yace "anjima Zaki ga aika"
A hanyar ta na fita suka had'u da Sarauniya ta gaishe ta, sarauniya Tace "Yauwa kece Wacce kika Zo duba Gimbiya?"
"Eh Ranki shi dad'e"
"Mene yake damin ta Dan Allah?"
Tace "Ai ranki shi dad'e, ba wani damuwa bane ba ciki ne da ita, har na tsawon Wata biyu"Cikin murna Umma tace Tace "Dagaske kike?"
"Eh ranki shi dad'e"
Sarauniya tace "gaskiya naji dad'in Labarin da Kika kawo min, kije turakana ki jirini Ina Nan zuwa"
"Toh ranki shi dad'e."
"Kar fa ki tafi ki Jirani"
Murmushi tayi tace "bazan tafi ba"
Umma d'akin da Husnah take ta Shiga ta rarar Husnah na bacci, ta maida kallon ta ga Yarima sai washe Baki yake Yana aikin kallon Husnah, Umma rike hab'ar ta tayi Tace "Oh ni Yar su baka San Ma na shigo ba, yanzu Kai Khaleed a gaban Ido na kasa yarinyar Nan a gaba kake ta kallonta Kai ko irin kunyar Nan ma baka ji?"Tsotsa keya Yarima yayi yace "Toh umma ai mata ta ce, Kuma ke Mahaifiyata ce kunyar me zanji, ai Ina ga ko a gaban Mama hakan zanyi"
Yarfa hannu Umma ta Shiga yi, Tace "Au abun naka ma bai tsaya a iya kaina har Kan Mahaifiyar Husnah surkuwar kace fa"
Murmushi yayi yace"Umma kenan."Sallamar Hafsah sukaji , Yarima yace "Bismillah ki Shigo mana"
Hafsah na Shiga ta gaida su cikin girmamawa suka amsa, Hafsah Tace "Lafiya Naga tana bacci? Ko ba ta da lafiya ne?"
Yarima yace "Ai abin murya na ne ya faru, yau Mun Tashi da hannun dama"Cikin Rashin fahimta Hafsa ta ke kallon su sai Tace "Ban fahimta ba Umma me ya faru?"
Murmushi umma tayi tace "Yar uwarki Husnah tana da juna biyu"
Shiru Hafsah tayi ta ma rasa me Zata ce, Umma Tace "Hafsah ya dai na ganki haka Baki murna da cikin nata ne?"
Kirkiran Murmushi Hafsah tayi tace "A'a Umma kawaii dai abin ya bani mamaki ne, yaushe aka yi bikin har take da ciki?"
Murmushi Umma tayi Tace "hafsah Kenan yau fa watan su kusan Bakwai Kenan Kuma kice Wai yaushe a kayi, Salma fa yanzu cikin ta ya tsufa, Khairat Kuma har yanzu shiru"
Yarima yace "Umma ai wannan ba matsala bane wata bakwai ba shekara Bakwai bane ba"