CHAPTER ELEVEN

23 4 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺
'''Story and Written'''
    *By*
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
08111791471

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️

'''PAGE'''1️⃣0️⃣0️⃣1️⃣1️⃣0️⃣
Haba My Real Fans har yanzu fa bana ganin comments dinku yanda ya kamata.
'''PREVIOUSLY'''
Husnah tunda ta barsu su abba da Yarima bata wuce gida ba, cikin jeji ta Shiga ta nemi wuri ta zauna.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Husnah babu abinda zuciyar ta bai Raya Mata ba Mai kyau da mara kyau ciki harda kashe Kan ta, taci kuka sosai sannan ta Hora kanta da yunwa ba ci ba Sha sai dai takancin kayan marmari dake gun.

Abba da Yarima suka je Kashere sun dai dai ta abokin sa, sun yafi juna, Abdulrahman ba karamin dad'i yaji ba musamman da yaga abokin sa Yarima sun Kai kimanin shekara biyu basu had'u ba, Abdulrahman yace "Khaleed ya kamata mu kwana"
Sarki yace "yi hakuri Abdul zai zo a gaban Amma ya kamata mu koma gida don shirye shirye"

Sarki Musa yace "Hakane  Allah ya tsare sai mun zo" basu kwana ba su ka juya suka tafi sun tsayar da magana akan Sarki zasu zo neman auren Khairat.

Wannan kenan
Hafsat, Amina, Aisha, Zainab , fateema da Salma sunyi murna sosai sabida a yaune Yarima zaiyi zab'in sa.

Motsi Husnah taji a tsorace ta Tashi ta tsaya don taga ko wane ne, in Kuma abin gudo nake ta gudu ( Ni ko nace Husnah ke da kike son mutuwa me kuma na gudu? Ko ya kuka ce guys kamata ai ta tsaya ko? To muje zuwa)

Wasu mutane ta gani sun biyu dattawa ne don zasu haura shekaru arba'in, bata musu magana ba, tun daga nesa d'aya daga cikin su yace "Mutum ko Aljan?"
Cikin Rawar tace "Mutum Ce"

Suka matso kusa da ita D'ayan yace "Yarinya me kike yi a dajin nan Baki San akwai mugayen namomin jeji ba? Za su iya kashe ki ko gawar ki baza a samu ba"
Tace "Na sani so nake su cinye Ni"

D'ayan yace "haba ke kuwa me yayi zafi da har Zaki Ce haka?"
Tace "Gara na mutu ko Zan samu sa'ida Rayuwa cike take da abubu marasa dad'in ji da gani"
Murmushi mutumin yayi yace "Yaro yaro ne, to Munji fad'a Mana mene ne ya faru da har kike son kashe kanki Kuma ki fad'a Mana gaskiya in dai kin chanchani mutuwa sai mu bar ki anan"

Nan Husnah ta Shiga Sanar musu da dukkanin abinda ya faru tun had'uwar su da Yarima har i'zuwa dalilin ta na zuwa cikin dajin, a tare mutanen Nan suka ce "Alhamdulillah Alhamdulillah"
Cikin Rashin fahimta Husnah tace "Meyasa kuke hamdala?"

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now