CHAPTER SEVEN

19 3 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺
By
*FADEELAH YAKUBU* (Milhaat)
08111791471
*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️

'''PAGE''' 6️⃣0️⃣↪️7️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
Bello ya nufe shi da gudu ya na Kirin sunan sa amma ya Riga yayi Suma, Bello yace "Me Kika sa Masa a cikin abincin?"
Husnah kuka take sosai Tace "Wallahi ban sa mishi komai ba."

D'aga shi bello yayi ya nufi hanyar fita daga gidan, Husnah na biye da shi bello ya Nuna ta da Adda yace "Wallahi idan Kika bini sai na fille Miki Kai, ki koma" a tsawace.
Husnah ba don taso ba ta koma.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Kuka Husnah take sosai kamar ranta zai fita, sallamar Abba taji da gudu taje ta rungume shi tana Kuka hawaye da majina ya wanke Mata fuska Tace "Abba na Shiga uku, Abba Zan mutu"
Abba hankalinsa yayi mugun Tashi yace "Husnah me ya faru? Dan Allah ki Daina kuka hakan Nan, fad'a min me ya faru?"

Husnah Tace "Abba Khaleed, Khaleed"
Cikin Rashin fahimta Abba yace "Khaleed? Wai kina nufin Yarima?"
"Eh abba shi" ta amsa cikin Kuka, Abba yace "Har yanzu ban fahimce ki ba Husnah me ya faru?"
Cikin sheshshekar kuka tace "Abba Yarima yazo d'azu na Masa girki yana cikin ci ya Fara kukan cikin sa na ciwo kawai sai ya Suma" ta karasa maganar cikin kuka Mai cin raaii, Abba yace "Ya Salam ikon Allah,to ya Isa ki Daina kuka zai samu lafiya"

Husnah Tace "Abba idan ta mutu fa?"
Abba yace "Haba Husnah ai shi cuta ba mutuwa bace ba, insha Allah zai samu lafiya kinji?"
Tace "Abba naso na bi bayan sa amma Bello ya Hana Ni"
A razane Abba yace "Husnah Ashe Baki da da hankali Yana cikin wannan yanayin Zaki bishi, Ke kanki kin sani bayan Yarima sai bello babu Wanda yake sonki a garin bellon ma yanzu na San zai tsane ki don zai ce kece silar Rashin lafiyan Yarima,sai su cutar min da ke amma yanzu dai Dan Allah ki kwantar da hankali ki muyi ta Masa addu'a"
Jiki a tsanyaye Tace "To Abba"
Sai suka Shiga cikin gida.

B'angaren su Yarima suna Isa fada, ya kaisa d'akin Abba, Abba, umma da Khairat ganin Yarima cikin wannan Hali yasa su kuka, Abba ma karfin Hali yayi Kun San na miji da karfin Hali yake, Sarki ya bada izini a Kira Mai magani ba b'ata lokaci yazo ya duba yarima, wasu itatuwa da ganyayyaki ya jika sannan ya bud'e bakin Yarima ya zuba masa sai da ya tabbatar ya Sha yanda ake so, sannan ya aje kwaryar, ya maida kallon sa ga Sarki yace "Ranka ya dad'e insha Allah Yarima zai Samu lafiya Kar ku Tashi hankalin ku"
Sarki yace "To,to... Me ke damun sa me ya same shi?"
Murya kasa kasa yace "Guba ne Ranka ya dad'e"

Sarki gyara Zama yayi yace "Guba?"
Umma dafe kirji tayi Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un guba?"
Khairat hannu ta d'aura a ka Tace "Na Shiga uku"
Mai magani yace "Kar ki damu zai d'au lokaci Kan ya farfad'o Yana harar da shi shikenan"
Sarki yace "Ka tabbata zai Tashi?"
"Eh Ranka ya dad'e"
Rai a b'ace Sarki ya Shiga Kiran sunan Bello "Bello!!! Bello!!! Kana Ina ne?"
Cikin sauri Bello ya shigo d'akin, cikin girmamawa yace "Ranka ya dad'e gani"
Sarki yace "Ina kukaje?"
Kai a kasa Bello yace "Kuri mukaje Ranka ya dad'e munje gidan su Husnah"
Sarki yace "ehen ina sauraron ka sai akayi Yaya?"

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now