💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫_(Ni da Yarima)_😭
_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''
*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️M. W. A
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne
'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️*PAGE* 2️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
Husnah na gani zaune a cikin gida tana wanke wanke, Sallama taji kanta ansa sai taji inuwar mutum akanta da sauri ta d'ago ganin Yarima tayi a saye Yana kallon ta Yana Murmushi.Cikin sauri ta durkusa Tace "Barka da zuwa Yarima" kanta a kasa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yarima yace "Tashi, Tashi gimbiya matar sarki"Kasa d'ago kanta tayi yace Murmushi yayi yace "kunya ta kike ji?"
Kai ta d'aga Masa alamun eh, murmushi ya sake yi sai yace "Husnah haka ake tarban bako? Babu gun Zama bare ruwan Sha?"Da sauri ta mike Tace "tuba nake yallab'ai" Kai kawaii ya d'aga mata alamun ba damuwa,taburma ta d'auko ta shumfud'a Masa sannan ta Koma ta d'ebo ruwa Tace "Bismillah rankashi dad'e ka zauna"
Zama yayi sannan da bawan sa na tsaye a kansa,Yarima ya umurce ta da ta zauna a kusa dashi da fari taki ganin kamar baiji dad'in hakan ba yasa ta zauna, bayan ta zauna ya ce "Husnah nasan Kinyi mamakin ganina ko?"
"Eh rankashi dad'e" Kai a kasa."Husnah Kar kiyi mamakin ganina, ina matukar kaunar ki,Allah ne yayi halitta, halitarki daban ce cikin jinsin yan mata. Kina da faren idanu tas mai dauke da yalwatar bakin gashin gira, a kan su.Gaki da dogon hanci kamar ke kika wa kanki, dai dai tuwar labban bakin ki akan dogowar fuskar ki shi ya fito da cikar kyawun ki, ta yadda ko bakiyi kwalliya ba kyawun dirin ki hada da kyawun fuskarki shi yasa na fad'a tarkon son ki"
"Umm umm Yarima nagode sosai amma ina so kasani in da Wanda nake so Kuma yake Sona, kayi hakuri ka bi zab'in mahaifin ka dana al'adar mu"
"Husnah in dai Zaki karb'i Soyayya ta Sam bani da wata damuwa in Kuma matsayina ne bai Miki ba wallahi Zan iya ajiye shi don na rayu dake"
"A'a Yarima bado. Matsayin ja bane kawai ina son Sharif ba Kai ba, bazan cin amanar sa ba"
Jin hakan yasa Yarima yaji duk ba dad'i Amma Bai nuna Mata ba yace "Ki dai zauna kiyi tunani a Kai shi gaggawa aikin shaidan ne"
Tashi yayi ya ce "Na barki Lafiya" ya d'aga wa bawansa hannu sai suka yi tafiyar su, fitar su ke da wuya, naga wani saurayi wankan tarwad'a dogo ne sosai Mai faffad'an kirji, kyakkyawa ne Amma ko kad'an bai kamo kafan Yarima ba, Rai a b'ace ya shigo tana ganin sa tayi Murmushi tace "Masoyina Ashe Kai ne?"
