💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫_(Ni da Yarima)_😭
_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺'''Story and Written'''
*By*
'''Fadeelah Yakubu''' *(Milhaat)*📞08111791471
*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''
*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️M. W. A
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne
'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️Ga Masu tambayar daga farko ga link
https://chat.whatsapp.com/BTX3iMSweahFhRYGaSseHj
Amma Dan Allah idan kin San baza kiyi comment ba Dan Allah Kar ki Shiga.
Mata zallah pleaseNot edited
PAGE 4️⃣0️⃣↪️5️⃣0️⃣'''PREVIOUSLY'''
Isah duk da hakan shine plan d'insa Amma baiso ta dawo da wuri ba don surarta ya rikitar da shi ya ji Yana mugun Jin sha'awarta Amma dole ya hakura.Nan da Nan mutane suka cika gidan, Ana Allah ya wadaran da irin halinta.
Jiki ba Karfi Husnah ta Tashi ta tafi gida tana kuka, ga sharrin da aka Mata sannan ga duka.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Tana Isa gida tarar da Mahaifin ta a zaune da jiki a sanyaye murya chan ciki tayi Sallama, ya amsa "har kin dawo?"Ba Tace Masa komai ba, sai ya lura da jinin dake zuba a goshin ta da sauri ya tashi ya nufi inda yake, ga mamakin sa dukkan nin jikin ta ciwo ne, cikin b'acin raii da Rashin fahimta yace "Husnah me ya same ki? Waya Miki Haka?"
Kuka ta Shiga yi Mai cin Rai, Abba ba karamin rikicewa yayi ba don tunda yake Bai tab'a ganin Husnah na kuka Haka na ya ce "Husnah ki Sanar Dani me ya faru?"
Cikin muryar kuka Tace "Abba Meyasa? Meyasa sai Ni Abubuwa maarasa kyau ke faruwa Dani ne? Ko nayi wa Allah laifi ne?"
"Haba Husnah ki fad'a min me ya faru Kai tsaye ki daina jaan maganar"
Cikin kuka ta Fara msanar dashi abinda ya faru, Abba Nan da Nan zufa yake keto Masa jikin sa na kyarma, Bai ce mata komai ba ya fita Kai tsaye gidan Isah yaje a dai dai lokacin Isha ya fito daga wanka don jikin da duk a mace ganin Husnah da yayi, Abba riko Isah yayi da karfin gaske ya Fara Kai Masa duka tun Yana tsaye har ya Kai kasa Yana Kai masa naushi Yana ihu Abba ya toshe Masa baki duka yake Kai Masa sosai har sai da yaji ya gaji.
Matar Isah sallah take tana Jin ihun mijin ta Amma ba Hali ta taimaka Masa, sai dai Abba ya Masa tilis Kan yace "ka d'an ka gani Wallahi sai kashe ka idan baka fita days harkan 'yata ba."
Yayi tafiyar sa, ya bar Isah a kwance ko mutsi baya yi, da gudu matar Sa ta fito ta nufi inda Mijinta yake ganin yanda ya Masa jina jina ta Fara kuka magana take Masa Amma ya kasa Bata amsa da alama Suma yayi.