💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫_(Ni da Yarima)_😭
_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺'''Story and Written by'''
*Fadeelah Yakubu Milhaat**Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''
*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️M. W. A
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne
'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️
Wannan page naku ne
Ummu Abdallah
Mom jawwad
Nagode sosai Ina Jin dadin comments dinku Allah ya bar kauna'''PAGE'''9️⃣0️⃣↪️1️⃣0️⃣0️⃣
Sarki yace "Ku mika Masa sandar rantsuwar Nan in gaskiya ne Mahaifiyarta ta rasu gun haihuwa ne kamar yanda sukace zai tsira in ko ba Haka bane zai mutu yanzun Nan"Mika Masa akayi Abba yaki karb'a ya maida kallon sa ga Husnah Yace "Asma'u kiyi hakuri da abinda kunnuwan ki zasu jiye Miki yanzu"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Husnah tace "Abba ban fahimce ka ba meyasa kace haka? Bayan ka Sanar Dani Mahaifiyata ta rasa ranta ne a gun haihuwa ta?"
Abba yace "Husnah ba Haka bane, bani bane Mahaifin ki"
Dukka kowa na gun Saida ya gyara zama don Jin abinda yake Shirin fad'a.Cikin Rashin fahimta Husnah Tace "Abba kamar ta ba Kai ka haifeni ba"
"Ina nufin ke ba 'yata bace Ni ba Mahaifin ki bane"
Sarki yace "To a ina ka Samo ta? 'yar wace CE?"Abba yace "Na kasance Ina zaune ni da mata ta cikin garin Kuri shekaru talatin da suka wuce, Mun d'auki tsawon shekaru goma bamu samu haihu ba bata tab'a ko da b'ari ba Amma hakan bai sa na rabu da ita ko nayi tunanin Kara aure ba, Yan uwana kullum cikin tsamgwamar ta suke wasu suce Mata juya wasu Kuma suce Mata mayya, Ni Kuma Ina Kaunar Mata ta sosai sabida auren Soyayya mukayi da ita tun bani da komai har na Zama Mutum, bata da aiki kullum sai kuka a fad'in ta bata cika mace ba sabida ta kasa bani zuri'a gashi Allah ya d'aura min son 'ya 'ya, ganin yanda Mata ta take Shan zagi, da warayya acikin dangina hakan yasa muka bar garin muka koma Balanga cikin kauyen Talasse, garin wajawa anan muka zauna har tsawon wattani shida kullum cikin rokon Allah muke akan ya bamu haihuwa kwasam Rana d'aya Matata ta Sanar min da cewar tana da juna biyu har na tsowon wata biyu, tun daga Nan nake Bata kulawa na musamman nake tarairayan ta da abinda yake cikin ta bayan wata Tara ta haifi 'ya mace nasa Mata Suna Asma'u a ranar da akayi Suna Allah ya d'auki ran Asma'u, munyi kuka Ni da Mata farin cikin mu ya koma ciki na yi kokarin na cire abin a Raina Amma Matata ta kasa jurewa kullum cikin kuka take,hakan yasa na je gun Abokina Yusuf don neman shawara"
Nace Masa "Yusuf don Allah ka taimake Ni na rasa yanda zanyi da Zainab Bata da aikin yi sai kuka tun sanda muka rasa Husnah na kasa gane kanta"
Yusuf yace "Ya kamata ya kasance kullum kana tare da ita ka Rika Mata nasiha duk Mai Rai mamaci ne, sannan Allah da ya baku ita shi zai baku wata, tunda yanzun ma ai ba wayon ku bane ya baku"
