CHAPTER NINE

18 3 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺
*Fadeelah Yakub (Milhat)*
08111791471

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️

'''PAGE''' 8️⃣0️⃣↪️9️⃣0️⃣
"Kar ka damu nasa Hauwa tasa musu maganin bacci duk sunyi bacci, sannan zamu Isa in kuka gaisa sai mu dawo"
Yarima wani dad'i yaji, yaji Soyayyar da yakewa kanwar sa ya nin ku a zuciyar sa yace "Nagode Sosai Allah ya...."
Hannu Khairat tasa a bakin tace "Kayi shiru Yaya yanzu ba lokacin Godiya bane mu tafi"

Ta kofar kicin ta baya suka fita, suna fita sukaji muryar Bello yace "Ina zukuje?"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Yarima yace "Bello me kake yi anan? A tunani na nace maka kayi bacci ko?"
Bello yace "Yarima na fad'a maka umarnin Sarki nake bi"
Khairat Tace "Bello me haka? Har da kai? Yanzu fisabilillahi ba Kai ya dace ka taimaka Masa ba?"

Bello yace "Gimbiya umarnin Sarki nake bi, bazan Bari ku tafi ba sabida yarinyar Nan Zata cutar da shi"
Khairat Tace "Husnah baza ta tab'a cutar dashi ba saibada tana don sa, Bello idan baza ka goya Masa baya Kar Zama d'aya daga cikin Masu lalata musu Soyayyar ba, da Allah ka bari mu tafi"

Shiru yayi sannan yace "Amma dare yayi Kuma hanyar ba kyau"
Khairat Tace "Karka damu, babu abinda zai faru Allah Yana tare damu"
Yana kallon su Khairat ta rike hannun yarima suka tafi, suna Isa suka tarar da Abba nayi wa Husnah fad'a Akan ta Tashi taje tayi bacci, Tace "Abba Dan Allah ka barni na d'an Sha iska kad'an, Kuma Wallahi Abba bana Jin bacci ban San wani Hali Yarima yake ciki ba hankali na a tashe yake"
"Husnah hakuri zakiyi tunda an Mana iyaka da garin"

Muryar Yarima suka ji yace "Gimbiya ta Kar ki damu Ina lafiya Lau Babu abinda ya same Ni"
Khairat tace "Yaya ko sallama fa bamuyi ba muka shigo musu gida"
Murmushi Abba yayi yace "Kar ki damu Gimbiya ai Nan ma gidan ku ne"

Husnah tashi tayi ta tsaya kallon yarima ta kasa cewa komai , matsowa Yarima yayi kusa da ita yace "haba sarauniyar Mata ko sannu da zuwa ba za a min ba? Ko ba a farin ciki da zuwata ne?"

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta a kasa Tace "Mamaki nake Yarima cikin Daren Nan kazo, bakaji tsoron hanyar ba?"
Dariya yayi yace "Husnah Kenan Ni kai na ban San da zuwar ba, Mahaifina ya hanani fita Yana d'aya daga cikin sharud'an da ya gindayamin Kan ya sa aka barku, har na cire Rai da sake ganin ki, Amma Khairat ta taimaka min don nazo na ganki"

Husnah maida kallon ta tayi ga Khairat Tace "Gimbiya dagaske hakan ne?"
Murmushi Khairat tayi tace "Eh Hakane Husnah, gani nayi Hankalin say tashe baida walwala ko kad'an Ina son yayana Kuma Shima Yana Sona na tabbata Shima hakan zaimin ko fiye da haka farin cikin shi shine nawa"

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now