💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*
*Rubutu daga Alƙalamin.....* ✍️
✨ *RAHMA SABO USMAN*✨
*my wattpad*
*_@rahmasabo_*☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* ☀️
*SHAFI NA 27-28*
A tsakkiyar wani tanƙamemen falon wani danƙareren gida abin birgewa,da ke unguwar Banowa a ƙaramar hukumar Abadam ta maidugurin jihar Borno. Wata kamilalliyar dattijuwa ce ƴar kimanin shekaru hamsin ko za ta ɗara hakan dai jin daɗin da da ta ke ciki ba zai bari ka fuskanci asalin shekarunta ba,baƙa ce amma ba wuluk ba mai kykykkywar ƙira. Da alamun cikakkiyar ƴar gayu ce domin hannunta ya sha ado da zabba na ɗanyen zinare.
Ma'abociyar murmushi da son ƙawa ka na ganinta ka ga babarbariyar usil domin tribal marks(bille) da ke gefen chiks ɗinta zai bayyana maka hakan,ta na zaune akan ɗaya daga cikin danƙara-danƙaran kujeru ƙirar royal na ƙasar turkiya da su ka yi wa falon ƙawanya hannunta ɗauke da haɗɗiyar wayar tecno pova,ta na ƙoƙarin karata a kunnenta ga dukkan alamu kira ta ke yi,wayar na shiga fuskarta ma'abociyar murmushi nan ta tsume sak ta juye ta koma ta basawa cikin faɗa ta fara magana,"wannan wane irin shashanci ne za ki baro Kano ki taho har Maiduguri a public car?". shiru ta ɗan yi for a while ta na sauraron martanin ta cikin wayar,gwauron numfashi ta ja duk da haka muryarta da alamun faɗa ta cigaba da magana,"ok Allah ne kawai ya kawo ku lafiya,amma mustly drivers ɗinnan reckless driving (tuƙin ganganci) su ke,kuma kar ki sake ki baro motor park(tasha) domin yanzun zan turo yayanki Khalil ya ɗauko ki." Ba ta jirayi amsawar ta wayar ba ta datse kiran. Jinjina kanta ta yi, sannan kuma ta ƙara latsa wayar,"ka zo main palour ina son ganinka." Kawai abinda ta faɗa a taƙaice kenan,sannan ta katse kiran,cikin mintunan da ba za su gaza goma ba wani kyakykkyawan matashi ya yi sallama ya shigo cikin palourn kunnensa saye da abin ƙaro sauti(bluetooth) da alamar tarin nutsuwa da kuma sauƙin shirme da shiririta ga saurayin. Cikin alamun da ke nuni da tsantsar girmamawa ya russuna ya ce,"barka da gida Ammi." Cikin harshen barebari,"barka." Ta mayar masa a taƙaice cikin yaren da ya tambaye ta. Bai kai ga amsawa ba ta karɓe da faɗin", Abadam motor park za ka je, ka taho min da Ya gana." Sai da ya ƙara rissinawa sannan ya amsa da,"to Ammi." Cikin hanzari ya juya ya bi wata hanya ya fice. Bin shi ta yi da ido har ya fice,sannan ta miƙe ta na murmushi zuciyarta ɗauke da zallar farinciki da nishaɗin yau za ta yi tozali da ɗiyarta. Tunaninta mai za ta shirya mata na tarba,ta san ɗiyar tata bata da wani fav na abinci komai cinsa ta ke.Su na ƙarasowa ko kammala parking bai yi ba,ta diro daga motar zuciyarta cike da zallar farin ciki ta nufi hanyar cikin gida da gudu tun daga compound ta fara ƙwalla kiran Ammi. Ta baya ta ji an riƙo mata doguwar rigar da ke jikinta cikin masifa ana faɗin," to uwar rawar kai trolley ɗinki da ki ka bari a bayan mota wa ye ki ke tunanin zai shigar mi ki da ita cikin gida?" Cak ta tsaya da gudun da ta ke,ta kuma kafe shi da idanu. A cikin ranta ta na faɗin mutum ma ya je guri mai nisa ya dawo ba za a masa kara ba sai an nuna masa halin da na nan, daka mata tsawa ya yi ya ce,"ke! Don ubanki ba ki fahimci yarena ba ne? Kayanki na bayan mota waye zai ɗauke mi ki?" Cikin muryar kuka ta fara magana," to ba ga su Baba Mudi nan ba(mai bawa flowers ruwa."
Tun kafin ta ƙarasa faɗar sauran ya katse ta cikin salati,ya na faɗin,"tantirancin da ki ka koyo kenan? Su Baba Mudin sa'anninki ne kenan? Wane yaro ki ka taɓa gani ya saka su aiki a gidan nan? Kin wuce kin ɗebi kayanki ko sai na ƙaraso na ɓalla mi ki ƙafa?" Ya ƙarasa maganar ya na ƙara matsowa inda ta ke,sarai ta san halin yayyinta da mugunta yanzun nan mai ƙwatarta a gurinsa sai Allah da ma dalilin da ya saka ta tsaya musu da shi ta ga a baƙuwa ta ke tunaninta kewarta da ya ce mata ya yi a mota zai saka ya ɗaga mata ƙafa cikin sanyin jiki ta juya ta nufi gurin motar kafin ta ƙarasa ya buɗe mata shi kuma ya ƙarasa shigewa cikin gidan.Ta na shiga palour su ka yi arba da Amminta cikin sauri ta yada jakar da ke hannunta ta ƙarasa da gudu ta rungume ta,a tare su ka saki wata sassanyar ajiyar zuciya mai nuni da zallar soyayyar da ke tsakanin ƴa da uwar. Kamar ba za su saki junansu ba har tsawon mintuna sannan mahaifiyarta ta janye jikinta ta na faɗin," maza je ki toilet ki yi wanka,sannan ki fito mu yi lounch." Ba domin ta so ba haka ta cika ta,ba ta ko bi ta kan jakar tata ba ta nufi ɗakinta da ke up stairs.
Ba ta samu kanta ba sai dare,sannan ta ɗan samu nutsuwa domin kaf ƴan uwanta ke kusa sai da su ka zo ganin autar Ammi. Da ƴaƴansu da matansu ganinsu ya shagaltar da ita ga barin komai. Sai bayan isha gidan nasu ya ragu daga ita sai Amminta sai kuma wanda ta ke bi kuma abokin dabinta Ya Ibarhim Khalil. Ɗakinta ta shige sannan ta fara lalubar inda ta saka wayarta, a can saƙon tarolley ɗinta ta hango ta sai da ta yi murmushi sannan ta dauki wayar ta fara dubawa morethan 15 missed calls ta gani,wasu na Zainab sai rabi da heart beat ɗinta. Sai da ta kira Zainab su ka gama gaisawa su ka ɗan taɓa ƴar hira sananna ta kashe ta kira shi kamar da ba zai ɗaga ba don sai da ta kira shi kusan sau goma,sam ba ta taɓa gajiyawa da kiranshi ko da kuwa ba zai ɗaga ba. Ba kuma ta saka hakan a sahun wulaƙanci ta kan ayyana cewar uzuri ya hana shi ɗagawa.
Ya na ɗagawa ya fara complaining ɗin daga zuwanta gida har ta manta da rayuwarshi,haƙuri ta shiga ba shi ya haƙura da ƙyar sanannan ya sakko su ka fara shan hirar soyayya.Satinta biyu da dawowa ta na zaune,a palourn Amminta ta na yanke mata ƙumba kiran shi ya shigo nauyin Amminta ta ke ji don haka ta kasa ɗaga wayar har ta tsinke sai bayan da ta kammala mata ta shiga ɗaki kan stool ta zauna sannan ta ta kira shi abin mamakin da ya sanar da ita ne ya daskarar da ita a gurin da ta ke zaune.
*COMMENTS, VOTE & SHARE*
YOU ARE READING
SOYAYYATA DA SHI
Non-FictionLabari ne mai matuƙar rikita ƙwaƙwalwa,da kuma razana makaranci. Ya ƙunshi zallar rashin imani da son zuciya.