35-36

42 5 4
                                    

Kafin ya kai ƙarshe, ta jefa masa wani mugun kallo zuciyarta na bugun tara-tara wanda ya sanya shi gaggawar yanke maganarshi babu shiri. Ganin haka ya sunkuyar da kanshi ƙasa sannan ya cigaba da maganar da ya ke," tabbas lokaci na gudu,rayuwa na canjawa,al'amura na taɓarɓarewa,zukata na ƙara bushewa. Idan har ban karɓi gaskiya ba a yanzu to babu rana,wata ko lokacin da zan ɗanɗani zaƙi,ko kuma garɗin da ke cikin imani.  lokaci ya yi da zan musulunta domin samun rabauta da kuma hawa turba ko kuma tudun mun tsira." Ya na faɗin zai musulunta ba ta ma ji ƙarshen maganarsa ba ta ji wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta,duhun da ya sarƙe ƙirjinta gabaɗaya ya yaye ta na jin da sauri ta kalli fuskarshi ta ce,"ar u sure?" Gyɗa mata kai ya yi ya ɗan kashe idanu ya ce,"more than sure." Cikin hanzari ta miƙe ta na faɗin,bara na kaiwa Zainab albishir don ba zan iya murna ni kaɗai ba. Ai kafin ya yi wani yunƙuri har ta ɓace da ganinsa,a zaune a praying ground ta same ta ta na latsa waya da gudu ta ƙarasa gurin ta rungume ta baki har kunne ta ce,"Zainab albishirinki." Da sauri ta ɗago kai ta na murmushi ta na faɗin,"da alama ta samu kenan,to ba ni na sha." Sai da ta gyara zama kan carpet  ɗin gurin bakinta na rawa ta ce,"ya amince zai Musulunta." Waro idanuwanta ta yi cikin mamaki ta ce,"haba da gaske?"
"Wallahi da gaske na ke,yanzun nan ya sanar da ni." Ta ƙara tabbatar da zancenta,sai kuma ta gyra zamanta ta na faɗin,"to yanzun ya ta ina za mu fara? Kin san fa ba a bori da sanyin jiki". Dafa cinyoyinta ta yi ta ce,"ina Usman wannan cousin ɗin nawa?" Gyɗa mata kai ta yi alamun ta gane shi,ganin ta gano shi ya sanya ta cigaba da faɗin,"ai shine Naƙib(shugaban mssn)na wannan facultyn kin ga kayanmu ya tsinke a jikin kaba kenan."
"kira mana shi kawai yanzun kin san da zafi-zafi a ke bugun ƙarfe,kuma da safiya a ke kamun fara."
"Ok bari na kirawo shi a waya mu ji ko yana kusa." Ta ƙarasa faɗi ta na jawo wayarta da ke cikin jaka a kusa da ita,bayan ta kira shi ya ke sanar da ita cewa ai yana cikin faculty ɗin a lecture hall A17 ta zo ta same shi. Ta na jin haka ta miƙe ta na faɗin, "bara na je na yi masa bayani."
"Ok mu haɗu a can A17 ɗin". Gyɗa mata kai kawai ta yi sannan ta tafi.

Kiranshi ta yi a waya ta na cewa,"kana ina ne?"
Bayan ta yi masa bayani ya ce,"babu damuwa amma ina son abin ya zama secret don ba na son a yi exposing abun kowa ya ji,domin ina ji a jikina Momm ɗina ba za ta rasa waɗanda za su kai mata labari ba." Kwanatar masa da hankali ta shiga yi ta na cewa,"ya kamata fa ka fitar da dukkanin wani tsoro daga zuciyarka,ka saka a ranka cewar Allah ya na tare da kai kuma zai kare ka da dukkanin wani sharrin mai sharri."
"Na sani kuma ina jin hakan a jikina amma abun da na ke so ki fahimta shine,sharrin Bayahuden mutum a bun tsoro ne, domin ya zarta na dare idan ya tsala."
"Muje kawai ko ma meye Allah zai kare min kai."
"Ok". Ya faɗa sannan su ka miƙe a tare.

A zaune su ka same su da alamun tattaunawa su ke a kan mas'alar,su na shiga Usman ya hango su ya ɗan faɗaɗa fara'arsa ya na faɗin,"ai ga su ma sun ƙaraso."
"Allah ya ƙaraso da mu." A'isher ta faɗa ta na ƙoƙarin zama a kusa dawti Zainab,shi kuma Joseph miƙa masa hannu ya yi ya na faɗin,"barka da rana Ustazu (da ya ke haka ya) ke kiranshi da shi." Sai da ya amsa sannan ya nemi guri ya zauna,shiru ne ya ɗan biyo baya na ƴan wasu mintuna. Can Usman ya nisa ya fara magana ya na cewa,"yanzun nan Zainab ke sanar da ni wani abun alkhairi kan cewar ka na son Musulunta,tabbas wannan abu ne mai matuƙar sanyaya rai da kuma jindaɗi. Sai dai ina ɗan son na yi maka wasu ƴan tambayoyi."
"Ina jinka kuma Allah ya ba ni ikon amsawa."
"Tambayoyin  su ne: Menene dalilin da ya saka ka ke son Musulunci? Da fatan ba wani abin duniya ka hango ba misali alƙwarin kuɗi ko kuma mace wanda idan har ba ka shiga Musulunci ba ba za ka same su ba."
"Sai da ya yi tsai a ransa ya na jujjuya maganaganun sannan ya fara ba shi amsa," na zaɓi Musulunci ne domin ina ganin shine tabbataccen addini maras ɗungushe,na yi bincike iya bincike na gane addinin Islam ba shi da na biyu zallar gaskiya na damfare da shi. A kwai abubuwan koyi masu matuƙar yawa a cikin addinin,na gane cewa addini tsarkakke a gurin Mabuwayi shine Musulunci.
Ban hangi wani abun duniya ko wata mace ba,face zallar tsira da fatan dacewa da kuma neman ɗaukaka a gurin Allah. A tunanina iya ka waɗannan dalilan su ne su ka sanya ni na amsa kiran da wannan baiwar Allah ta yi min." Ya ƙarashe maganganunshi ya na nuna A'isher da kanta ke durƙushe ta na sauraron bayanansa. Tabbas kalamanshi sun tsuma dukkan wanda ke zaune a gurin domin jawabinsa cike su ke da zallar hikima da zalaƙa.
Ganin ya kai aya ne ya sanya Usman karɓewa ya ce,"madalla da hange mai kyau,hasashe mai kyau da haɗi da zaɓi mai kyau,yanzun nan zan biya maka kalmar shada idan ka shirya sai ka maimata."
Bayan ya faɗa masa ya maimaita a tare su ka yi kabbara,cikin matuƙar farin ciki Usman ya miƙe ya rungume shi ya na faɗin, "yanzun ka dawo ɗan uwa kuma abin so a gare mu". A'isher da ke gefe ita ma jinta ta ke tamkar ta tashi ta rungume shi sai dai babu hali,amma ta ke ta saki wani irin kukan daɗi,Zainab ma zuciyarta ce ta tsinke ta shiga taya ta,sai da su ka nutsu sannan Usman ya ɗora,"yanzun wane suna ka ke so a saka maka?"
"Sunan fiyayyen halittu."
"Muhammad kenan?" Ya tambaye shi domin tabbatarwa kai kawai ya gyɗa masa alamar ehhh,"daga yau ka dawo Muhammad mun taya ka murna." Daga nan ya ɗora da koya masa yadda zai yi wankan shiga Musulunci,abin birgewa shine tuni ma ya iya komai hatta da yadda zai yi salla ya iya. Umartarshi ya yi da ya yi maza ya tafi gida ya je ya yi wanka domin ba a son jinkiri.

VOTE & COMMENTS

SOYAYYATA DA SHIWhere stories live. Discover now