SOYYAYATA DA SHI

50 3 0
                                    

💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
     ( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )

*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*

*RUBUTU DAGA ALƘALAMIN......* ✍️

       ✨ *RAHMA SABO USMAN*✨

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*  ☀️
    ( *_Home of eloquent and trusted writers of the nation_* )
*SADAUKARWA GA A'ISHER RAWAYAU*

*SHAFI NA 17 - 18*

Ƙwarai ta ji tausayinsa,wani irin sonsa ta ke ji ya na narkewa a dukkan wani lungu da saƙo na jikinta. Kanta ya yi wani irin nauyi ta rasa abinda za ta tuna kawai kallonshi ta ke ita ma zuciyarta na mata suya. Wannan shine a ke kira da kuɗi ya yi gardama,domin ya kasa biyawa mai su buƙatun rayuwa ya gaza samarwa da mamallakinsa gatan iyaye da kuma na abinda kowa ke tutiya da kuma taƙama da shi wato addini mai tsabta maras datti ta yi Allah wadarai da rayuwar Patrick da ta Youhanas.

Cike da dakiya da ƙoƙarin kwantar da hankali ta shiga magana,"tabbas jin tarihin rayuwarka ya tsuma ni,ya kuma sanya na daɗa sakankacewa da jin kuɗi ba su ba ne jin daɗin da mutum ya ke nema a rayuwarsa ba. Mutum ya na neman soyayya domin ita ce mafi garɗin abubuwan garɗi soyayya kan sanya makaho mantuwa ko kuma makuwar a kan rashin wata gaɓa mai matuƙar muhimmanci wato ido.
Ta kan sanya talakan da ya fi kowa talauci jin cewar ya fi Ƙaruna dukiya,ta kan janyo rago ko kuma matsoracin da kiyashi kan gagareshi kashewa jin cewa ya fi Antaru jarumta. Na yi maka alƙawarin zan so ka zan kuma kula da rayuwarka fiye da yadda uwa kan kula da ɗan tayin da ke cikinta ko domin tsoron ka da wahala.
Zan jagoranci rayuwarka zuwa ga fitilar da bata taɓa mutuwa,zuwa ga haske mai kore dufunnai. Zan jaka zuwa ga kogin da ba ya ƙafewa,lambu da ba ya taɓa rasa kayan marmari. Zaƙin da ya ɗarawa zuma Musulunci addini gagarabadau halastaccen addini a gurin mabuyi ma mallakin mamallaka mabuwayi sarkin Sarakuna wato Jallah sarki Ilahu." Tana kaiwa nan ta ɗan tsagaita da maganar da ta ke,haɗi da furzar da sassanayar iska daga bakinta.
Tunda ta fara magana ya tsurawa fuskarta idanu,ya na hango zallar gaskiya abinda ta ke faɗa a ƙwayar idanunta. Ya na jin saukar furucinta har ƙasan zuciyarsa. Kunnuwansa na daɗa gasgata zance mafi daɗi a rayuwarsa,ƙwaƙwalwarsa na hango masa walwala da nishaɗin da zai tsunduɓa muddin ya same ta a matsayin matar aure. Rabon da ya ji daɗan kalamai tun rabuwarshi da Bilal tabbas yau ta dawo da shi duniyar da ya fidda ran sake shiga ya rasa ma wane kalamai zai faɗa mata su sanyata cikin nishaɗi da jin daɗi kamar yadda ita ma ta sanya shi.
Sai da ya aro jarumta sannan ya samu damar haɗa ƴan kalmomin da ke bakinsa,"kin gama min komai na rayuwa,kin faɗa min kalmomi masu matuƙar tsadar da ko ɗanyan Diamond ba zai iya siya ba. Kin sanarwa zuciyata abinda tun da na zo duniya ba a taɓa sanar da ita ba, ki sani cewa ba ni da bakin da zan nuna godiya a gare ki. Kalaman bakina ba za su taɓa iya biyan  zuciyarki kyautar da ta ba ni ba alfarma guda ɗaya ki sanar da ni abinda zan aikata a gare ki domin ya zamo tukuicin kyautayin a gare ni."
Murmushi ta yi sannan ta gyara zamanta, domin ta ƙara fuskantar shi sannan ta fara magana,"kai kuwa ka ke da kyautar da za ka sakamin,ka na da abinda za ka ba ni mana wadda kyawunsa da tsadarsa ya zarta zinare da azurfa". Cikin sauri ya katse ta ya ce,"gaggauta sanar da ni, Domin ki ga aiki da cikawa."
"kasan me ye buƙatata?"  Ta ƙara jefa masa tambaya.
"a'a." Ya girgiza mata kai cikin zaƙuwa domin burinshi kawai ta ƙaraso inda ya ke son zuwa.
"Burina kawai ka musulunta." Shiru ne ya biyo bayan tattaunawar ta su domin kowa da zaren da ya ke saƙawa a ranshi,ƙwarai ta zo masa da lamari mai girma wannan shine karon farko da a ka fara tallata masa addini,domin iya tsawon rayuwarsa da ya kwashe a duniya bai taɓa jin mahaifiyarshi na faɗawa ɗaya daga cikin yaranta ya shiga addininta ba wanda binkicen da ya yi ya gano cewa Yahudawa ba sa son addininsu ya ƙaru amma fa su na da burin ya danne kowanne addini a duniya. Mahafinsa kuwa shi kanshi lamarin addininsa bai wani ɗaɗa shi da ƙasa ba,tun bayan aurenshi da Tabita bai ƙara halastar church ba.
Ganin shirun ya yi yawa ne,ya sanya ta katse shi ta hanyar jefo masa wata tambayar,"da alamar na zo maka da al'amari mai girma ko?" Tamkar ta karanci zuciyata,ya faɗa a ranshi a fili kuma girgiza mata kai ya yi sannan ya ce,"ko ɗaya abinda na ke tunani shine,shi fa al'amarin addini ba sha'ani ba ne na gaggawa ba. Ina buƙatar da ki ɗan ƙara min lokaci in yi dogon nazari da binkice." Kallon tuhuma ta jefa masa,ta ce,"kai da ka ce kullum cikin binkice ka ke a kan addinai, to idan har da gaske ka ke ka amince da tayina mana." Kafin ya bata amsa su ka tsinakayi kiran sallar la'asar,cikin gaggawa ta miƙe ta na faɗin,"mu ƙarasa maganar bayan mun fito daga lecture." Gyɗa mata kansa da ya yi nauyi ya ke,ya na ƙoƙarin miƙewa daga durƙuson da yayi a cikin ciyayi.

Cikin sauri ta ke tafiya, domin ta san zuwa yanzun Zainab ta gama shaƙa. Sai yanzun ta duba wayarta ta ga ta yi mata  har five missed calls, hirar da su ke ba ta barta ta ga ko guda ba,balle dama wayar a silent ta ke.
A praying ground ɗin da ta barta nan ta isko ta,ta na shirin ta da sallar la'asar, tun kafin ta ƙarasa isowa gurin Zainab ɗin ta ce,"ke kuwa wani irin surutu ku ke yi,tun daga azuhr har la'asar ?" Sai da ta dire wayarta a kan jakunkunanansu da ke gefe sanan ta ce,"ke dai bari na idar da salla dogon labari ne." Ta na kammala faɗar haka, ta tada kabbarar salla.


*COMMENTS & SHARE*

SOYAYYATA DA SHIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin