31-32

33 4 5
                                    

💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
     ( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )

*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*

*Rubutu daga Alƙalamin.....* ✍️

       ✨ *RAHMA SABO USMAN*✨
  *my wattpad*
        *_@rahmasabo_*

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*  ☀️
  

*SHAFI NA 31-32*

Haka ta kwashe tsawon sati guda cikin wananan baƙin yanayi,babu mai yi mata magana hatta Amminta babu mai shiga sabgarta. Ganin haka ya sanya ta yankewa kanta hukuncin zaman ɗaka domin ta gaji da kallon tsanar da Amminta ta ke jifanta da shi a duk sanda su ka gamu. Shi kam da ta sanar masa bai wani girgiza ba domin ya tsammaci hakan daga kallon da Ammin tata ta watsa masa amma sai dai bai zata haka abin zai zo da wurwuri ba ya bata shawarwari da kuma kwantar mata da hankali,ya kuma ce ta ƙara haƙuri har zuwa sanda za ai resuming.

Daga gobe Sunday hutunsu ya ƙare,domin haka kwana ta yi kan darduma tana addu'ar Allah ya ɗora ta kan a kan ƴan gidansu su barta ta koma school domin ga yadda ta ke hasashen take-takensu za su iya dakatar da ita daga zuwa makaranta gabaɗaya hukuncin da ta ke ji mafi muni kenan domin shi kaɗai ne zai iya zamo mata  barrier daga ganin masoyi kuma abin ƙauna a gare ta. Cikin wata hikima ta ubangiji ta na tashi da sassafe ta isa zuwa bedroom na Amminta ta shaida mata za su yi resuming gobe domin haka a yau hutunsu ya ƙare babu musu Amminta ta yarje mata haɗi da faɗa mata da ta shirya zuwa yamma Yayanta yamma yayanta Khalid ya mayar da ita,wannan ita ce magana ta farko da ta shiga tsakaninta da mahaifiyar tata tun bayan zuwan Joseph kuma a ganinta ita ce magana mafi daɗi da kunnanta ya saurara tun bayan zuwa nashi.

Nasiha sosai Ammin tata ta yi mata lokacin da ta zo tafiya, mai nuni da zallar hatsarin da ke tattare da soyayyarta da arne ba kuma yanzun a ke ji ba sai zuwa gaba.
"Ya ce zai musulunta fa in sha Allahu." Abin da ta sanar da mahaifiyar tata kenan,kanta a durƙushe ta na wasa da bangles  ɗin da suka yi wa hannunta ƙawanya. Sai da ta ɗan yi murmushi irin nasu na manya sannan ta ce,"iyayensa musulmai ne?"
"a'a". Ta bawa mahaifiyar tata amsa tana girgiza kai.
"To abinda na ke hango mi ki shine ƴaƴanki,duk ranar da mahaifinsu ya rasu danginsa su ka karɓe yaran shikenan sun zama arna suma. Ni na zama kakar arna kenan ke kuma mahaifiyar arna,abinda zan gaya mi ki shine ki zaɓi soyayyar Allah sama da ta kowa domin haka Allah ya kiyaye hanya ya baki nasara a kan karatunki je ki na sallame ki kada dare ya yi mu ku a kan hanya."  Cikin sanyin jiki ta miƙe daga durƙuson da ta ke ta na gyra zaman jakarta da ke saƙale a baya.

Tun tana mota su ka yi waya da Zainab ta ke sanar da ita itama ta taho, domin haka za ma ta riga ta zuwa. Bayan yayan nata ya sauke ta shi ma nasihar ya ƙara yi mata. Ta na shiga hostel direct ɗakin Zainab ta nufa duk da ta san ba su ƙara yin waya ba amma ta san zuwa yanzun ta ƙaraso.
Tun daga bakin ƙofa ta fara yi mata oyoyo,da gudu ta ƙaraso ta rungume ta. Tayata jan trolley ɗinta ta yi su ka ƙarasa zuwa cikin ɗaki hannunsu na saƙale da na juna. A bakin gado su ka zube a tare sai yanzun Zainab ɗin ta kai dubanta zuwa ga A'isher a ɗan zabure ta ƙara kallonta ta na faɗin,"me ke faruwa da ke ne?"
"Me ki ka gani?" Ta tambaye ta cikin alamun rashin sani,"na ga kin yi baƙi kuma kin rame." Ta mayar mata da martani ta na ƙara ƙura mata idanu. Ƙwalla ce ta fara zubowa daga idanuwanta,domin haka cikin muryar kuka ta zayyane mata dukkan abinda ya ke faruwa. Dafa ta yi cikin sigar lallashi ta fara magana," A'isher wannan al'amari fa ba wani na tada hankali ba ne,dukkan iyaye na gari su ka samu labarin ƴarsu na soyayya da arne hukuncin da za su ɗauka a kanta kenan,ni yanzun shawarata a gare ki guda ɗaya ce ka da soyayya ta rufe mi ki idanu ta hana ki hango aibunshi duk da tarin aibun da ya ke da shi. Ki kara shi ya zo anjima ki sanar da shi cewar muddin bai musulunta ba za ki rabu da shi faƙaɗ."
Sai da ta ɗan jinjina lamarin a zuciyarta,ta na kuma hasashen zallar gaskiyar abin da ƙawar tata ta ke sanar da ita. Ci ke da gamsuwa ta gyɗa mata kai ta na faɗin,"tabbas zan bi shawararki." Wayarta ta zaro ta kunna sannan ta danna masa kira,"ehhh na shigo,mu haɗu da daddare pls." abinda kawai ta furta kenan sannan ta katse wayar,ta na miƙewa tsaye ta ce,"bara na je ni ma na ɗan kimtsa nawa kayan."
"Ok". Zainab ta mayar mata da martani a taƙaice.
Misalin ƙarfe takwas da rabi na dare(8:30pm) ya kira ta ya shaida mata yana ƙofar Gambo Sawaba,ƙaton hijabinta maroon calour ta zura ta fice. A saman mota ta hango shi ya na danna waya,bai san ta ƙaraso ba kawai sai ji yayi ta fizge wayar ta na faɗin,"ka fara sana'ar taka kenan". Dariya kawai ya yi sannan ya ce,"ki yiwa girman Allah ki bani wayata." Ganin ya gamata da girman Allah ne ya sanyata babu musu ta miƙa masa wayar,light ɗin wayar ya kunna ya na haska fuskarta ya na leƙawa,ɓata fuska ya yi ya ce,"ke kinga kuwa wani uban baƙi da ki kayi?" Kujerar cement da ke ɗan nesa kaɗan da su ta nuna masa da hannu ta na faɗin,"mu ƙarasa can gurin mu zauna ka ji bayani." Ta ƙarasa maganar ta na nufar gurin,babu musu shi ma ya bi bayanta.
Sai da su ka kammala zama,sannan ta kalle shi, ta fara magana cikin sanyin murya,"Joseph lokaci fa na daɗa tafiya,ruwa kuma ya na nema ya ƙarewa ɗan Kada,duk wanda na ambatawa cewa ina soyayya da wanda ba musulmi ba zallar hauka da kuma shirmena ya ke gani,ana yi min kallon wacce notinan kanta su ka kunce. A da can ban yarda ba sai a yanzun na farka na kuma gane gaskiyar magana,na kuma shirya rabuwa da kai muddin ba ka musulunta a kwanan nan ba." Ƙwarai kalamanta sun yi matuƙar girgiza masa ƙwaƙwalwa kansa ya ɗau charge,ya rasa takamaiman amsar da zai bata,cikin sanyin jiki ya miƙe tsaye ya na faɗin,"ki ba ni nan da zuwa Wednesday  za ki ji gamsassheɓ bayani." Bai bari ta ƙara cewa ko ƙala ba,ya nufi motarsa ko sallama bai yi mata ba ya juya a guje ya bar gurin.

Cikin halin ɗimauta,ta tsaya a gurin zuciyarta na hasaso mata abubuwa masu yawa. Ta na ji a jikinta idan har a kan ya musulunta ƙwara ya rabu da ita to ita ma ta shirya hakan,domin ta na son Allah da manzonsa fiye da kowane ɗan adam.


*VOTE,COMMENTS & SHARE*

SOYAYYATA DA SHIOnde histórias criam vida. Descubra agora