Ya na tsaye a gaban dressing mirror ya na gyra fuskarshi don yau Friday, ya k'uduruci aniyar zai je masallacin jumu'a haka kurum ya tsinci kanshi cikin farin ciki da nishaɗi wanda bai taɓa samun kansa a ciki ba lallai Musulunci haske ne. Kuma dukkanin wani jin daɗi da kwanciyar hankali na tattare da shi a cikinsa ne kad'ai za ka yi kyakkyawan barci mai tattare da nishaɗi da walwala.
Sauri ya ke ya kammala shiryawa domin ya je ya gana da abar ƙaunarsa rabonshi da ita tun shekaran jiya Laraba da su ka rabu sai dai kawai waya da su ke. Ya na jin matuƙar kewarta a ƙasan ransa ya kuma k'udurce yau zai yi mata kwalliya ta musamman don ta bashi abinda duk duniya babu wata mace da ta isa ta bashi ta jagorance shi izuwa ga haske wadda duhunta ba ya tab'a dusashewa,closet d'inshi ya nufa ya fiddo wata dakakkiyar shaddar senagal new design ya saka ruwan makuba(maroon colour) ta sha ɗinkin mr president style. Hannunshi ya sha haɗaɗɗen agogon rolex mai adon zaiba ya fesa turaruka masu tsada da matuƙar ƙamshi sama da kala goma jinsa ya ke tamkar wani asabon ango sai faman sheƙi ya ke da walwali tamkar wata ɗan daren goma sha biyar.
A gogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunshi ya kalla,da sauri ya ɗan ɓata fuska domin ganin ya kusa makara a gurguje ya jawo takalmin fata half cover ƙirar Idonesia ya saka a ƙafarshi ya zari mukkulin mota da wayarsa ya fice.A tsakkiyar garden ɗin gidan ya yi kicib'is da ita ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,ka na ganinta za ka hango zallar isa da kuma izza a fuskarta jikinta saye da doguwar rigar alhariri kalar sararin samaniya (sky blue)har k'asa hakan ya bawa k'afarta damar b'uya kykkyawa ce a jin farko mai d'an matsakaicin jiki ba za ka tab'a ganinta ka ce ita ta haifi zabgegen saurayi kamar Joseph ba sai dai kamarsu d'aya tamkar kaki ta yi ta ajje shi ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta na taunar tuffar da ke a jiye a basket kan wani k'aramin teburin gilashi. Tamkar ya ga wata dodanniyya ko kuma kashi haka ya ja ya yi turus ba don dole ba da ba zai taɓa bari su haɗu ba amma dole sai ya bi ta inda ta ke sannan zai samu damar ficewa sai da ya gimtse fuskarsa ya kawar da ilahirin murmushin da ke kanta sannan ya ce,"good morning Momm." Sai da ta ƙare masa kallo from head to toe sannan cikin basarwa ta ce,"Morning." Har ya raɓa ta gefenta ya ɗan shige ta kaɗan, kawai ya ji ta ce,"Joseph where ar u going?" Cak ya tsaya da tafiyar da ya ke yi ya na jinjina maganar ya yi a ransa domin idan zai iya tunawa ko kuma hasaso gaskiya tabbas wannan shine karo na farko da ta taɓa cigiyar ina zai je, _to ko dai ta gano ne?_ tambayar da ya yi wa kansa kenan tun da ya san masaniyar halayyar ɗan adam ce kan ya ankare har gumi ya fara karyo masa. Kafin ya amsa mata Allah ya yi serving ɗinsa ƙirrr wayarta ta hau ƙara ba ta ko bi ta kanshi ba ta bar gurin wayarta a saƙale a kunnenta.
Sai da ya saki nannuyar ajiyar zuciya sannan ba shiri ya nufi motarsa ya na addu'ar Allah ya ƙarawa wayar tata tsayi.Sai da ya sallaci Jumu'a a Markazul Imamul Bukhari da ke daura da sabuwar jami'ar Bayero, sannan ya k'arasa cikin makarantar. Ya na zaune a cikin mota ya na tsammatar fitowarta ganin ta d'an jima ba ta fito ba ne ya sanya shi sauke kujera ya jingina da bayansa ya na sauraron karatun k'ur'ani daga bakin Sheikh Maheerul mu'aik'ili wata sabuwar nutsuwa ke saukar masa jinsa ya ke tamkar babu wani a duniya bayan shi kad'ai. K'ofar da a ka k'wank'wasa ne ya saka shi d'agowa daga kwanciyar da ya ke, unlocking motar ya yi bayan ya kashe karatun da ya ke sauraro sannan ya bud'e seat d'in mai zaman banza ya tura kanshi waje ya na fad'in,"malama shanyar da ki kai fa ta jima da bushewa." Ta na tsaye hannunta na dama sagale da jaka ta sha katon hijabi mai kalar hanta, ta dube shi ta d'an rik'e hab'a alamun mamaki sannan ta ce,"auuu wai dama babu wanda ya kwashe min ai na d'auka ganin ban iso ba za a samu wani mai imanin ya tattare min ko don gudun ka da su zubo kasa." Ta karasa maganarta ta na danna kai cikin motar sannan ta zauna a gefenshi, d'an dukan sitiyari ya yi ya na dariya ya ce,"ai ba ki sanar ki na buk'atar a kwashe mi ki ba,amma duk tarin matan da ke karakaina a kan kayan naki da an samu wata ta kwashe. Amma babu komai tunda kin fad'a haka mu tara next time." Duka ta kai masa ya goce ya na dariya, gimtse fuskarta ta yi ta na fad'in,"duk ranar da ka yi wa wata kallon so ban yafe maka ba eheee." Kamo hannuwanta ya yi ya na murza y'an yatsunta da su ka sha ado da kyakkwan jan henna sai da ya kalli k'wayar idanuwanta yadda idanuwansu su ka had'e da na juna cikin shak'k'k'iyar murya ya fara magana,"ki saka a ranki ni naki ne babu abinda zai shiga tsakaninmu duk rintsi kuma duk tsanani babu macen da zan iya kallo da sunan so domin ni duk kallon maza na ke mu su, ke kad'ai k'wayar idona ke hango min a matsayin mace ki saka a ranki ni naki ne har abada. Kin shayar da ni zazzak'ar zumar da har na koma ga mahaliccina babu macen da za ta iya shayar da ni kwatankwacinta, kin tallafi rashin gatana kin mayar da ni cikakken mai gata kin tsamo ni daga datti kin saka tsabtataccen ruwa kin wanke ni ba ni da bakin da zan iya fayyace adadin kyautayinki a gare ni." Ya na kaiwa nan ya d'an tsagaita da maganarshi bayan ya saki hannunta,still dai idanuwansu na sark'afe da na juna. Wani irin maganad'isu ne ya taso tun daga k'afarta har zuwa k'wak'walwarta ganin ta na yawo a cikin gajimare ne ya sanya ta babu shiri ta yi k'asa da k'wayar idanunta ta zubawa ta mayar da kallonta zuwa ga gefen hijabinta a k'asan zuciyata kuwa kalamansa sauka su ke tamkar k'ankar a kan ciwo mai zubar da jini wani karaashi da tarin soyayyarsa ke dad'a bijiro mata. Bata da abin cewa sai da nuna godiya ga mahaliccinta domin rahamarsa ce ta saka shi yi mata wannan babbar kyautar kallonshi ta k'ara yi a karo na biyu ta ce,"in ye irin wannan kwalliya haka tamkar angon da zai shiga d'akin amrya."
"Ai na fi wanda zai shiga d'akin amarya don jina na ke tamkar jariri sabon haihuwa." Gyad'a kai ta yi cike da gamsuwa sannan ta ce",tabbas u'r born again kai da jariri sabuwar haihuwa marabarku k'alilan ce."
Su na tare da ita har a ka yi sallar magrib da Zainab ma su na k'ara koyar da shi wasu abubuwa da su ka shafi addini.VOTE & COMMENTS
YOU ARE READING
SOYAYYATA DA SHI
Non-FictionLabari ne mai matuƙar rikita ƙwaƙwalwa,da kuma razana makaranci. Ya ƙunshi zallar rashin imani da son zuciya.