35-36

20 4 10
                                    

Kwana ta yi kan darduma ta na salla,roƙonta shine Allah ya karkato da hankalin Joseph ya musulunta. Allah ya cire masa dukkan wani baƙin tunanin da zai hana shi ganin haske,ya share masa dukkanin wani dattin da zai hango wanda zai hana shi karɓar gaskiya.

Ba ta son ta rabu da shi domin ta na sonshi,iƙirarin da ta yi kawai ta na jin kamar daga shallow of her toungue ya ke  bai ƙarasa har ciki ba. Sai da ta yi sallar asubah sannan ta ɗan samu runtsawa,kiransa ya ƙara tada ta daga barci ta na jin ringing wayar ta tashi ta maka ta a silent domin ka da ta damu room mate ɗinta. Don ma Allah ya saka ba a gama dawowa ba tunda ba a yi fixing time table ba,barcinta ta juya ta cigaba da yi amma fa ƙasan zuciyarta na wani irin zafi tamkar ƙunar garwashi.



Shi ma ta ɓangarenshi haka abin ya kasance,kwana ya yi yana juyi a kan gado tunanin wannan issue  ɗin da ya bijiro masa da kuma hanyar da zai magance ta ya ke. Yana mtuƙar tsoron sharrin Bayahuden mutum,ya sani idan har ta samu labarin ya Musulunta tsab za ta iya kassara rayuwarshi. Za ta iya hana shi ganin haske a lamuranshi. Ya na jin dama bai kasance tsatsonta ba,da a ce ana iya biyan ladan haihuwa to da tabbas sai ya biya ta ladan tata dama kuma ba ta shayar da shi ba,balle ya ƙara da takaicin hakan. Ya na juyin a haka har barci ya yi awon gaba da shi duk da ba mai daɗi ba ne amma atleast ya ɗan samu peace of mind ya ɗan runtsa.

Bai tashi ba sai wajejen takwas saura minti biyar,(7:55am) ɗan miƙa ya yi ya zuro ƙafarsa gaban gado. Wayarsa ya ɗauka ya danna mata kira,kamar dai jiya 5missed calls babu amsa,jinjina kansa ya yi yana furzar da huci mai tsananin zafi. Jinsa ya ke tamkar wanda ya yi gudu a sahara desert,tsabar zafin da jikinsa da jikinsa ya ɗauka wanda ya bijiro daga myocardium of his hert. Da zai samu dama to da tabbas babu abinda zai hana shi zubar da hawaye irin na jiya ko zai samu sa'ida na wannan ibtila'in domin daga jiya zuwa yau zuciyarsa ta gama ƙeƙashewa.

Miƙewa tsaye ya yi ya nufi toilet,ya na fitowa ya shirya duk son kwalliya da ƙawa irin nashi yau kam ya haƙura kaya kawai ya saka. Sai turare da ya ɗan fesa,sauri ya ke ya je gurin Tabita domin sanin halin da ta kwana. Wanda ya san barcin da za ta yi ragagge ne,domin ba ta taɓa kwanciya barci sai a kan cinyoyinsa kuma tana farkawa shine mutum na farko da za ta fara tozali da shi.


Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya,in ji Malam Bahaushe na dauri mai ban haushi. Tabbas wannan batun haka ya ke ga dukkan wanda ya naƙalci kuma ya nazarci rayuwar ɗan adam. Duk abinda aka saka masa rana zai zo kuma ya wuce ka shirya ko ba ka shirya ba,Allah ba ya taɓa gagara da yin ikonsa komai nashi a shirye ya ke kuma a tsare ba ya taɓa fasa wanzar da abin da ya yi niyya.

Wayer garin Laraba tun safe ta ke tsammatar wayarshi amma shiru ka ke ji,tamkar Malam ya ci shirwa ta na son karya billenta ta kira shi amma ta na tunanin girmanta,ajinta da kuma ƙimar abin da ta kawo masa talla sun zarta hakan. Lamo ta yi a kan gadonta domin ta na jin yau ko area class ba za ta je ba,ta na jin tamkar ma wannan shine lokaci na ƙarshe da za ta yi rayuwa a cikin makarantar ya na gaya mata inda ya tsaya matuƙar ba tayinta ya karɓa ba za ta tattara nata-ya nata ta karɓi trans script ta bar makarantar dama ƙaddarar su haɗu ta shillo ta nan daga Maiduguri. Da waɗan nan tunane-tunanen ta miƙe daga kwanciyar da ta ke domin ta je ta yi brush ta kuma samawa cikinta da ke kururuwa tallafi.
Su na cikin tafiya da Zainab za su tafi class,tattauna batun su ke ta na sanar da ita cewar ga dukkan alamu fa ba zai taɓa lasar madarar gaskiya ba domin ya gaji ma ya daina kiranta a waya ya zaɓi rabuwa da ita da kuma zama a cikin duhun ɓata kenan,kamo hannunta ta yi tana lallashinta ta na sanar da ita gabaɗaya yaushe garin ya waye da har za ka zartar da hukuncin abinda zai faru a tsawon rana. Waye ya san me zai faru nan da ƙibtawar udanu ma? Babu shi idan ba Arrahamanu ba don haka su cigaba da dako da kuma jiran hukuncin Buwayi. Ba ta kai ƙarshe a maganaganun da ta ke mata ba wayar A'isher da ke riƙe a hannunta ta hau ƙara,a tare su ka kalli screen ɗin cikin tsammanin warabbuka murmushin da ke fuskokinsu ya ƙara faɗaɗa ganin sunan da ke yawo a kai HEART BEAT,sai da su ka tsaida tafiyar da su ke sannan ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta," muna hanyar zuwa nan." Shine kawai abinda ta ce sannan ta sauke wayar ta na kallon Zainab da ta yi mata ƙuri da ido ta na jiran labari,"ya ce mu haɗu a faculty." Ta ƙarasa maganar ta na jan hannunta domin su cigaba da tafiya,kowanne daga cikinsu gabanshi faɗuwa ya ke ba su san meye za su tarar ba.

A zaune akan mota su ka yi arba da shi,ya na ganinsu ya tsirgo ya na faɗaɗa murmushin da ke fuskarsa. Ba su tsaya kallon fuskarshi ba balle su karɓi saƙon da ya ke tarbar su da shi,jingina su kai a gaban motar suna facing ɗinshi da ke tsaya ɗan taƙi kaɗan da su. Gaisawa su ka yi da Zainab ya yi mata kallon ɗan ba mu guri mu zanta,kallon A'isher ta yi ta ce,"mu haɗe department idan kun kammala."

Shiru su ka ɗiba na ƴan wasu sakwanni,kallonshi ta yi ta na zumɓura baki ta ce," Malam ina jiran feed back fa idan ba ka da ta cewa kawai na ware,ka zo ka tusa ni a gaba ka na kallo kamar ka ga sabuwar halitta."  Cikin dariya ya ce,"abina da ke sweet heart azarɓaɓi,ba kya barin mutum ya yanke decision  cikin nutsuwa." Kwaɓe fuskarta ta yi ta na masa gatsine ta ce,"auuu haka ka ce? Idan ba ka da ta cewa ni ka ga tafiya." Ganin da gaske za ta tafi ya sanya shi gaggawar janyo hannunta suka nufi wani ɗan dakali a jikin theater J. Sai da su ka zauna sannan ya cika hannunta ya na faɗin,"tabbas na gama yanke hukuncin cewa....."


Vote & Comments

SOYAYYATA DA SHIWhere stories live. Discover now