SOYAYYATA DA SHI

29 4 1
                                    

💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
     ( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )

*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*

*Rubutu daga Alƙalamin.....* ✍️

       ✨ *RAHMA SABO USMAN*✨
  *my wattpad*
        *_@rahmasabo_*

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*  ☀️
  

*SHAFI NA 29-30*

Ƙwarai maganar da ya faɗa ta rikita ta,ba shiri ta yi hanzarin miƙewa jikinta ya na rawa tamkar mazari.
"Are u serious?" Ta tambaye shi tamkar ba ta ji mai ya ce ba, sarai ya san ta ji shi amma cike da mazantaka ya ƙara tabbatar mata,"yeah i'm serious." Ta rasa takamaiman kalmar da za ta faɗa masa, domin haka cikin saddaƙarwa ta ce,"to shikenan let me prepare." Wayarta riƙe a hannu ta fice,zuciyarta na ƙissima mata abubuwa da dama.
Kai tsaye palourn Amminta ta nufa,ta na shiga ta taras da ita a zaune a gurin da ta barta ta na kallon tashar sunna tv. Da sallama a bakinta ta shiga ta na faman sunkuyar da kai tamkar wata munafuka,Kan carpet ta nema ta zauna ta na kallon Amminta ta na ɗan murmushi. Ita ma murmushin ta yi ka na ta rage sautin talabijin ɗin da ta ke kallo,domin ta fahimci tunda ta shigo ta na sum-sum da kanta ta san da abinda ta ke buƙata cikin kulawa ta kalle ta ta ce,"auta me ke faruwa ne?" Sunkuyar da kanta ta yi ƙas ta na cigaba da murmushinta sannan ta ce,"dama wani ɗan makarantarmu ne da ya ke yi mana tutorial ya kira ni, ya ce wai ya shigo garin nan gidan wasu ƴan uwansu." Ta na kaiwa nan ta tsaya ta na ƴan soshe-soshe, kallonta kawai Ammi ta ke ta na shirin ta kai aya.
"ok ina jinki". Ta faɗa ta na ƙara kishingiɗa a kan kujerar,sai da ta ɗan yi jim na ƴan wasu sakwanni sannan ta ɗora,"to dama shine ya ce min zai biyo mu gaisa wai na bashi adress." Ta kai ƙarshen maganarta tamkar wacce a ka yi wa dole.
"babu damuwa ki bashi in dai kin yarda da tarbiyarsa." Ta na jin ta faɗa haka ta miƙe cikin hanzari,zuciyarta ɗauke da zallar farinciki da jin daɗin yau za ta haɗu da abin ƙaunarta.
Ta na shiga ɗaki ta ta faɗa kan gado,ta na murmushi tamkar wacce a ka bawa kyautar kujerar Makka. Wayarta ta ɗauka ta tura masa adress ɗin duk wanda ya nunawa zai fahimta kuma bugu da ƙari, ma gidansu ba ɓoyayye ba ne duk faɗin garin Maiduguri babu wanda bai sani ba. Mahaifinta shaharrren malamin addinin Islam ne kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Borno Sheikh Muhammad Sharif Fannami.

Tunda driver ya sauke shi a ƙofar gidan ya ke mamaki,anya kuwa nan ne gidan kar fa ya je shirme ya tafka domin yadda ya ke kallon rayuwar Aysher ba ta yi masa kala da wacce ta fito daga danƙararen gidan nan ba. Wayarsa ya fiddo ya danna mata kira domin ya tabbatar da gidan ya zo, umartar shi ta yi da ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa za su yi magana da mai gadi. Ya na zuwa mai gadin ya kalle shi cikin fara'a ya ce masa,"baƙon Hajiya ƙarama?" Gyɗa masa kai kawai ya yi,hallau dai ya na matuƙar mamaki. Bai gama tsinkewa  da al'amarin ba sai da ya shiga tsararren palourn gidan,ko shi da a ka haifa a ƙasar turai tsarin palourn nasu ya birge shi. Ya ƙara jinjina halin da kuma dattaku irin nata na rashin ɗaukar rayuwa da girma,tabbas tsarin rayuwarta na shige da na Bilal. Takunta ya jiyo mai cike da nutsuwa a hankali ta ƙaraso gurin da ya ke zaune hannunta riƙe da tray,tun daga nesa ya ke kare mata kallo yadda ta yi matuƙar fresh ta ƙara wani mugun kyau tamkar ba ita ba. Har ta ƙaraso inda ya ke bai daina kallonta ba,shi ma ya na jifar ta da arnen murmushin na yi missing ɗinki. Dire taray ɗin hannunta ta yi a kan center table sannan ta fara magana cikin shagwaɓa ta ce,"wannan kallon fa? " Kwaikwayon muryarta ya yi ya ce,"na missing ɗinki ne."
"Ba ka yi missing ɗina ba gaskiya,domin na ga yadda ka zama tulele." Abin ya bashi dariya sosai,domin haka cikin dariya ya ce mata,"me ye kuma tulele."
"Ka duba google." Ta mayar masa da martani cikin sigar rainin hankali, sannan ta matso da table ɗin zuwa kujerar da ya ke zaune,ita ma ta zauna kan ta kusa da shi sannan ta fara magana,"kar ka jani da dogon surutu malam ga abin motsa baki nan."  Bayan ya kammala, sun taɓa hirarsu me cike da ƙauna da kuma tarin shauƙi tamkar kada su rabu haka su ke ji a zukatansu. Jagora ta yi masa har zuwa palourn Amminta domin su gaisa,cikin kyakkyawan murnushinta ta tarbe shi ya zauna a ƙasa kansa ya na kallon carpet a hankali ya ɗan saci kallonta sai yau ne ya ga inda A'isher ta yo gadon murmushi tamkar ita sak haka ya ga Ammin tata. Bayan sun kammala gaisawa ne ta tambayi sunanshi domin ita kam bai yi mata kama da Hausawa ba sam,"Joseph". ya ce mata domin bai jin zai iya yi mata ƙarya domin ya samu karɓuwa,"Joseph". ta ƙara nanatawa cike da al'ajab,cikin sanyin jiki ya gyɗa mata kai domin ya fahimci bai samu karɓuwa ba a nan, shiru su ka babu mai cewa ko ƙala gajiya ya yi da zaman kawai ya miƙe ya fara mata sallama ta na daga zaune cikin halin ko in kula ta ce,"ka gaida mutanen gida."  Da kai shi ma ya amsa mata sannan ya fice,ita kuwa gogar ba ta fuskanci komai ba ta dai ga murmushin fuskar Amminta ya ɗan ragu amma hakan bai wani sanya ta ji wani abu a ranta ba. Sai da ta raka shi har gaban gate ɗin gidan ta na yi masa kallon zan yi kewar ka fa,shi ma irin kallon da ya yi mata kenan sananan ya fita daga gidan nasu.

Baya fa ta haihu a gidansu A'isher,domin ta na dawowa daga rakiyar tashi kai tsaye ɗakinta ta wuce ta na jin wani irin feeling na ratsa ta. Kan gadonta ta kwanta ta tada idonta ta na kallon ceiling iskar a.c na ratsa ɓargonta ta lula cikin duniyar masoya ba ta farga ba har aka turo ƙofar ɗakin a ka shigo. Amminta ce fuskarta a murtuke tamkar an aiko mata da mala'ikan mutuwa gefen gadon da ta ke kwance ta nema ta zauna sannan ta ce,"A'isher tashi za mu yi magana."Sai yanzun ta fahimci cewar a kwai matsala a cikin lamarin nan,cikin sanyin jiki ta kalli fuskar Ammin nata ta ce,"Ammi lafiya." Sai da ta ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa sannan cikin muryar da ke nuni da tsantsar fusata ta fara magana,"me ke tsakaninki da wannan arnen? Cikin gigita A'isher ta ƙara kallon mahaifiyar tata da ita ma ta tsare ta da kallon bani amsata. Cikin muryar da ke nuni da rashin gaskiya ta fara magana,"kamar yadda na faɗa mi ki ɗan ajinmu ne." gauruwar ajiyar zuciya Ammin tata ta sauke sannan ta  fara magana,"ni za ki rainawa hankali? Na haife da cikina amma za ki mayar da ni wata sauna ko an gaya mi ki ina shan weeds ne?(wiwi) to bara ki ji na fahimci tsagwaron soyayyar yaron nan a cikin idanuwanki,na fuskanci kina matuƙar sonshi ba wai dangantakarku a iya course mate ta tsaya ba ta kai har matsayin love relation ship." Ganin ta gano ta ne ya sanya kasa musa mata domin ta riga da ta san duk duniya babu wanda ya fahimce ta ko kuma halayyarta sama da mahaifiyarta. Ganin har yanzun idanuwan mahaifiyar tata na kanta ne ya sanya ta miƙa wuya cikin sanyin murya ta fara magana,"ehhh Ammi soyayya mu ke da shi." Ba ta kai ƙarshen kalamanta ba ta ji an wanke ta da wani gigitaccen mari da ya sanya ta fara ganin stars, dafe kuncinta ta yi ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro Amminta kuwa ko a jikinta bal ma cikin faɗa ta miƙe tsaye ta na nuna ta da yatsa ta na faɗin ,"mu za ki tozartawa ahali? Mu zaki wulaƙanta a duniya? Mahaifinki malamin addinin musulunci ne har ya rasu kuma kaf danginsa babu arne haka ni ma amma shine ke ki ke so ki jajibo mana arna a zuri'armu?". Ta rasa takamaiman kalamin da za ta yi amfani da shi domin ta rarrashe ta ta fahimci waye shi amma ta kasa faɗa kawai ta ke ta na faman kumfar baki tamkar za ta taune haƙorinta. Idanuwanta sun kaɗa sun yi jazur domin macece ita mai cike da sanyin hali amma fa idan ranta ya ɓaci bata iya fushi ba sam. Juyawa ta yi ta fice ta tafi ɗakinta ta ɗauki waya ta  kira Yayyunta guda biyu da su ke garin kasantuwar ɗayan ya na Jami'atul Islam,ta sanar da su A'isher na soyayya da arne. Ta yi kuka tamkar ranta zai fice daga gangar jikinta,ta na ji a jikinta tamkar an raba ta da ruhinta ne domin ita kam raba ta da shi raba ta da rayuwa ne. Yayyinta ma da su ka zo faɗan dai su ma suka hau yi,wai a matsayinta na ɗiyar babban malami kuma ƙanwar malamai amma ta rasa wanda za ta so sai arne dukkan tarin musulman da su ke garin nan. Yadda su ke treating ɗinta tamkar ita ma arniyar ce ita ana ta ganin babu wani laifi domin ka jawo wanda ba musulmi ba kuma ka nuna masa soyayya tabbas wataran zai biyo ka,zai bi addinin da ka ke muddin ba ka ƙyamace shi ba.

*COMMENTS, VOTE & SHARE*

SOYAYYATA DA SHIWhere stories live. Discover now