*SOYAYYATA DA SHI*
( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )*_GAJERAN LABARI MAI TSUMA ZUCIYA_*
*DAGA ALƘALAMIN BAKANUWA*
*RAHMA SABO USMAN**SHAFI NA ƊAYA*
Faculty of art and environmental sciences da ke jami'ar Bayero Kano. Department of Geography cikin theater H.
Theater ta yi tsit ana sauraron lecture,daga bakin DR Muhammad Bakori a darasinsa na EES 1301 level one fresh students. Theater ta cika maƙil da ɗalibai sama da ɗari biyar sabo da kasantuwar faculty course a ke yi.
Cikin nutsuwa ta ke sauraron lecture da alamu tana nishɗantuwa da abinda ake koya mata,kamar daga sama lecturer ya watso mata tambaya wani Equation ya rubuta ya ke buƙatar ta solver.Ya Salam ta furta a hankali tare da miƙewa tsaye cikin takunta mai ɗauke da tsantsar nutsuwa ta take taka step har zuwa gaban board ƙaton hijabine har ƙasa a jikinta ash colour na yadin moris mai hannu,haɗaɗɗen taransparent glass ne a idanuwanta takalmi low pass ne a ƙafarta shi ya sa babu jin takunta.
Sai da ta rissina sannan ta karɓi marker a hannun malamin hakan yayi matuƙar birge shi.
Cikin gwaninta,baiwa da kuma fikira ta fara solver math ɗin,a hankali ta kan juyo ta kalli ɗalibai ta yi musu bayanin procedures ɗin da ta ke bi tamkar dai itace malamar.
Ba ga iya ɗalibai ba hatta da malamin ta birge shi,tana kammalawa ta miƙawa malamin marker kallonta cikin kalaman da su ke nuna tsantsar jinjina ya ce,"thanks for your co-operation". Cikin murmushinta na gado ta mayar masa da martani ta ce,"thanks sir".
Ta tafi da imanin mafiya yawa daga cikin mazan dake class ɗin nasu,ana kammala lecture ta saɓi jakarta ta yi hanyar wani shop can kusa da Geology department wata muguwar yunwa ke nuƙurƙusar ta rabon ta da abinci tun jiya gashi kuma ta na da ulcer babu yadda room mate ɗinta ba ta yi kan ta tsaya ta yi break fast amma ta yi biris domin a rayuwarta babu abin da ta tsana sama da latti this attitude is running in her blood ba ta son a ɓata mata lokaci ita ma ba ta son ta ɓatawa wani.Snacks da lemon roba na c'mon ta siyo,sauri ta ke tamkar za ta kifa domin ta isa gurin da za ta ci. Can cikin wasu ciyayi ta samu gurin babu kowa don tun da suka fara lecture yau tsawon sati biyu a nan take zama ta ci abinci ta kuma yi karatu gurin shiru babu hayaniyar mutane yanayin da ta fi ƙauna kenan a rayuwarta.
Bayan ta kammala,tana ƙoƙarin zuge zip ɗin jakarta domin ɗauko littafin da ta ke jotting ta ɗan yi nazari ta hangi inuwar mutum a kanta. A firgice ta ɗaga idanuwanta sama ta yi arba da shi dogon saurayi ne kykkyawa ajin farko mai kwantaccen gashi da kuma yalwatacciyar suma ya sha shadda getzner brocade da kuma haɗaɗɗen agogo na rolex a ɗaure a tsintsiyar hannunshi lallausan ƙafarsa mai ɗauke da takalmi ƙirar italy ta nutse a cikin grasses sai da ta kammala ƙare masa kallo from head to toe.
Sannan ta kalleshi cikin murya mai nuna alamun zallar masifa ta ce,"Malam domin me za ka wani zo ka tsaya min a kai babu ko sallama". Kallonta ya yi cikin sigar rainin hankali ya ce,"amma da alamu ke ƴar level one ce ko?" Ƙwarai kalamansa sun yi masifar tunzura ta domin ta tsani rainin wayo don haka a tunzure ta mayar masa da martani ta ce,"a'a talla na kawo cikin makarantar nan,ina fatan za ka siya". Kalamanta sun ɗan so su bashi dariya amma ya gimtse,don bai son raini ko kaɗan taɓe baki ya yi ya ce,"ai dama kin fi kala da ƴan tallan any way". ya furta ya na ɗage kafaɗa sannan ya ƙara da cewa,"nan palace ɗina ne,ni ke zama a nan kullum". Ɓata rai ta yi ta mayar masa da martani ta ce",wannan kai ta shafa tun da nasan ai ba daga gidanku ka taho da shi ba". Kalamanta fa sun yi masifar tunzura shi don haka dolensa ya sanarwa yarinyar nan ko shi waye.
YOU ARE READING
SOYAYYATA DA SHI
Non-FictionLabari ne mai matuƙar rikita ƙwaƙwalwa,da kuma razana makaranci. Ya ƙunshi zallar rashin imani da son zuciya.