SOYYATA Da SHI

14 2 0
                                    

💗 *SOYAYYATA DA SHI* 💗
( *_Duk da kasancewar shi ba musulmi ba_* )

*_LABARIN GASKIYA MAI TSUMA ZUCIYA_*

*Rubutu daga Alƙalamin.....* ✍️

✨ *RAHMA SABO USMAN*✨
*my wattpad*
*_@rahmasabo_*

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* ☀️

*SHAFI NA 23-24*


A cikin Maiɗugurin jihar Borno, a ƙaramar hukumar Abadam wata unguwa da a ke kira da Banowa. Cikin wani danƙararen gida mai siffar birgewa,gidan ya tsaru matuƙar tdaruwa abin birgewa ga dukkan wanda ya tada ido ya kalle shi kuwa zai tabbatar da zallar kuɗin da mamallakin gidan ya ɓatar kafin ya mallaki wannan gida. Alƙalami ko kuma birona ya yi ƙarancin da zai iya zayyano muku fasalin kyawun da wannan gidan ya ke da kawai sai dai zan ɗan haɗa zukatanku da aikin hasko wannan zuƙeƙen gida.

A tsakkiyar ƙayataccen falon wannan gida kuwa,wata kamilalliya kuma haɗaɗɗiyar dattijuwa ce a zaune kan danƙareriyar kujerar zamani ta royal mai cin mutum guda(one seater) hannunta riƙe da wayar hannu (cellular) ta na magana cikin faɗa ta na cewa,"wannan wane irin shashanci ne,da zaki taho tun daga Kano a motar haya. Ba ki san kalar gangancin da ki ka ɗauka ba ko?" Shiru ta ɗan yi da alamar ta bawa ta cikin wayar dama ne ta kare kanta,cigaba ta yi da maganar da ta ke yi still(hallau) dai cikin faɗa ta na faɗin,"kar ki kuskura ki baro tasha a yanzun,domin zan turo ɗaya daga cikin yayyunki ya ɗakko ki." Ba ta tsaya jin cewar ta ɗaya ɓangaren ba ta murtsike wayar ta na jan tsaki,zuciyarta na hasaso mata zallar shirme da nuna halin ko in kula na ɗiyar tata. Ta na shirin ajiye wayar can teburin tsakkiya (center table) da ke cikin falon ta yi arba da ɗaya daga cikinta yaranta mai suna Ibrahim,kallonshi ta yi ta ce,"yaushe ka shigo ? Ko sallama babu." Cikin dariya ya fara mayar mata da martani ya na faɗin,"a'a Ammi tun ɗazun na shigo sai na taras ki na waya,sai faman faɗa ki ke yi ga dukkan alamun da wannan shashashar ɗiyar taki ki ke waya."





SOYAYYATA DA SHIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant