33-34

34 6 4
                                    

Tsananin gudun da ya ke,Allah ne kawai ya isar da shi gida lafiya. Bai gamu da accident ba ko kuma y'an karota su cafke shi.
Jinsa ya ke tamkar ba a duniya ya ke ba,ya rasa takamaiman tunanin da zai yi. Koma ya kalla duhu ke zuwar masa wannan shine karo na farko tun bayan had'uwarsa da ita da ya ji ya shiga wani k'unci. Ya na kammala parking motarsa bai ko kai ga kulle ta ba,ya nufi cikin gida,Tabita na zaune a palour ta na kallon tashar Zee world a gefenta mug d'in fresh milk ne ta na kurba cikin jin dadi.
Fuskarsa a murtuke ya shigo,bai ko kalli gurin da ta ke ba ya nufi part d'inshi cikin sassarfa tamkar zai yi tuntub'e. A firgice ta mik'e tsaye ta na kallonshi,"bro". Ta ambaci sunanshi ta na k'ara kallon fuskarshi.
"Yess". Ya fad'a a tak'aice ya na nufar k'ofar part d'in nasa, cikin hanzari da kuma tsantsar kid'ima ta bi bayanshi. Domin wannan shine karo na farko da ta fara riskar yayan nata cikin irin wannan hali. Duk wanda ya b'ata masa rai ita ce mutum ta farko kuma ta k'arshe da ya ke sanarwa, baya tab'a moye mata damuwarsa domin ta na ganin su kad'ai ne duniyoyin juna.
Ya na shiga d'aki ya fara safa da marwa,kansa na yi masa wani mugun zafi. A hankali ta shigo d'akin domin ya manta bai kulle k'ofar ba. Ganin halin da ta riske shi ne ya k'ara tada mata da hankali da k'arfi ta d'aga muryarta ta ce,"bross what's wrong with you? I'm totally scared" A tsakar kansa ya ji tambayar tata, cikin k'araji ya d'ago idanuwansa da su ka rine su ka koma jazur ya ce yana had'a hannayensa alamar magiya,"leave me alone pls!". Ya karasa maganar ya na mata nuni da hanyar waje. Ba musu ta fice  ta na gunjin kuka, domin ta gama tsorata da lamarin a nata tunaninta   ya fara tu'ammali da miyagun k'wayoyi har sun tashi zauta shi.

Ta na fita ya bi bayanta ya  dannawa k'ofar key, sannan ya dawo ya zame a k'as, ya kifa kansa a saman bed kawai ya saki wani mugun kuka maras sauti. Ya shafe tsawo 10 minute a haka  sannan ya yi shiru zuciyarsa na ayyana masa dalilin da ya sanya shi kuka tamkar wata mace, ya rasa dalilin da ya saka zuciyarsa ta ke suya, ya rasa me ya saka ta ke jin k'unci. Mik'ewa ya yi a hankali ya nufi bathroom domin ya watsa ruwa ya san wannan shine kawai dalilin da zai sanya shi samun nutsuwa har ya samu damar yanke decision(hukunci). A hankali ya ke lunk'aya a cikin ruwan da ya had'a a bahon wanka (jacouzzi) wanda ya sha had'in turaren wanka sama da kala goma. Nutsewa ya yi a kasan bahon tamkar wanda ya samu swimming pool, cikin hikima da k'udura ta Ubangiji nutsuwa ta fara shigarsa tunani ya fara zuwar masa a cikin ransa ya ayyana zab'i fa ta ba shi ba wai tursasa shi ta yi ba,d'an cije lower lip d'insa ya yi yana tuna yawan kyawawan  y'anmatan da ke karakaina a garin nan babu matayi ya san latsi d'aya za su bada kai,  kenan ko da ta rabu da shi zai iya samun dubunta,"mtsww!." Ya ja tsaki a ranshi ya na ayyana wannan ta faye azarb'ab'i da ta yi hak'uri ya kammala binciken da ya ke yi kawai ya na ganin time d'in rabuwarsu ne ya zo. D'an rufe idanuwanshi ya yi ya na watsa sassanyan ruwan a fuskarshi bayan ya d'ago sama, murmushin nan nata da baya tab'a yankewa a  kan adorable face d'inta ya hango da kuma wannan idanuwan nata masu matuk'ar maik'o da shek'i tamkar zaiba. Bai san sanda wani kyakkwan murmushi ya sub'uce a kan kyakkwar fuskarsa ba,a fili ya furta,"i can't leave you my charming princess i will  live with you till end of my journey u'r better than thousands of babes to me."  Tamkar wani zarrare haka ya ke sambatunsa,sanan kuna ya tuno yadda ta ke da aji, nutsuwa da kuma d'abi'u na gari  ga kuma tsantsar soyayyarsa da ya ke hangowa a  k'wayar idanuwanta duk da ya kasance ba milla guda su ke kai ba,"she's perfect." Ya k'ara furtawa a fili,bai san tsawon mintuna nawa ya kwashe a cikin bahon wankan ba amma ya san ya jima,realising ruwan ya yi sannan ya k'ara mai kyau ya d'auraye jikinsa ya fito. Ya na tsaye a jikin dressing mirror da hand darayer a hannunsa ya na busar kansa, Tabita ta fad'o masa a rai,tabbas ya san yanzun ta na can cikin tsananin damuwa tunda ya ke da ita bai tab'a kyararta ko yi mata tsawa ba. Ita ce farkon halitta a mace da ya ke so kuma ya tausawa a hanakali ya kai dubansa kan agogon bangon da ke dakin its after eleven ya san zuwa yanzun ta jima da yin barci da ya je ya rarrashe ta.
Ya na kammala dukkanin shirye-shiryensa ya saka pyjamas dinsa ya saka, sannan ya nufi kan bed hannunsa rik'e da laptop da kuma ruwan zafin da ya matso a disfenser. Allah ya so shi kafin ya fita sai da ya take cikinsa ba don haka ba da ya ya yi sallama da abinci for today. A hankali ya kalli screen d'in laptop d'in hotonta ne ta na murmushi jikinta sanye da bak'ar abaya ta yi rolling irin na larabawan k'asar Afghanistan,kawai tsintar kansa ya yi yana sumbatar allon kwamfutar, sannan ya bud'e ya fara research d'insa as usual. Ya na kan laptop din har around two, lumshewa idanuwansa su ka fara yi alamun barci, ga nauyin da kansa ya yi har yanzun bai saki ba. Ture laptop din ya yi gefe ya janyo wayarsa da ke kan bedside drawer, ya na k'ok'arin kiranta domin bai jin zai iya barci bai saurari cool voice dinta ba. Almost 3-5 miss calls ya yi mata ganin haka ya sanya shi wurgi da phone d'in a side, ya na k'imanta girman matsalar da A'isher za ta yi refuse na call d'inshi domin ko da zai kai four bai kira ta ba har sai ya kira za ta kwanta,"goshh! ." Ya furta ya na tab'a goshinsa da ya d'au zafi tamkar wadda ya ke cikin oven duk da a,c da ke aiki. Babu shiri ya jawo neck roll pillow ya tada kansa ya na kallon ceiling. Zazzafan tunanin  baƙar rayuwar da zai fuskanta nan gaba muddin ya ce zai Musulunta,tabbas ya kwana da masaniyar cewa mahaifiyarsa ba za ta taɓa barin shi ya zauna lafiya ba.

Ta na shiga hostel ta wuce d'akin Zainab kai tsaye, ta zayyane mata yadda su kai da shi. K'warai ta yaba mata ta kuma jinjinawa jarumtakarta domin ba kowacce mace  ce da ta yi nisa da nutso a cikin kogin soyayya mai zurfin k'afa dubu ba za ta iya d'ago kai domin ta shak'i iskar gaskiya ba.
"Maddala da wannan namijin k'ok'arin da ki kai." Cikin k'ok'orin k'arfafa guiwa,"madalla da k'awa ta gari, mai cike da kyautayi da kuma tarin  kamala." Ita ma ta furta mata, yayin da tq ke k'ara gyara zamanta kan d'an wani table da ke tsakkiyar dakin. Shiru ne ya biyo bayan y'an wasu sakwanni biyu,Zainab ce ta katse shirun ta ce,"amma fa ki sani wannan tamkar jihadi za ki yi don haka za ki iya encountering  a lot of obstacles, so you have to be brave and tie your belt to face everything that can block you to fulfil your achievement." Sai da ta saci kallonta ta tabbata hankalinta na kanta sannan ta d'ora da fad'in,"kar ki sake kuma ki d'aga wayarshi ko kuma ki bari ku had'u har sai ranar da ya d'iba mi ki ta zo, domin idan ku na waya zai iya karya zuciyarki ki janye kudirinki abu na karshe kuma ma fi muhimmanci shine ki dage da addu'a."
Tabbas a cikin kalaman  k'awar tata a kwai zallar hikimar da mai dimbin basira ne kawai zai gane,cikin gamsuwa ta shiga amsa mata da,"in sha Allahu zan bi dukkanin shawarwarinki in yi amfani da su har zuwa sanda zan kai ga gaci." Mik'ewa ta yi ta na mata sallama domin ta d'an gaji ta na son ta huta. Ta na ganin kiranshi around two ta tashi domin ta yi salla amma ta k'i d'agawa ya kamata ta fara koyawa kanta rayuwa babu shi, tun kafin tafiya ta yi nisa ya ce ya amince da sharad'inta cewar zai iya rabuwa da ita. Amma fa a a k'asan zuciyrta ta ke jin duk kira d'aya da ya yi, daga k'arshe d'aukar wayar ta yi ta rike a hannu ta na ganin sunansa na yawo a kan screen din zuciyrta na sanyi ta na jin ko banza ya damu da ita.

VOTE & COMMENTS

SOYAYYATA DA SHIWhere stories live. Discover now