BABI NA HUDU

10 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
 
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
      

         

         *BABI NA HUDU...!*

      *CIGABAN LABARI*
        

Yau litinin wacce ta kama sati gud'a kenan tunda muka rabu bata dadi ba da Dr. Mubeen awaya, Shi bai sake k'ira ba haka zalika nima banyi gangancin nemarsa awaya ba gudun kada ya raina mun aji, Abin haushi kuma abin dariya Suhaima wai ita alallai sai ta shiryamu, ganin hakan ne ya sanya na daina barin wayata anyhow ako'ina sabida at anytime tana iya daukakawa ta nemeshi wanda aganina idan ni na fara nemansa yawa ne babba, Ita Suhaimar bata da waya kasancewar Abbanmu nada ka'ida, ka'idar kuwa itace sai mutum ya kammala SS class d'insa kafin ya mallaki wayar kansa, rashin wayar ne ya sanya ta kasa samun hanyar daidaita tsakanina da my Mubeen, Idan kuka ganni awannan lokacin sai kun matuk'ar tausaya mun d'an komai ma da k'arfin hali nake yinsa, Damuwa ya taru ya mun yawa, gani nake k'amar na rasashi kenan har abada wanda nake ganin sam zuciyata bazata iya dauk'ar rashin nasa ba.K'iran Ummata ce ta katse mun 'yar gajeriyar tunanina, da murnata na d'anna receive tare da k'ange wayar akunne, nace"Assalamu alaiki ya Ummun Fadima"..daga d'aya b'angaren murmushi naji ta saki tace"Amin wa'alaikis salam d'iyar Kareematu 'ya ga Mai Nasara kuma 'yar gaban goshin k'annanta."Dariya na saki mai birgewa nace"Kai Ummun Fadima duk ni kadai? " Tace"Kin cancanci fiye da hakan d'iyar albarka " Cike da k'aunarta nace"Ina matuk'ar godiya Uwa da babu irinta "murmushi tayi tace"Ina autata da d'an sojana? "
      "basu wani jima da dawowa daga makaranta ba, autarki tana can tana sana'arta ta bacci, shi kuma sojanki yana dakin Karatu busy da aikin makaranta" Ahankali tace"Allah sarki Sojana akwai son Karatu, Su Suhaima basu dawo bako?"Nace"Eh su sai k'arfe hudu ai ko kin manta ne? "Tace"Ke kuwa ya za'ai na manta sai ki dunga gani k'amar kasuwancina na sanya na mantaku, Haba daughter ki gane mana cewar duk wannan fad'i tashin ina yinsa ne domin ku ya'yanah, Kinga dai mahaifinku ya kusa retire, kuma ni banason ya'yanah suzo nan gaba susha wahalar rayuwa, dalilin dayasa kika ga na dage da wannan kasuwancin kenan... Don Allah 'yar Kareematu ina bukatar goyon bayanki please, nayi miki alk'awari bazan tab'a watsa muku k'asa a ido ba "d'an yatsa na sanya na goge gutun hawayen daya d'igo saman kumatuna nace"Ummu Fadima ni kasuwancin naki bashi ne damuwata ba, ina dai so ki sani cewar mu ya'yanki muna bukatar lokacinki, kulawarki da kuma soyayyarki, kai infact Muna tsananin bukatarki kusa damu, mun amince Dad baya Samun lokacinmu, but Umma mun fi bukatarki sabida ke d'in uwace kuma tarbiyarmu tana hannunki, Umma ni kadai ba zan iya kula da tarbiyar k'annena ba duk da cewar na yabawa tarbiyar dukkaninsu, amma tarbiya da kulawar uwa ta musamman ce, Umma ki agaza mana muna tsananin bukatar iyaye ko daya ne akusa damu wanda zamu d'inga kai wa damuwar cikin sauri ba tare da mun jinkirta ba, ki duba fa kusan watanki daya a dubai baki waiwayi gida ba, Haba Ummu Fadima ko haka kukeson mu cigaba da gudanar da rayuwarmu ba kulawar iyayenmu ? Kodayaushe busy ?" Ajiyar zuciya naji ta sauke, tace"Daughter insha Allahu ina nan tafe nan da kwana biyu, Ki bari idan na dawo zamuyi magana Kinji ko? "..Cikin tsananin murna nace"Da gaske ? "Da gaske zan dawo acikin kwanak'i nan kusa, sai anjima ki kula da kannenki sosai, yauwa kafin in manta meyasa baki je makaranta yau ba ? Ko baki da lacca ne ?" Nace"a'a Umma muna cikin mid-semester break" Tace"Good, ki mik'a sak'on gaisuwata ga sirikina Haidar " Ban bata amsa ba sabida kunya, na dai ce"Bye mum" na yanke call d'in. Umma bata da labarin Dr. Mubeen, Leedar kawai ta sani wanda take masifar sonsa tare dani gashi ni kuma Mubeen nakeso wanda shi kuma nake ganin watakila na rasashi kenan har abada. Ganin ni kadai ke zaune afalo ya sanya na furta afili, "No Mubeen d'ina bazan tab'a bari na rasaka ba "
   "Shima d'in na tabbata bazai tab'a barin yaga ya rasaki ba idan akayi la'akari da irin son da yake miki yar'uwa"Da sauri na waiga don ganin wanda ke magana, ido hudu mukai da Suhaima wacce take shigowa, dawowarta kenan daga makaranta, "Yaya Fadima wallahi Uncle Mubeen shima yana masifar sonki da k'aunarki, Am sorry to say dukkanku kun kasa yadda da soyayyar da kukewa junanku ne shiyasa har kuke kokonto akai "Cike da mamaki na tari numfashinta"Taya akai kika san da hakan ? Kina cikin zuciyarsa ne ko kuwa baki ajiyar zuciyar tasa yayi da har kika gama yaddar wa kanki cewar lallai yana k'aunata ? in har da gasken yana k'aunata kamar yadda kika fad'a meyasa bai sake nemana ba ? Ni ban yarda da wani zancen kishi anan ba, kawai dama can ba sona yake tsakani da Allah ba "..K'arasa shigowa falon tayi har zuwa inda nake tayi cilli da school bag d'inta akan wani two seater, sa'annan ta fuskanceni sosai tana murmusawa, murmushin da bazan iya cewa ko na menene ba, tace"Sis kenan, bana cikin zuciyarsa kuma bai bani ajiyarta ba, amma inaso ki sani Mubarak na sonki, so na gaskiya yake miki d'an tun daga kan yadda yake sabunta salon soyayyarsa, kama daga kalamai, yanayin yadda yake b'atar da lokacinsa wajen baki kulawa shine zai tabbabtar miki da cewa lallai yana k'aunarki har zuciyarsa, kuma kishi asoyayya ai shine zai tabbatar miki da lallai mutum yana sonki da gaskiya, wanda kuwa baya kishinka to kiji da k'yau wallahi wannan d'in ba masoyinka bane, Ki sani Mubarak deserves you amma ba wannan d'an akuyan wai shi Leedar ba " Da azama na mik'e na dauketa da wani wawan mari ina huci na nunata da 'yar yatsa" kika sake zaginsa wallahi wallahi saina zubar miki da hak'oran gaba, yau ina son na sani wai shin bawan Allahn nan mai ya tsare miki adoron kasa ne ? Ya kashe miki iyaye ne ko wani da kike tink'aho dashi ? Ko kuma dai kun tab'a Samun wani d'an sab'ani ne da dad'ewa tun kafin haduwata dashi ? Suhaima Sa'ad kiyi magana ko mamak'in marin da nayi miki bai gama sakinki bane ? " zuba mun idanu tayi tana bina da kallon mamaki, ban damu ba na girgiza kai kana na cigaba" To kadan kika gani, next time da zaki sake zagarmun Haidar sai gidan nan ya mana kadan ni dake "
  Shanye mamak'inta tayi tasa hannu ta dafe wajen tana sakin gutun murmushi tace"Kika mareni akansa ?" Adakile nace"Eh kuma zan rama idan kika kuma, haba tsanar tayi yawa mana sai kace wanda ya kashe miki wani " murmushi mai zafi naga tayi still dai tana dafe da kuncinta tace"Da fari dai bazan tab'a daina tsanar Ali Haidar d'inki ba d'an kuwa duka Aliyu awurina daya suke, basu da imani, mayaudara ne kuma maciya amana ne, bai kashemun kowa ba haka zalika ban tab'a saninsa ba sai ta sanadinki, nasan kin cika da mamak'in ko wani laifi ne mai suna Aliyu ya tab'a aikata mun ne arayuwa da har yasa na tsani duka masu suna irin nasa, tambayar data addabeki kenan right ? Karki damu idan lokacin daya dace ki sani ya karato zan bud'e miki cikina kiji komai amma ba yanzu ba, sai dai ki sani har abada bazan tab'a daina tsanar Aliyunki ba muddin ba canza sunarsa yayi ba, kai koya canzan ma bana jin zan daina domin kiyayyar da nake masa ta riga ta gama tasiri ajinin jikina " Cikin zafin nama na sake mik'ewa na wanke mata fuska da mari nace"To idan bada tsanarsa aka halicceki ba to kisa tsinken tsire ki sokeshi ki ciro in ba haka ba zan baki mamaki agidan nan "
    "ai ni kin daina bani mamaki sai tsoro ganin tsegeran d'a namiji yana neman shiga tsakaninki da 'yar'uwarki, jininki " da sauri nace" ke dalla rufemun baki, Ni zaki rainawa hankali ? An gaya miki ban ganoki bane ko mai kike nufi ? Kawai just open up to me kice, yaya Fadima na fad'a tarkon soyayyar saurayinki Aliyu, am madly inlove with him amma kunyar yana saurayinki ne yasa na kasa bayyanawa shiyasa nake borin kunya na kafe da tsanarsa nake, wallahi da zaki fi wayau da hankali a idona amma ba wannan b'oye b'oyen da kike ba, kinga ma sai in bar miki shi idan har zai soki tunda ni na kama Mubarak in shi kuma ba tserewa yayi ba kenan " ina kaiwa nan na fashe da kuka wanda ban san kona menene ba,
    Kallona take Cike da mamaki hawaye duk ya gama wanke mata fuska, da rawar murya ta soma magana"Hasbunallahu Ya Allah! Hasbunallahu Ya Allah...Ya Allah kana kallo kuma kasan mai gaskiya atsakaninmu, Ya Allah ina rokonka ka gaggauta fitar da wanda ke acikin duhu tsakanina da 'yar'uwata " Kala bata ce mun ba ta dauki jakarta tana sharan hawaye zata wuceni, da sauri nace"Are you just trying to walk out of me ?" Murmushin takaici ta saki kan tace"a'a gwadawa zanyi dan zuciyata bazata iya cigaba da karban irin maganganun da kike sossoka mata ba, i can't endure it any longer Fadima Sa'ad "..K'ok'arin magana nake sai bata bani damar hakan ba, tace"please sis kindly get ur beautiful hands off me". Da sauri na sauke hannuna daga rukon dana mata, tayi murmushi tace"Thanks, ki huta lafiya. "tayi gaba na bita da kallon mamaki, har ta soma hawa matattakalar bene sai kuma naga ta dakata, ta juyo ta dubeni"Oh! Ya rabbi har zan manta, kinga na k'ira Mubeen kuma na wankeki agunsa sannan shima d'in yayi mun bayanin dalilin dayasa har ya kwashi tsawon Kwanak'in nan without calling or chatting u up... in takaice miki, yayi alk'awarin k'iranki yau idan har aiki ya ragun masa, d'an haka my dear na kashe wutar tunda dama can nice na haddasa gobarar, da fatar za'a daina mun wani gani ganin da akemun kwanan nan ?"Wani dadi naji ya ziyarci zuciyata amma sai na wayance nace"Meyasa zaki soma nemansa salon ya raina min class? Wama ya baki izinin dauk'ar wayata ni dama nake b'oye miki wayar kwanan nan sabida nasan zaki iya aikata kalar shirmen nan ? Karki k'ara bana so"Da sauri ta tari numfashina"Sabida kin barshi carelessly ne akan gado jiya kika shiga bandak'i, a guntun tunaninki ai ina dakin karatu kuma bazan shigo daki da wuri ba, cikin rashin sa'a sai na shiga dakin dauk'ar abu anan naci karo da wayar, hakan yasa nayi amfani da wannan damar na k'ira dan na daidaita tsakaninku... Sis my advice here,  ki rage girman kai dan tana iya cutar dake nan gaba, gashi  baki san dalilin dayasa tsawon k'wanak'in nan bai nemeki ba, ke azatonki kishi ne yasa ? to hasashenki bai yi daidai ba, ki nemeshi kiji it's very important, yanzu na daidaita komai dan haka ya rage gareki dashi, dan girman Allah ku cire Suhaima aciki "Azuciyata nace"Hmmm ji wacce take magana agame da girman kai... Yarinya kafin ki farga watakila lokaci ya k'ure mik'i, kayya ina jiye miki Suhaima, kina cikin halin kila wa k'ala "  Tana b'acewa ganina na rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya ina duban 'yan yatsuna"Na shiga uku, wai 'yan yatsun nan ne ayau suka sauka akan yar'uwata ? Mace mafi kusanci dani ? " dan wallahi ko Ummata bata kai Suhaima samun kusanci dani ba, dan kullum muna tare, ita kuwa Umma idan kun duba ba zama take ba.

*Ku muje zuwa har yanzu nace muku BA'A FARA BA ...*

*Meet the writer above the word's👇🏻*

*HAFNAN💜*








SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now