*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA GOMA...!*
Kallon juna muke cike da shauk'in so da k'auna, ayayin da kowannenmu da abinda yake ji azuciyarsa agame da d'an'uwansa.Adaidai lokacin kuma ruwan da ake ta tsulawa ya d'auke wanda bazan iya fadin awanni nawa aka dauka ana yinsa ba, amma abunda na sani dai shine mun dad'e Zaune acikin wannan 'joint' d'in.
Samin kaina nayi da katse mana wannan sweet moment d'in ta hanyar fadin"Mubeen pls tashi mu tafi ruwan ya tsaya don banga dalilin daya zaisa in cigaba da b'atar da lokacina anan ba bayan nasan da cewar ba aurena zaka yi ba..... " Na fad'i hakan in a romantic voice d'ina.
Da sauri ya tari numfashina"Says who?.... wallahi Zahra u ar the woman of my dreams...wlhy da'ace ni dake mun soma soyayya kafin Mummy ta kawo shawarar hadani da Hanan toh wallahi da ke kadai kawai zan aura.... Amma Allah shi kadai yasan daidai daya sanya hakan ta faru...dama can an riga da an rubuta cewar Hanan must be my first wife kafin ke becuz Zahra aurenki nake so nayi, sai dai idan kece kika gujeni... Amma fa ki sani cewar muddin kika gujenin, toh tabbas rayuwata tazo k'arshe..... "
Girgiza kai na soma yi ayayin da hawaye ke gangarowa saman cheeks d'ina, nace"No Mubeen d'ina daina fad'in hakan, Ka tuna Hanan da Jasmine ba zasu so su rasaka ba, kuma kai ma d'in ba zaka so ka gansu acikin kunci ba, Haka zalika nima bazan so na rasaka ba...amma the fact is that bazan iya aurenka ba Mubarak..... "
Cike da tashin hankali yace"Fadima idan har baki aureni ba toh wallahi duk wani masoyi na zai iya rasani...... " Ya fadi hakan cikin rawar murya, alokaci daya kuma naga yakai hannu ya dau wayarsa dake saman table din dake gabanmu.
Dialing wata number naga yayi tare da kange wayar akunnensa, alokaci daya kuma naji ya sanya wayar aloudspeaker ah sa'ilin da numbar wanda ya kira ya soma ringing alamar yayi nasarar samin wanda zai kira d'in.
"Hello hubbina" hakan naji an fada ah sa'ilin da wanda aka kira yayi picking wanda jin muryar da kuma sunan da aka ambato agareshi ya sanya nasan *HANAN* d'in ce ya k'ira.
"Naam Hanan.... ga antynki nan tace wai ita ba zata aureni ba sabida ina dake....... "
Da sauri na fizge Wayar na kange akunne, cike da tsiwa na soma magana"Sannu munafaka, duk naji irin taku kalar basajar da kuka shirya akaina, in ma tambayeki man, Ke wacce irin macece da har take goyan ma mijinta baya daya k'aunaci wata bayan ita har take burin ita wannan d'in ta zamo kishiyarta?.... Are u sure u are alright kuwa dan ni dai banga macen da zata taya mijinta irin wannan aika aikar da yayi ba wanda ak'arshe ke d'in zai cuta sabida idan ya aureni ba lalle ne ya kwatanta adalci atsakaninmu ba sabida yadda yake nuna miki tun ayanzu ya fi sona akanki... Yanzu so nake ki auna maganganuna ah mizanin hankali ki fada min ya kike ganin labarin zai sauya bayan ya aureni...?
Cikin shesshek'ar kuka tace"Anty nasan bayan ya aureki zan zama abar tausayi sabida yadda zai dunga fifita sonki afilli akan nawa... Nasan zan shiga cikin wani mayuwacin hali fiye da wanda nake ciki ayanzu amma farin cikin mijina ya fiye mun komai, banyi tsammanin zaki ga laifina don na baiwa mijina goyon baya akan ya auro wata bayan ni ba, Ni dai don Allah ki auri mijina don dake yake kwana azuciya kuma dake yake tashi da.... Mijina yana masifar sonki.... Mubarak d'ina is dieing for you, so pls Sister Zahra ki rayu da Abu Jasmine d'ina idan har kina kaunar ki cigaba da ganin farin cikinmu........"