*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA BIYU...!*
Ni sunana Fadimatu Bintu Zahra'u, cikakkiyar bafillatana ta asalin mutan Mayo Belwa dake jihar Yola,amma muna zaune acikin unguwar G.R.A Nassarawa dake agarin Zaria sabida yanayin aiki daya kawo mahaifana garin. Sunan mahaifina 'chief justice Sa'ad Muhammad Mai nasara'... Mahaifiyata Kuma Haj. Kareema Aliyu, iyayen nawa auren dangi sukai, 'yar d'a namiji da d'an d'iya mace suke. Mahaifina yayi zuzzurfan ilimi akan alk'alanci, tun daga kuruciyarsa agida da waje da Kuma taimakon mutane har zuwa matakin da yake kai ayau.Tsohon alk'ali ne fitacce Kuma shahararre wanda ya shahara kwarai akan aikinsa, wanda yasha gwagwarmayar rayuwa ah kuruciyarsa, ya Kuma sami kudi da suna ashekarun girmansa.Mun zauna agaruruwa daban-daban, kusan duk manya manyan biranen Nigeriya babu inda bamu zauna ba, kamun daga k'arshe muka dawo nan Zaria a inda Abba ke aiki da federal high court amatsayin Alk'ali wacce kasarmu ke tink'aho dashi domin kakaf Nijeriya babu wani alk'ali daya sha gaban Justice M sa'ad, da wuya Abba yayi fighting kan wani case kaga an bigeshi ya fad'i, akullum cikin nasara yake, dalilin daya sa mutane suka masa lak'abi da 'MAI NASARA' kenan, Kuma komai kan gaskiya da tsoron Allah yake yinsa.
Ita kuma Ummata shahararriyar 'yar kasuwa ce wacce ta shahara ab'angarorin kasuwanci daban daban, ta kan ketare zuwa kasashe da dama d'an zan iya cewa acan kasashen wajen ne take fita ta shigo da kayayyaki kamar su, gwala-gwalai irinsu daham da sauransu, kayan kitchen, manya manyan turamen zannuwa , takan had'awa mutane akwatinan lefe ma, kasuwanci dai take ba kama hannun yaro.
Iyayena 'yan dangi ne gaba da baya amma ba wani saninsu mukai ba kasancewar ba wani zuwa muke ba sabida yanayin aikin mahaifanmu da basa zama wuri gud'a musamman Abba, yau ana wannan gari gobe ana can, amma ga dukkan alamu nan Zariar itace zata kasance wajen zamanmu na d'ind'ind'in har yayi ritaya d'an akalla mun kwashi kusan shekaru bakwai anan d'in, Abba da Umma sukan dai yi aike na abubuwan alheri da yawa ko kuma su turamu muje ziyara idan har su bazasu samu zuwa ba kenan.
Mu biyar ne kacal da iyayenmu suka Haifa... Ni Fadima ni che 'yarsu ta farko, ina da shekaru ashirin da hudu aduniya kuma ni daluba ce amakarantar ABU ZARIA, ina karantar medicine 300l..Sai my masoyiya ko kuma ince my separate born twin sis wato 'Suhaima Sa'ad' ita ke bi mini, tana da shekaru goma sha tara aduniya,tana SS3, 'Lubna Sa'ad' ke bi mata, shekarunta goma sha hudu tana Jss3, Sai 'Umar Faruk Sa'ad' mai shekaru goma a primary 6, Sannan autarmu mai sunan mahaifiyar umma wato 'Maryam Sa'ad' amma muna kiranta da 'Baby Yesmin'..... Kuma duk a Zaria academy suke karatu wacce anan nima nayi SS classes d'ina alokacin da muka dawo garin sabo sabo.
*FADIMA SA'AD* (my precious self)
Ba yabon kai ba amma agaskia babu wanda zai kalleni yaso dauke kansa daga gareni musamman ma opposite sex d'in, ina nufin maza sabida irin zub'in halittar da Allah ya k'era mun, Kuna ganina kunga fulanin usuli, though wasu mutanen ma sukan yi tunanin ko ni d'in na had'a iri ne da larabawa, sabida yadda nake da k'yau da kuma hasken fata irin tasu mai daukar ido, gashin kaina baki siddik gashi da tsawo da sulbi,idan muka gangaro kan fuska kuma, zan iya cewa subhanallah sabida k'yan k'yau.. Eyebrow dina acike yake, bak'i dashi wanda yake dauke da shape mai k'yau, idanuwana dara-dara da eyelashes zara-zara wanda ya baiwa idanuwan wani irin sirri na k'yawu, hancina gashi zirr dashi kamar pencir, sai kuma pinkish lips d'ina wanda yafi daukar hankalin mutane, Ina da matsakaicin tsawo da 'yar kiba, ma'ana ni d'in 'yar duma-duma ce (chuppy in body frame.)
