BABI NA DAYA

77 8 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
 
      

         

         *BABI NA DAYA...!*

Kwance nake saman katafaren gadona,hirar soyayya nake tare da mutumin da ban tab'a gani ba haka zalika shima din bai tab'a ganina ba, Allah ne kawai ya had'a abinsa ta dalilin wayar sadarwa, ya sanar dani cewa lambar wani abokin aikinsa ya karba gun wani, toh ayayin kwafe lambar acikin wayarsa ne yayi kuskuren rubuta wani lamba gud'a aciki, wato amaimakon takwas da zai saka ak'arshe, shine aka sami kuskure yasaka sifili ,wanda adalilin hakan ne K'iran ta fad'o layina.

Tun daga lokacin muka kulla alak'ar soyayya wanda dak'yar ya samu har ya iya shawo kaina kafin na yadda na karbi tayin soyayyar tasa, tun bana wani sakewa har nazo na ware na soma d'an sabawa dashi wanda har takai ta kawo idan har banji muryarsa arana daya ba to kuwa kafin wayewar gobe zazzab'i na iya rufeni kasancewar soyayyarsa ta riga ta gama yi mun mugun kamu, ta gama gaurayewa da jinin jikina, lokaci kalilan ya mallaki zuciyata, jin Mubarak nake tamk'ar wani b'angare na jikina d'an sai da ya tabbatar babu wani gurbi da yayi saura wanda bai cike da soyayyarsa ba, sai da ya cusa mani k'aunar ra'ayoyinsa, ya kuma d'orani akan yadda yake son soyayyar tamu ta cigaba da gudana.

wayyo Allah jama'a ya zanyi da rayuwata idan har na rasa shi? Abun takaicin ma ni Fadima bani da tabbacin mutum nema ko kuwa aljan? Sabida har kawo wannan Lokacin bamu tab'a had'uwa ba, har yanzu dai muna kan gudanar da abun namu ta waya ne ...DR MUBARAK MUHAMMAD MUSTAPHA kenan.

Tsawon watanni biyar kenan muna fama da abu gud'a ta waya wato soyayya da Kuma chatting akan WhatsApp amma koda wasa kamar yadda na fad'a bamu tab'a haduwa azahiri ba, duk kuwa da kasancewar garuruwar da muke basu da nesa da juna,hasalima ina iya cewa tamk'ar baka da hanci muke...Ni mazauniyar garin Zaria ce ayayin da shi kuma d'in mutumin Kano ne.

Bazan iya kirga adadin magiyarsa kan mu hadu ba, amma ni d'in ce kawai na hana hakan faruwa, dalilina kuwa shine, ina fargabar kar yazo ya ganni yaga ban masa ba duk da cewar nasan  ni d'in irin matan nan ne da akewa lak'abi da son kowa k'in mai hassada.

Ni dai na riga na daukarwa kaina alk'awarin koyaya kammani da suffar
Mubarak yake muddin dai shi d'in ya kasance mutum ne kamar kowa, to bazan damu da kammaninsa ba, ina son abuna ahakan, ban san wani hukunci shi zai yanke ba idan yayi tozali dani tunda ance 'abincin wani gubar wani' dalilin dayasa nake amatuk'ar tsorace dashi kenan da har yasa na kasa bari mu ga juna azahiri.

Ahalin yanzu d'in ma, sana'ar tasa daya saba yake yi wato ina nufin magiya,"Haba my Zahra ki tausaya ki ceci rai, ki bani damar nazo naga sarauniyar data dad'e tana mulki acikin babban birnin zuciyar bawan Allah Mubarak, wallahi zuciyata, gangar jikina dani karan kaina muna muradin muyi tozali da kyakkyawar fuskarki yake ma'abociyar hankali da nutsuwa wacce ita kadai ta iya sarrafa daddad'ar soyayyarta acikin zuciyar
Mubarak d'inta, Please babyna ina fatar wannan karon my request will be granted? " ya karashe maganarsa cikin wani irin salo na soyayya wacce sai da naji duk wani kuzari na jikina ya kau sakamakon yadda zumar soyayyarsa ta narkar da duk wani d'an gudan jini dake gudana acikin jikina.

Da k'yar na iya tattaro nutsuwata, na d'an saki kasaitacciyar dariyata mai birge mutane tare da rage muryata, Nace"Wow haka nake da babban matsayi acikin rayuwarka ? Mubarak haka kake jina aranka ? ai azatona ni kadai ke haukata, ada kokonto nake akan watakila son da kakemun ta k'arya ce, amma acikin kalamanka na yau kadai na tabbatarwa kaina da lallai sakonninmu na isa ga juna dak'yau yadda ya kamata, babu zancen yaudara, Mubarak na aminta dakai amma zancen haduwar tamu kuwa, Zan sake fad'a, kadan k'ara hakuri har sai zuwa lokacin da nayi ra'ayi please. "

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now