*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA SHA BIYU...!*
*BARI MU WAIWAYI MUBEEN*
Tunda motarsu Fadima ta tashi, ya bi motar da idanuwa,bai daina kallonsa bah har sai daya ga motar ta bar layin.Tambayar kansa yake, "anya na kyautawa Zahrata kuwa? "Meyasa zan boye mata cewar ina da mata har da 'ya? Meyasa zan b'oyewa dangina zancen soyayyata da ita akan dalili mara tushe Wanda na lura abinda ma yafi bak'anta ranta kenan?"
Tambayoyin daya shiga jerowa kansa kenan wanda bashi da amsar ko daya. Gunjin kukar Hanan ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula.
Sannu ahankali ya juya ya soma takawa har yakai inda take tsaye take kukarta mai tab'a zuciya.
Ganin ya iso dab da ita ne ya sanyata saurin d'aga masa hannu,tace"Meh kuma zaka ce min? Koh ba'a fad'a ba kowa ya shaida ka fi sonta akaina.... Na maka abinda kakeso don farin cikinka mijina ya fiye min komai... Zan iya jure ko wani irin kuncin rayuwar da zan shiga in har akanka ne, Inaso ka bani izini ni da kaina zanje na nuna wa Mummy cewar nice na baka goyon bayan ka k'aro wani auran..... Abu Jasmine bana k'aunar wani abin ya sameka sabida ba karamin so kake yiwa wannan baiwar Allahn ba, ka bari kawai inje in fahimtar da Mummy "
"And do u think diz is a minor problem da har kike tunanin tunkarar mum da wannan maganar? "
Murmushin takaici yayi, sannan yace"Hanan ke kanki kin kwana da sanin cewar yadda mummy ke masifar kaunarki ba zata taba yadda na karo wani auren bah.... Ke dai kawai ki bari zanyi handling wannan issue din da kaina, zanyi k'ok'ari in sameta da batun zuwa gobe "
Kokarin magana take ya katseta ta hanyar rungumota"Shhhhh! Its okay Hanan dita karki sake cewa komai.... Kuma bana son kina fadin cewar nafi sonta akanki... No, kowacce da matsayinta azuciyata, zan mah iya cewar matsayinki yafi nata aguna because ke din 'MATATACE' kuma 'UWAR YA'YANA'........ Don gashi muna expecting wani babyn very soon.... " Ya fadi hakan tare da shafo 3months old pregnancy dinta wanda babu wanda zaiyi tunanin tana da ciki sai su d'in da suka san da abinsu.
Yace"Hanan d'ita I love you so much.. Hakika ke macece ta gari... Allah ya miki albarka matata"
Maganganunsa ba k'aramin dad'i sukai mata bah, don haka tace"Ameen mijina.....Mubarak d'ina nima ina mutuwar sonka... Pls kada ka juya min baya idan har Allah ya kaddara aurenku da sister Zahra..... "
Da sauri yace"Haba Hanan stop saying dat.... Taya za'ai na soma tunanin rabuwa dake? Idan har mah nayi hakan toh wallahi na cika babban butulu kuma na rasa mace ta gari wacce kowa zai so ace matarsa ce ke....Don Allah kisa aranki cewar ni dake mutu ka raba ne takalmin kaza insha Allah..... "
Murmushi tayi tare da furta"Thank you hubbyna💗..... "
Yace"U most welcome wifey.... Gaskiya ni dai bazan iya shiga cikin gidan nan yanzu ba don ban shirya fuskantar rikicin Mummy ba .... Nasan tana cikin b'acin rai ahalin yanzu, dan haka zan bari ta huce idan yaso gobe zanzo na sameta sai muyi wacce zamuyi.......yanzu akwai abinda zaki dauka ne acikin gidan?"
Tace"Kayan sawanmu nida Jasmine kala bibbiyu ke ciki amma ga wayata nan ahannuna.... Sai kuma ita Jasmine d'in "Yace"Rabu da Jasmine ta kwana anan tunda dama gobe zamu zo..... Kinga taho mu hanzarta mu tafi gida kada hajiyar ta lek'o waje ta ganni.... "