*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA TAKWAS...!*
Ido cikin ido muke kallon juna ayayin da kowannenmu ke raya wasu al'amura acikin aransa agame da juna.Kyawun Dr. Mubarak ya wuce yadda nake ta tsammanin gani. Namiji ne tsayayye mai cikar zati da kamala, k'warjininsa ma har wani kashe mun idanuwa yake wanda hakan ya sanya nayi saurin kau da idanuwana daga kallonsa. koma kallon Jasmine nayi wacce tana jin muryarsa ta ruga da gudunta wurinsa tana fad'in"Daddy oyoyo wato dazu shine ka tafi ka banni ina ta nemanka ko? "
Lakatar karamin hancinta naga yayi yace"Am sorry babyna nayi laifi ayafewa Daddy... "Tace"To Daddy na yafe maka amma wacece waccan antin mai kyau sosai...? "
Tayi masa wanna tambayar tana nuno ni da 'yar yatsarta ayayin da ni kuma na kasa kunnuwa inji ko mai zai fad'a mata.
"Kawar mominki ce... " hakan naji ya furta tare da nuna Hanan wacce naga yana gama fad'in hakan ta juya tabar dakin da sassarfa.
Gabana ne ya shiga bugawa da sauri da sauri.... Daddy ? Mommy ? Kawar mominki?.... mai hakan ke nufi ne wai ?
Kaina akasa ina tunanin abinda Mubeen ya fad'a, "Kawar mominki ce.... " wannan maganar shi yafi tsaya mun arai.
"Bugun zuciyata sannu da zuwa..... Please Zahra ki gayamun cewa ganinki da nakeyi agabana yanzu its reality ba mafarki nake ba..." Maganarsa ce ta katse mun gajeriyar tunanin da nake. Had'iye wani katon abu kamar dutse nayi wanda naji ya tok'are min mak'ogoro kan nace"Mubeen ba mafarki kake ba, Fadimarkace dai zaune agabanka " ahankali ya furta yana sakin tsadadd'en murmushi"Zahra wallahi you are very beautiful " kunyace ta kamani sosai, kwata kwata na kasa bari mu sake had'a k'wayar idanu. Hakan ne yasa ya juya yana kallon Suhaima wacce sai k'ok'arin son b'oye fuskarta take atsakanin cinyoyinta amma kash! ta makaro don ya riga ya kamata.
Nunata yayi da 'yar yatsa yana fadin"Hey! Lil sis na kamaki..wato ke mai wayau wai zaki b'oyemin kada na ganki ko ? ... Haha ai tun awaje na gama capturing faces d'inku... serious da gasken kina matuk'ar kama da My Zahra.. "
Dago kanta tayi tana dariya, tace"Kai yaya Mubeen wallahi kayi mana wayau sosai... Wato Kai kana ta kallonmu mu bamu sani ba, karka damu muma zamu rama ai"
Yace"hahah babu wani nan, mun daiyi 1-1 Ko kuwa ba kallona dukanku kuke ba yanzu ?"
"Hey! Na sake kama wata tana satar kallona.. " Ya nuna Ash queen da yatsa wacce kallonsa take amma fuskar nan tata cike yake da alamun tambaya.
Dariya muka sanya duka sai kace wurin shakatawa muke ba gidan rasuwa ba, Anan muka kawo k'arshen barkwancin da wasannin, muka shiga gaggaisawa tare da masa gaisuwar rashin da yayi.
Yace"Oya baby Zahra sauko kuci abinci.... Lil sis, mal. Aysha asauko pls kada abincin yayi Sanyi.. " (Dama yasan Ash queen don ina yawan bashi labarinta)
"Ni akoshe nake.... " hakan na fadi cikin wani irin cool voice wanda ni kaina ban san cewar inada ita ba sai ayau agaban masoyi.
Hararar wasa naga ya jefeni dashi, yace"Ai wallahi baki isa ba.... Baby Jasmine samo mun bulala na Zane beautiful antin nan naki don naga bata son taci abincin.. "
Jasmine ce naga tana kokarin fita samo bulalar, ban san sanda nace"Jasmine dawo zanci.... " bah
Dariya akayi duka, yace"Better... "