*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA SHIDDA...!*
Zazzaune muke saman gadon Umma mun sanyata atsakiya, kowa sai murnar dawowarta ake musammam Yesmin wacce ta hanata sukuni.Akalla an sami kusan awa biyu kenan dasaukan nata.Fira muke sosai irin ta d'a da mahaifi.can Umma ta rarrabawa kowa tsarabarsa anata ihu da tsalle tsallen murna.Umma tace"Oya auta, soja aje ayi wasa abarni na huta kadan.. Ko dayake nasan daga nan Sojana dakin karatu yayi babu ruwansa da wasa koh? " Ina ruwansu Faruk cikin fahari da kai yace"Umma aini kullum bana wasa karatu nake, ko a makaranta malamin mu na cewa nafi kowa k'ok'ari a aji. "Dukkanmu muka fashe da dariya, nace"Dalla wuce ka bamu wuri sai shegen fahari da kai. "Umma tace"ku k'yale min shi yayi sabida yasan mai yake yi kuma ina alfahari dashi.. "
Daga hakan shida Yesmin suka fice, umma tace"Oya Lubna kema bisu..."Ahankali ta mik'e tabi bayansu, Sai ayanzu na fahimci cewar Umma so take dakin ya rage daga ni sai ita da kuma Suhaima, juyowa tayi ta kalle mu, tace"Fadima... Suhaima.."Da sauri muka d'ago kai muka zuba mata idanu har muna rige rigen fad'in "Na'am Umma ?"Dad'a gyara zamanta tayi saman gadon ayayin da ni nake gefen damanta, Suhaima kuma tana gefen hagunta. Tace"Abunda yasa zaku ga ku na tsai daku, sabida ku d'inne manyan kuma abunda nake shirin fad'a nasan zaku bashi k'yakk'yawar fahimta musamman ke Fadima dake babba " Numfasawa tayi kan ta cigaba"Fadima inason ne na dakko maganar da muka soma yinta tun awaya, kuma albishirinku?" Da sauri mukace cike da farin ciki"Goro fari kal Umma "
"Fadima kamar yadda kika fad'i cewar lallai kuna bukatar lokacina, kulawata da kuma soyayyata, atakaice dai kuna tsananin bukatata akusa daku, to wallahi na zauna nayi tunanin lallai ban tab'a k'yauta maku ba, kuma nayi tunanin yau idan har na koma ga Allah mai zan fad'a masa kan amanarku daya bani ? Dalilin dayasa ayau d'in nan nake farin cikin shaida muku cewa na daina kasuwancin abroad... Zan dinga yinsa acikin gida nan Nigeria, sabida haka daga yanzu zakui ta samun time na Umman kunji ko ?"
Suhaima ce ta saki ihun murna ta rungumeta tana fadin"Woww Umma can't juz believe this, wai dagaske kike ko wasa ?"Murmushi Umma tayi sannan tace"Yeah ni na fadi hakan so ki rubuta ki Ajje my pretty angel. "
Umma ce ta juyo gareni ganin ni bance uffan ba,ta kamani ina goge d'an gutun hawayen daya digo saman kumatuna kuma alokaci daya ina murmushi,janyo ni tayi kusa da ita tana fad'in"Haba 'yar Kareematu ya naga kina murna alokaci gud'a kuma kina hawaye ? tell me Wats wrong? Kodai baki ji dadin hukuncin dana yanke bane ?"
Murmushina na cigaba dayi ayayin da hawaye sai dad'a kwaranyowa yake saman kumatuna, nace"Ummu Fadima the best moment in life is 'Smile' and 'cry', they won't meet each other at a time.. if they do, then believe me its the best moment in ur life...Nayi farin ciki sosai Umma da irin hukuncin da kika yanke , muna sonki matuk'a Ummu Fadima "
Na rungumeta, wannan karon kuka nake sosai, umma Duk tabi ta rude tace"Haba my baby kiyi shiru ko so kike nima nayi kukan? "Da sauri na tsaida kukan, na shiga share hawayena ina fadin"Ummu Fadima ki banni nayi kukan hakan na nufi da irin tsantsar farin cikin dana tsinci kaina aciki ne" gyad'a kai tayi cike da gamsuwa, ta mik'e ta shige bandak'i don watsa ruwa. Dad'i ne ya lullubeni ganin yanzu Mahaifiyarmu zata dunga bamu time d'inta kamar yadda ta jaddada mana dai yanzu... Don bani mantawa tun Suhaima nada shekaru uku kacal aduniya Umma ta soma harkan kasuwancinta, Wanda tun alokacin muka daina samun cikakkiyar kulawa da lokacinta dan kosu Lubna ma basu wani ji dadinta ba, sannan kuma nayi matuk'ar murna da Umma ta yankewa kanta hukunci kafin Abba yama kai ga yi mata magana akansa dan ni na tsani ganin see parents fighting or arguing,zan iya cewa tunda na mallaki hankalin kaina ban taba ganin iyayena na fada atsakaninsu bah, shiyasa nayi matukar murna da ita tayi saurin ganewa harta sauko kafin shi ya hau Wanda nasan sam abin da bazai yi dadi ba idan har aka sami banbancin ra'ayi.