BABI NA TARA

9 1 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA TARA...!*

Zai soma magana kenan mukaji k'arar tsawa wanda k'arar ba k'aramin tsoratani yayi ba, kuma adaidai lokacin text message ya shigo wayata daga Ash queen,kamar haka,

_"Malama hope kina dai ganin had'ari koh?  and dix is 15mins to 1pm... Don Allah duk inda kike ki taso mu kama hanya kada ruwan nan ya sauko bamu bar garin nan ba... "_

Ina gama karantawa na d'ago kai ak'idime ina kallon Mubeen nace"Mubeen don Allah mu tafi kawai kada ruwan nan ya sauko ya tsayar damu anan, Gashi Ash ta min text wai inma taso mu kama hanya kawai, dan haka duk wani tattaunawa mu barshi  zuwa lokacin da kai zaka kawo mun taka ziyarar.... " Na mik'e da niyyar fita a 'joint' din.

Da sauri naji yace"Don Allah Zahra ki tsaya ki saurareni don yau nake son muyi ta ta k'are... "

"No Mubeen bazan iya saurarenka yanzu ba don gaba d'aya hankalina ya k'arkata zuwa ga 'yan'uwana da kuma can gida Zaria..... " Na fadi hakan cikin k'osawar son mu bar wajen.

"Koda kuwa zan fadi miki cewar akwai dangantaka mai k'arfi tsakanina da HANAN... Shi d'in ma ba zaki tsaya ki saurareni ba...? "

Da sauri na kalleshi, na koma na zauna da mataccen jiki. Cikin rashin kuzari nace"Ban fahimta ba... Pls ka fitar dani acikin duhu.... "

Ahankali ya cigaba da magana kamar bai son yayi, yace"HANAN is my wife not a blood sis...sannan Jasmine 4years old daughter d'inmu ce........... "

Ak'idime na mike ina fadin"What????? Mubeen mai kunnuwa suke jiye mun?? Mubeen dama ashe kana da aure yaudarata kawai kake son kayi.... ? Dan Allah ka amsani.... " Na furta hakan already in tears Allah ma yasa inda muka zauna babu mai jin abinda muke fada sai dai yaga actions namu.

"Don Allah Zahra take it easy I can  explain...."

Cike da tsiwa nace"Bayanin meh kuma zakayi??? Komai anan is clear and straight forward..... Hanan matarkace and Jasmine d'iyarka...Mubarak nidai kawai kawai ka yadda ka riga ka gama da rayuwata totally... " Na k'arashe maganata cikin tausayawa kaina, sannu ahankali na soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Sai daya kyaleni nadan tab'a kukan maybe don na dan sami rest of mind ne don kun san ance wani kukan yakan yi reducing pains, zuciya takan sami dan sassauci.

Don kaina nayi shiru, na koma yin kukan zuci. Ganin nayi shiru ne ya bashi damar cigabawa"Hanan 'ya ce ga wata k'anwar Mummy. Mummy itace tayi rik'onta tun tana yarinya har zuwa sanda ta mallaki hankalin kanta.Tun tana k'aramarta yarinyar ta shaku dani, nima hakan na shaku da ita.

As time goes on, shakuwarmu ta wuce over wanda na lura ita yarinyar mah harta kamu da matsanancin sona, ni kuma har ga Allah Soyayyar wa da k'anwa kawai nake mata.

Ganin ta kamu da matsananciyar soyayyata ne ya sanya na soma k'aurace mata don bana son soyayyar ta mata yawa acikin zuciya har tazo mata illah.Ashe abinda ban sani bah kuwa shine, ashe dama can Mummy ta kudira aranta son ta had'amu aure ni da Hanan d'in.

Sanda tajewa Mahaifinmu da kudirin nan,  nata atake yayi na'am da zancen tare da nuna mata lallai yama fita son wannan had'i.Mahaifiyata kuwa tama riga ta rasu kafin wannan zancen ya taso, koda yake even if she was alive,nasan bah zata hana hakan faruwa bah don yadda suke zaman lafiya da Mummy da kuma yadda taga Mommin ke masifar kaunata dole ta mata k'ara ta hanyar yin na'am da batun.

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now