*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_
*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
*BABI NA SHA UKU...!*
"Haba Yaya Fadima its too early ki soma tunanin rabuwa da Mubarak dan kawai yana da mata hadda 'ya, dan girman Allah ina son please kiyi masa Uzuri tare da bashi k'yakk'yawar fahimta, karki ga laifinsa, Ki sani Sonki ne ya saka ya b'oye miki komai dan atunaninsa idan har ya kuskura ya bayyana miki gaskiya da wuri to zaki rabu dashi, Yanzun kuma daya fito fili ya fad'a miki gaskiya, kina k'ok'arin break up dashi.... Wallahi sis karki kuskura! I repeat, karki sake kiyi gangancin barin Mubeen akan wannan Leedar d'in, ki sake zama kiyi tunani "
Yadda take zuba maganganun nan zaka san cewar ba'a cikin hayyacinta take yinsa bah. Kokarin katseta nake sai ji nayi an riga ni.
"Hey! guys wai meyake faruwa ne da har kuka tadani bacci da hayaniyarku?.... Huh? " Ash queen ce ta tunkaro inda muke tana fad'in hakan.
Da sauri na amsa ta don bana son ta san abinda yake faruwa, nace"Ash kin mayi sallah kuwa? Don ni dai ko motsinki banji bah tunda kika kwanta jiya kamar wata sabuwar gawa.... "
Harara ta jefo min tare da fad'in"Eh fah alarammiya ina fah za kiji motsawar tawa?... Toh bari kiji yarinya komai da kika yi adaren jiya akan idanuwana ne, ke da kika kwana kina ibada kamar wacce taji an bata k'yautar Ajannah free shine take nuna godiyarta ga Allah?..... Kina kwantawa shidda ni kuma na mike na gabatar da tawa sallar kafin na koma second round na baccin......... "
Dariya muka sanya nida Leedar don maganarta, sab'anin Suhaima wacce sa kai tayi tabar wajen fuskar nan ah murtuke babu koh d'igon annuri akansa,Ash dai binta tayi da idanuwa amma bata ce komai bah, kuma nasan ta d'ago wani abin wanda sam bah hakan naso bah.wallahi Suhaima is very annoying at times.
"Ash na Bash.... " hakan Leedar ya fad'a don ya dawo da hankalin Ash zuwa garemu.
Murmushi tayi masa tare da fad'in"Hey! Lee na Teema watsup!.... Sai yanzu na lura dakai.... Meya kawoka gidan surukai da sassafe haka bayan koh 'yan gidan mah basu gama tashiwa bah? " Ta fad'i hakan in a teasing way.
"Ash ai ni na riga da na zama d'an gida... Don haka ke zan mah yiwa tambayar koh meya kawoki gidanmu da safiyar Allahn nan? "
"Hmmm ina ruwan masu gida.... Toh don kaji, ni anan mah na kwana.... "Ta bashi amsa atakaice.
Murmushi yayi tare da fad'in"Ash kenan! Wato ke dai ba zaki taba canza halinki bah..... Hope dai kina kular min da aminina.....? "
Harara ta wurga masa tace"Kai Kanka kasan dai Ash bata d'aukar last..... Shi ne ma zance idan har beyi serious ba toh tabbas na kusa bashi red card..... "
Dariya muka sanya duka, nace"Ash ke dai wallahi akwai shirme....... "
Ignoring d'in maganata tayi ta hanyar fad'in"Alamu dai ya nuna ba'a son naji abinda ke faruwa don naga Suhaima ma barin falon tayi, yanzu na gane cewa family issue ne wanda bai kamata ace na tsoma dogon bakina aciki ba...... "
Da sauri nace"No Aysha wallahi ba abunda kike tunani akai bane, Bawai ina boye miki wani abun bane.... Alright naji zanyi bayani...... "
Taran numfashina tayi ta hanyar sanya 'yar yatsarta saman lips d'inta, tace"Shhhhh! Karki damu I understand.... Kuma ba wai fushi nayi bah... No, kawai gani nayi ke baki daukeni kamar yadda ni na daukeki amatsayin yar'uwa ba, kwata kwata ke d'in ba kiyi trusting d'ina ba...amma watakila kina tsoron karki gayamun sirrinki sannan inje in bazar dake awaje ne "
