BABI NA BIYAR

12 1 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
 
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
      

         

         *BABI NA BIYAR...!*

Tun sanda Suhaima ta furta mun cewar wai Mubeen d'ina zai k'ira yau, na kasa Samun sukuni, bini bini nake duba wayata ko zanga missed calls d'insa, text message ko kuma message ah watsap, amma ko daya ban gani ba har zuwa yanzu da muke k'arfe goma sha daya na dare shiru kake ji, cire rai nayi kawai dashi.kwance nake saman gado amma na kasa bacci sai tunaninsa nake gashi naki sauke girman kai na k'ira kamar yadda 'yar'uwata ta shawarceni.duba nakai gefena jin motsin gyara kwanciya, Yesmin ce kwance take bacci cikin kwanciyar hankali amma da k'yar na sami tayi baccin sabida ta dameni da rigimar son ganin Umma, da lallashi da kuma 'yan dabaru na sami tayi baccin.Na gyara mata lullub'i da bargo kasancewar babu laifi ana d'an tab'a sanyi dayake muna cikin lokaci na hunturu ne.
   Ahankali na sauka kan gadon gudun kada na tasheta, nayi dakin su Suhaima wanda yake akusa da Nawa... Ita da Lubna ke Kwana daki daya ayayin da Faruk ke Kwana tare da Abba, idan kuma Umma nanan to anashi dakin yake kwana.

Tura k'ofar dakin nayi ahankali dan duka gidan bama rufe kofofin dakunanmu, abin mamaki Suhaima ce na gani zaune saman gadonta ta zuba wani uban tagumi alamun tayi nisa cikin tunani, Cike da sanyi na furta"Ashe itama batayi baccin ba.." k'arisawa har inda take nayi na zauna a gefenta amma still bata sani ba. Dafa kafadanta nayi tare da k'iran sunanta ahankali"Suhaima.. wai ni tunanin mai kike ne haka wanda har yasa kika kasa bacci ak'ank'antar shekarun nan naki ? "..Firgigit! Ta dawo daga duniyar tunanin data lula tace"Sis yaushe kika shigo ban sani ba ?" Nace"Taya za'a ki sani kuwa bayan kin lula duniyar tunani... Tell me meke damunki? Idan kuma akan accusing naki dana yi dazun ne to dalilin dayasa nashigo kenan dan na baki hakuri, Nasan nayi kuskure babba hadda marinki... Wallahi ki yarda nayi ban san menene ya shiga k'wak'walwata ba da har yasa nayi tunanin hakan, Sis pls ki yafewa Yaya Fadimarki wacce baki da kamarta arayuwarki...dan Allah ki gafartamun hadda marin dana miki dazu"

Hararar wasa naga ta jefeni dashi, na gane hakan ne sabida Dim light daya haska dakin, tace"Ai ni am not like you.. Babu wanda ya isa ya shiga tsakanina dake musamman ma d'a  namiji, amma meyasa kikayi tunanin na fad'a tarkon soyayyar Saurayinki ?"

Ni kaina sai dana ji kunyar tambayar data min, ahankali nace"Banyi hakan da wata manufa ba.. kawai subutar baki ne amma bari in gaya miki gaskiya, hak'ik'a ina jin haushi sosai idan kina fad'in cewa kin tsani Aliyu alhalin bai tab'a miki laifin komai ba, yanzu dai kiyi hak'uri mu manta da komai kinji ?" Murmushin takaici naga tayi tace"Hmm Subutar baki ? To shikenan naji komai ya wuce amma next time kiyi k'ok'arin tauna magana kafin ki amayar " Azuciyata nace" Suhaima kenan, bazan tab'a daina fad'a miki cewar alallai kin kamu da soyayyar Leedar bane, sai dai zanyi shiru inga iya gudun ruwanki " tace"Uncle Mubeen ya kiraki din kuwa? "

Girgiza mata kai nayi alamar ah'ah,Cike da tashin hankali tace"Sis gaskiya yakamata ki k'irashi yanzun nan dan wallahi dad nashi aka fitar zuwa k'asar waje (India) aka masa dashen kod'a, jiyan jiyan nan dana k'irasa ne suka dawo, dalilin dayasa kika ga bai k'iraki ba kenan harna tsawon kwanak'in nan, ba wai akan maganar Leedar ne kadai ba "Mik'ewa nayi jiki na rawa nace"what?? Dan girman Allah da gaske kike ?" Tace" Sis mezai sa in miki irin wannan wasa ?"

Da dan gudu guduna na fita adakin na koma nawa don dauko wayata inbi shawarar da Suhaima taban, Cin karo nayi da Yesmin da wayar ahannu alamar zata kawo min, tace"Anty tun dazu nake ta nemanki na baki waya anata k'iranki kuma na duba bathroom bakya ciki shine ada zanje nemanki afalo ko dakin su Yaya Suhaima " Shafa kanta nayi nace "Nagode baby sis, oya koma ki kwanta abunki" Na karbi wayar daga hannunta ayayin da ita kuma ta koma baccinta. Na duba naga 5missed calls din my Mubeen, atake anan wani murmushi ya lullub'e min fuska, Ji nayi ance"Shi ya k'ira ko ?" Waigawa nayi naga Suhaima tsaye abakin kofa ashe ta biyoni ban sani ba, kai kawai na daga mata kana na latso lambar tasa.

Bugun farko naji wayar switched off.. Nayi ta gwadawa har kusan sau goma amma still switched off shegiyar baturiyar nan keta cewa. Ji nayi kamar zanyi hauka don bak'in ciki, Suhaima ce tace min"Lovly sis please ki kwantar da hankalinki watakila wayar ta mutu babu chargy ne, amma muna fatar Allah dai yasa lafiya, Kiyi hakuri zuwa gobe sai mu sake gwadawa kinji ?"..Ahankali nace"Ba damuwa Allah ya kaimun"Daga hakan mukayi sallama kowa ya koma baccinsa amma zan iya cewa yadda naga rana haka naga dare, kuma bayan minti biyar biyar nake k'ara gwadawa inga ko za'a dace ya shiga amma shiru kake ji.

  ****

Misalin shidda da mintina hamsin ta safiyar laraba 'yan makaranta suka kammala shirinsu cikin shiga ta uniform d'insu. Muna zaune kan dinning ana breakfast hadda Abbanmu Wanda shima sauri yake ya tafi gun aikinsa. Abba ne ya kada baki yace"Antynsu wai yaushe umman taku zata dawo ne ? naga kamar ke kin fimu samun information daga gareta" Murmushi Kawai nayi nace"Tace mun ata idanu kan hanya cikin kwanak'in nan tana tafe insha Allah " Su Yesmin kowa ya hau ihu ana murna. Abba kuma Gyad'a kai Kawai yayi sannan yadan yanki tissue ya goge bakinsa, ya mik'e hadi da daukar briefcase nashi yana fad'in"Antyn yara nadan ganki mana" Yayi hanyar fita falon kannena na"Abba adawo lfy"

Daidai barandar sashinmu muka tsaya, nace"Abba gani " Shiru ya danyi harna tsawon dak'ik'u goma, kana ya soma magana"Fadima don Allah ku cigaba da hak'uri da rashin zaman mahaifiyarku akusa daku, Nasan abin na damunku amma ayau na daukar muku alk'awari Wannan itace karon k'arshe da Kareema zata sa kafa tabar k'asar nan da nufin kasuwanci... Lokaci, kulawa da kuma soyayyar nan dole ne ta baku, ni ina Uba kenan Wanda aka sanmu da cewar bama cika zama sabida yanayin aiki amma duk da hakan ina iyakacin bakin k'ok'arina fiye da ita da take mace ? Ai ni bance mata na gaza ba da har zata dage da kasuwancin nan, Ki duba fa kusan wata daya take nema ak'asar mutane, abunda bata tab'a yi ba, tana can tana cudanya da iri irin kazaman Mutane... No I can't take that any longer ya zama dole na dau mataki.... "
Da sauri na tsugunna ina kuka nace"Abba please don Allah kada ka kawo k'arshen dogon burinta akanmu, Abba in tamu ne wallahi mun Riga mun saba da irin wannan rayuwar don haka kada ka damu da batunmu ka batta ta cigaba da kasuwancin nata " Yace"Look Fadima karki hanani daukar mataki akanta wannan karon, nayi hak'uri kuma kanku kunyi, dan haka ya isa hakanan, i will take action, idan ta dawo kema akwai maganar da zamu tattauna akanki "Damn! Naji k'irjina ya buga, atake anan naji hankalina kuma ya tashi. Murmushi naga Abba yayi yace"karki tada hankalinki ba wani k'wakk'waran abu bane amma trust me tattaunawace mai matuk'ar muhimmanci wanda ya shafi rayuwarki ta nan gaba, Nina tafi saina dawo"

Mukayi sallama ya tafi, driver mah ya kai yan makaranta ayayin da ni kuma aka Banni ni kadai agida sai kuma house girl Indo. Allah Allah nake monday yayi na koma school because I rilly missed many tinx especially my Leedar.

Now left alone with My Mubeen's thought Wanda har zuwa wannan lokacin wayarsa taki shiga.

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now