Page eleven

167 11 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

Follow and vote on

WATTPAD
@YoungNovelist4

Blog:
https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

INSTAGRAM
Khadeejaht-hydar -youngnovelist

TWEETER
@Young Novelist II

FACEBOOK
Khadeejaht Hydar YoungNovelist

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ban yarda wani ko wata ba ya juya min littafi ba.

Novel is free just need ur support dearies,visit me on wattpad,,@YoungNovelist4 to read more of my stories.ga link ga masu buƙata ku shige kai tsaye.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Wannan page din nakine Mummyn Afnan kyauta daya tak gareki.
Inamiki jinjina da yabo mai girma,inayinki over sosai.

~Page Eleven~🖊️

Sumewarta yayi dai-dai da faɗuwan gaban Sabeer alokacin yana Office,cikin dafe ƙirjinsa ya tashi tsaye yana ambaton Allah zufa na keto masa,yana iya juyo yadda ƙirjinsa ke bugawa kamar zai fito,idanuwansa ya lumshe yana maida ajiyar zuciya,cikin tsoro Fawaz yace"Sabeer lafiyarka miyene yasameka katashi a zabure haka?,komawa yayi ya zauna ya ɗau remote yana ƙara gudun AC yace"Fawaz wata mummunar faɗuwar gaba ce tasameni naji kamar wani abun mara kyau yafaru dawani na kusa da zuciyata,tun shekaranjiya gabana yake faɗuwa amma nayau yafi nauyi da ƙarfi,naji tsoro ya ɗarsu a raina,Fawaz kunamin addu'a ina cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa wanda nikaina bansan meke guduna acikin zuciya taba,Lukman dayayi shiru wanda shi dama ya kula da yanayin abokinnasa yace"Sabeer kodai akwai abinda ke damunka amma kakasa faɗa?,yace"haba Lukman kunsan babu abinda zan ɓoye maku ni wlh bansan meke damunaba,Hafeez yace"kacire damuwa a ranka sannan kana yawaita addu'a dukda nasan kai mai addini ne,yanzu dai ku tashi muje gida ya huta daganan mu gaida Ammee.

Gidansu Sabeer suka nufa motarsu n parking tasu Hanan na shigowa,fitowa su Sabeer sukayi suna zancensu suna dariya,su Ayshama fitowa sukayi daga motar amm babu wacce ta ƙarasa gun su,Hanan najin kunyar Lukman itakuma Aysha yadda Sabeer ta zuba mata idanune yasa takasa motsawa,dariya suka bama su Fawaz don haka cikin tsokana Fawaz,Shareef da Hafeez suka nufosu,Fawaz wanda yafi kowa barkwanci yace"tunda anƙi zuwa a gaishemu bari mu muzo mu kwashi gaisuwa,Hanan   ce tace"ina wuninku sannan Aysha ma ta gaidasu,Lukman kam  ƙarasowa yayi yana murmushi yace" Afternoon Wifey,kunyane ya lulluɓe Hanan don haka saita juya ta nufi cikin gida batare data ɗauki school bag ɗin nataba,dariya sukasa Shareef yace"saura sarauniyar kunya tunda gimbiyar kunya ta tafi,itama Aysha cikin murmushi tafara tafiya batako kalli inda Sabeer yakeba,shima bai tsayar da'itaba illa murmushin dayayi don yasan inhar su Fawaz nagun to bazata tsayaba,saida takai inda zai sadata da ɓangarensu ta juyo tana murmushi,shima murmushin yamata tare da ɗaga mata hannu tukun ta shige.

A parlour suka tadda Ammee zaune da Hanan tana mata shagwaɓa tana ganinsu tasake narkema Ammee ita ala dole Auta,zama sukayi suka gaidata ta amsa cikin fara'a tare da tambayar su ya aiki,kallon Hanan tayi tace"Auta ki kawomusu ruwa da abinci mana kima tashi ki cire uniform ɗinki ki huta,turo bakinta tayi don ita kunyar ta tashi tayi tafiya Lukman ya kalleta take,tace"Ammee basajin yunwa fa Allah ni ki ƙira Aysha tazo,Sabeer ne yace"to muje intayaki,Ummee wataƙil dai surikin kine anan shiyasa batason tashi,jin haka yasa Hanan tafiya kitchen ba shiri tana rufe fuskarta,Sabeer ne yabita ya taimaka mata suka jera abinci da drinks akan tray suka kawo musu Lukman kam kunya tarufesa dukda ba'a nuna shine maison Hanan ba amma yaji kunya saidai kawai dauriyar dayake,suna tsaka dacin abinci su Bappa suka shigo su ashirin ris hardasu Sani(Yaran Manga ba😄🤪),nan fa parlourn Amme yakacame da fira anatayi duk suka tada gidan kamar ana wani ƙaramin party don fita filin da'ake sport sukayi suka fara buga ball,bakajin komai sai ihunsu ana wasa da dariya,Ammee kam murna fal ranta don tayi murna da Sabeer ya ɗakko su Bappa gashi sunyi yawa a gidan kuma tana musu komai ba gajiyawa kamar ita tahaifesu,gashi gidan kullum baya shiru ga Bappa damo sarkin haƙuri,don duk cikinsu  Ammee tafi jin daɗin zama dashi sai Sani,sai la'asar lis sukabar gidan bayan Lukman ya zame yabarsu a bayan gidan suna wanka a swiming pool yaje gun Hanan,sun ɗan taɓa hira tukun suka tafi.

Zaune take a harabar gidan suna fira da Abuu Sabeer yaxo,tsugunawa yayi har ƙasa ya gaida Abuu,amsawa yayi yana murmushi ,Aysha kuma ta tashi zata wuce Abuu yace"a'a zauna bari in shiga daga ciki dama akwai abinda zanyi,bayan Abuu ya shige Sabeer ya zauna a kujerar da Abuu ya tashi ya kalleta yace"wana kama?,tace"Aysha Mrs Sabeer ka kama Inspector ,dariya tabasa wanda yasashi yinta hat dimple ɗinsa na lotsawa yace"kinganki ba,wato ɗazu shine don kinga su Fawaz shine kika shareni ko?,cikin murmushi tace"ni na isa kawai dai..."kawai dai miye uhmm ya ɗagr mata gira ɗaya,yace"sarauniyar kunya kawai,saida sukayi fira yasamu nustuwa sosai akan abinda ke damunsa tukun ya mata sallama ya wuce.

Saida safe yaje ma su Ammee anna yake sanar da Hanan cewa su shirya gobe yakaisu shopping tunda weekend ne ,tsalle tayi tay hugging ɗinsa tace"Wow Best Bro kamar kasan perfumes ɗina ya ƙare dama itada Aysha basa kwalliya saida ƙyer don haka insunje shopping a sun sayi kayan kwalliya su ɗauki powder da eye pencil da mascara,wanda hakam ma birge Sabeer don baisom mace mai shafe shafe,kumatunta yakama yace"Sleep tight lil sis i love you,tace"love u more,Ammee da kanta tamasa addu'a tashafamasa akai tukun ya fita,har yakai bakin ƙofa sai kuma ya dawo yace"Amee dama wani abu nakeson faɗamaki ko zaki amince,tace"inajinka Sabeer menene?yace"Ammee inba damuwa me zai hana Aysha tana kwana tare da Hanan,kallonsa tayi tace"inkanason hakan aiba matsala nima kuma nayi tunanin hakan Allah maka albarka,gobe saita dawo nan ɗin,rungumar Ammee yayi ya manna mata kiss a kumatu yace"U are the best mother that everyone can wish for,tace"u are the best Son every mother can wish for,Allah yaci gaba da muku albarka kaida ƴan uwanka ,ameen suka amsa tukun yafita.

Koda yaje ɓangarensu ya tadda duk sunyi bacci banda Bappa da Sani da suke jiransa zama yayi yace"Bappa sam fa banda lfya,Bappa yace"meke damunka haka,nan yabasu labarin abinda yafaru a office,Sani yace"Ikon Allah duk yadda akayi akwai wani ɓoyayyen sirri,Bappa yace"kaci gaba da addu'a kaji Allah zaisa komai yazo da sauƙi,nan dai sukayita kwantar masa da hankali yace"gobe Insha Allah ku shirya muje shopping dukanmu so nake gobe gidannan kaf mu ɗau gayya muje shopping,Sani yace"cewa zakayi gobe Mall ɗin lagos zai ɗauki ƙira,Sabeer yace"sosaima kuwa,Bappa yace"kaganmu nan haka zamuje mu kusan talatinfa,iyalan gidan ALHAJI HYDAR SABEER, murmushi Sabeer yayi yana mai jin daɗin yadda su Bappa suka ɗauki iyayensa kamar nasa.

Masoya kuɗanyi haƙuri da typing kaɗan,karku manta dayin share zuwa ga sauran groups.................plss.

Vote!!!!!!!!!!!!
Comment!!!
Share!!!!!!!!!!

Fans na wattpad karku manta da vote ngd.

Autar 🖊️💃
Youngest Writer.

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now