Na
Qurratul-aynASHIRIN DA DAYA.
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
Tsaraki na fita daga gidan jeji ya nufa ya yi ihu iyakar yinsa, ya yi birgima ya yi murna ya yi tsalle ya tuma a kasa yana wani irin kirari da kurari tare da wasu irin zantuka wanda shi ka dai yasan me yake nufi da hakan, take garin ya kara yin baki wuluk har duhun ya ninka na daren jiya, zama ya yi bisa kafafuwansa ya yi wasu irin dalasumai take hasken wuta kamar walkiya ya bayyana a gabansa, da wasu duwatsu guda goma sha biyar masu haske, rufe idanuwansa ya yi duwatsun na cikin hannunsa yana lissafi akan gobensa.
Abinda ya gani ne ya sanya shi mike wa a fusace, ya yi wani irin ihu da kurari take duhun garin ya yaye ya koma yanda yake da farko, kifa kansa ya yi a kasa yana gurza goshinsa tsabar kaduwa da dimauta, cikin wani irin gigitaccen ihu ya furta.
"Ishatuuuu!".
Firgigit ta farka daga barawon barcin da ya dauketa ba tare da ta shirya ba, salati ta yi a daidai sanda ta sauke idonta kan matashin saurayin dake zaune kan kujerar dake fuskantar ta ya zubawa mata ido tamkar TV da sauri ta tashi zaune tare da kokarin gyara jikinta kanta na kasa, ganin hakan da ya yi ne ya sanyashi kau da kai gefe ya mayar kan TV din karar bude kofa ta sanya su waigawa duka su Hafsy ne suka fito fuskokin su cike da nishadi, da sauri Samir ya sake hannun Hafsy ya karasa tsakiyar falon da sauri yana fadin.
"Aa babbar magana yau Khalid a gida na? Saukar yaushe?"
Ya tambaya yana mai mika masa hannu suka yi musabiha ko wanne fuskarsa cike da murmushi, shi kuwa gogan har lokacin ya kasa kau da idonsa daga kan Ishatu ko da ya yi kokarin hakan sai ya ji kamar mayan karfe na kara jan idon nasa kanta.
"Hasfsy ta kin tuna Khalid?"
"Ka jika kuma waye zai ce baisan abokinka Khalid ba, sai dai wanda bai zauna da kai ba?".
Ta fada tana mai fari da idonta suka sanya dariya, lokaci guda Ishatu ta mike da fadin.
"Mu tafi haka Hafsy lokaci ya tafi sosai".
Takai maganar tana mai duban agogon dake kafe jikin bangon dakin, Hafsy ma agogon dake daure jikin tsintsiyar hannunta ta duba da fadin.
"Kai Shatu ki jira lokaci kadan sai mu tafi".
Ishatu ta girgiza kawai ba tare da ta kuma furta komai ba ta nufi hanyar fita, da sauri Khalid ya mike yana fadin.
"Mu sauke su mana Samir".
"Dama ni na daukosu ai, Shatu ta gaji Hafsy muje na sauke ku kawai".
Hafsy ta dan daga kafada alamun babu damuwa hand bag dinta ta dauka tabi bayan Ishatu wacce tuni ta jima da yin wajen duk suka biyo bayanta, tsaye jikin mota Khalid ya tarar da ita saboda ya rigasu biyota, yana kokarin yi mata magana su Hafsy suka karaso a hankali ya daki saman motar kadan yana mai furzar da huci mai zafi kafin ya juya zuwa garesu da murmushi, Samir ya kunna motar, Hafsy da Ishatu suka shiga baya, yayin da Khalid ya shige gaba Samir na driven dinsu.
Sai da suka biya ta Rufaidah Yoghurt sunyi musu sayayyan kayan makwalece kafin su dau hanyar gidan nasu.
Motarsu na tsayawa kofar gidan Ishatu na bude kofa tuni ta wuce cikin gidan da sauri, Khalid ya yi ajiyar zuciya tare da kwantar da kai kan kujerar da yake zaune, Hafsy ta yi musu sallama tabi bayanta itama, Samir ne ya dawo da kallonsa ga Khalid ya dafa kafadarsa da fadin."Ya dai mutumin duk na ga baka da nutsuwa ko kadan?".
Ya kai maganar yana mai daga masa gira,Khalid ya dan gyara zama da fadin.
"Wannan yariyar daga kallo daya wallahi duk ta tafiyar min da dukkan nutsuwata".
Samir baisan sanda ya kece da dariya ba, har sai da Khalid ya kule kafin ya yi shiru ya dafa kafadarsa a karo ba biyu yana fadin.
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Ficción históricaKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa