BAHAGUWAR RAYUWA.

47 2 0
                                    

FITA TA TARA.

Na
QURRATUL-AYN

***

           Duk yanda Manya yaso ya gana da Zainaba abin ya faskara, gata dai tsaye a kusa da shi amma magana ta gagara a gareta illa dubansa kawai da take da ido alamu na nuna bama tasan me yake yi ba.
     Manya ya yi kwafa zuciyarsa na tafasa tamkar garwashin da ake hura wa, ji yake kamar ya rufe ta da duka amma babu damar yin hakan, Iyan Mairo dake lakance da yanayinsu ta karaso garesu fuskarnan tata sharkaf da ruwan hawaye, tana mai sharce hawayen tare da gyara zaman daurin kirjinta zata fara yi masa kwarkwasa ya bar wajen a fusace ba tare da ya ko dubi inda take ba, Iyan Mairo ta cije lebanta na kasa Kamar zata hudasu kafin ta kai wa Zainaba kallo na wulakanci ta kamo hannunta amma ko motsi bata yi ba, abin da ya kara baiwa Iyan Mairo mamaki kenan, ta dubi Zainaban da kulawa kafin ta ce.

   "Ke lafiya kike kuwa?".

Har lokacin Zainaba inda Manya ya bari ta kura wa ido babu ko kiftawa, Iyan Mairo ta janyo hannunta tare da dawo da Zainaba cikin mutane tana nazari da tunanin halin da Zainaba take ciki, sosai ta sanya wa al'amarin nata ayar tambaya.
      Ko da Manya ya fice daga farfajiyar gidan kai tsaye gidansu ya nufa domin karasa aikin da ya fara dazu, saboda a al'adarsu mata ke yin zama na mutuwa tsayin yini guda Asuba na yi shikenan kowacce zata kama gabanta, maza kuwa da zaran an binne mamacin kowa zai watse sai tashin labari kuma.

  Gaban abubuwan tsubbunsa ya zauna tare da nazari da lissafin taurari, abin da bai yi tsammani ba ya bayyana a gareshi kururuwa ya yi mai karfi tare da tuma a kasa ya yi birgima cike da kuna da dacin zuciya, har baisan sanda digon ruwan hawaye suka kwaranyo daga idanuwansa ba masu zafi da kuna, sosai ya manta ya sha'afa da cewar wutar tsafinsu sau daya take nuna abin da ya riga da ya wuce ba zata kara nunawa ba sai bayan shekaru goma sha biyu, babban kuskuren da ya aikata kuwa shi ne, yana tsaka da binciken ya tashi a lokacin kuma wutar daf take da hasko masa gaskiyar abin da ya faru, Mahaifinsa ya zo da batun mutuwar Innar Ishatu suka fice.

Manya baisan sanda ya buga kansa a jikin kasa ba tuni jini ya wanke masa fuska, amma duk da wannan azabar da yake ji yafi jin ciwo da zafin yanda zuciyarsa take tafasa fiye da zafin da goshinsa yake yi, kurawa wutar tsafin ido ya yi tsayin wasu sa'o'i kafin ya mike tare da fice wa daga cikin dakin baki daya ya nufi wajen Mahaifinsa.

        BAYAN KWANAKI UKU.

Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yayin da Innar Shatu ta yi kwana uku a kasa, haka Shatu ta shafe tsayin kwanakin ba tare da tasan abin da yake faruwa a gareta ba, kullum Dattijon nan yakan dura Mata ruwan magani sau uku a rana, sosai tana samun sauki illa dai rashin sanin inda kanta yake, kullum da yammanci ana fiddo da ita farfajiyar wajen saboda samun ishashshiyar iska, yauma kamar kullum da yammancin kwanaki uku da zuwanta wannan gari Dattijon na zaune farfajiyar gidan da sauran iyalansa suna tsaka da tsoro da fargabar rashin farkawarta kamar daga sama suka ga ta fara motsi kafin a hankali ta Ware idanuwanta akan fuskokinsu wanda suma kallon nata suke yi, yayin da kallo daya zaka yi masu kasan sosai sunyi farin ciki da farkawarta.

   Daya daga cikin matansa ta tallafota tare da taimaka mata ta jingina jikin dangar karan dakin kamar yanda Dattijon ya yi umarni a gareta, irin dangi na abincin su wanda mara lafiya zaici aka ajiye mata a gabanta, cike da lallashi da lumana matarsa ta sanya ta danci kadan tare da bata ruwan maganin ta kora abincin da shi, nan suka zauna suna masu cigaba da hirarsu kamar yanda bata yi magana ba babu wanda ya bukaci ji daga gareta harkokin gabansu kawai suke yi tare da bata kulawa.

    ***

  Duk yanda Dan Zabuwa ya so kamo bakin zaren al'amarin daya kulle wa Dansa Kai abin ya faskara, kwanaki biyu kenan ana abu guda daya har yau basu samu wata madafa ko da guda daya ba, Manya ya dubi Mahaifin nasa da kulawa kafin ya ce.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now