BAHAGUWAR RAYUWA.

51 1 0
                                    

NWA.

17.

Hafsy ta sake yi mata magana a karo na biyu tare da jijjiga kafad'arta kad'an, Shatu ta dawo da ga dogon tunanin data fad'a, daidai sanda Hafsy ta kalleta da murmushi tare da bud'e Mata murfin motar gidan baya tana mai yi mata nunin ta shi ga.
Ishatu ta sanya kai cikin motar zuciyarta na cike da rera addu'o'i kala-kala na neman tsari.

Tun da ta shiga motar Ishatu kanta na k'asa, bata fatan driven ya ga fuskarta, Hafsy dake zaune kusa da shi suke ta hira tsayin mintuna kafin ya jefeta da tambayar.

"Ina kika samo wannan kuma?".

"K'awata ce".

"Karki raina min hankali mana, kina son nuna min bansan k'awayen naki ba ne?".

"Sai aka ce maka su kad'ai ne k'awayena?".

"Ba nufina kenan ba, amma alamu sun nuna yarinyar farin shiga ce, domin na yi la'akari da tsoron da yake tattare da ita".

Hafsy ta yi ajiyar zuciya tare da watsa masa wani irin kallo na cikakkun 'yan bariki kafin ta ce.

"A nan na sameta, niyata mu wuce can wajen dinner din da ita kafin a tashi sai mu je gida tare, to amma kuma ina ganin kamar hakan zai takura mata, ko wajen Aunty zamu fara zuwa ka ajiyeta?".

Shiru ya ziyarci motar tsayin lokaci kafin ta sake magana da fad'in.

"Kamal kana jina kuwa?".

"Ke ! Ni fa duk tunanina ya tafi akan samun sabon nama".

Hafsy ta galla masa harara kafin ta ce.

"Ka da ma ka fara tunanin hakan wallahi, domin bana tunanin yarinyar ta san wannan harkar".

"Sannu ko?".

Ya fad'a ta cikin mudubin yana mai karewa Ishatu kallo ba tare da ya kula da maganar Hafsy ba, kai tsaye ya juya kan motar zuwa gidan magajiyar kamar yanda Hafsy ta fad'a masa, tafiyar mintuna talatin ce ta sada su da kofar gidan, Hafsy ta fito daga motar tana fad'in.

"Ka jira ni na fito, Ishatu fito muje".

'Ishatu'.

Kamal ya yi maimaicin kalmar sunan a cikin ransa, har suka shige cikin gidan yana bin bayansu da kallo kafin ya yi ajiyar zuciya yana raya abubuwa da dama a k'asan ransa game da Ishatun.

Tun daga yanayin k'ofar gidan zuwa tsakar gida Ishatu tasha jinin jikinta da al'amarin gidan, tunani ta dinga yi kala-kala tare da rokon Allah yasa ta fad'a hannun na gari.
'Dakuna ne birjit a gidan tsakar gidan ya haske da kwan lantarki, Mata ne kala-kala zaune a zagaye da wata k'atuwar mace mai cikar zati da kwarjini, tasha ado leshin dake jikinta kawai abin kallo ne ban da sark'ar kwal d'in dake damb'are a wuyanta mai manyan d'an kunne, suna shiga aka dakata da kidan k'waryar da ake yi, kowa sai binsu da kallo yake fuskokinsu kad'ai zaka kalla ka hasaso abin da ke k'asan ransu na tambayar WACECE ITA KUMA WANNAN?.

MAINA.

Dan zabuwa ya nemi sa'a akan kud'urinsa bayan shafe tsayin kwanaki da ya yi yana nazari da lissafin wuta da taurari akan neman mafita bai samu ba, abin da ruhinsa da tunaninsa baya so dole shi ne mafitar, ba shi da zab'in da ya wuce yin hakan a gareshi, kai tsaye bishiyar da yasan kullum nan ne dandalin zaman Tsaraki ya nufa tun kusantuwarsa garesu suka zuba masa ido domin karantar da yanayin da yazo garesu, bayan ya k'araso kallan kallo aka fara yi, kafin Dan Zabuwa ya yi ajiyar zuciya ya dubi Tsaraki da fad'in.

"Magana na zo muyi cikin masalaha da sirri".

Tsaraki yakai dubansa ga sauran abokansa kafin ya mai da kai ga Dan Zabuwa yana karewa yanayinsa kallo, mik'ewa ya yi sauran abokansa suka suka mik'e da nufin bin bayansu ya dakatar da su da nunin baya buk'atar su zo garesu.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now