SHA TARA.NA
QURRATUL-AYN.
***Alerm na wayar Hafsy da ya buga shi ne ya yi sanadiyyar tashinsu daga dad-da-dan barcin da ya daukesu baki dayansu har Ishatu wacce bacci barawo ya yi awon gaba da ita.
Hafsy ta mike zumbur da fadin."Lokaci ya yi, Ishatu kina sauraron shirin Masoyana a gidan Redion Express kuwa?".
"Aa Ni ban ma taba jin sunan shirin ba".
Ishatu ta bata amsa tana murje ido, Hafsy ta gyara zama tare da janyo wayarta tana kokarin nemo tashar Express cikin azama kafin ta cigaba da fadin.
"Azif Malami shi ke gabatar da shirin a duk ranar Juma'a da karfe hudu na yamma, ai gayen ya yi a rayuwa akwai murya mai kashewa masoyansa jiki, duk da dai ban taba ganinsa ba nasan Allah zai yi halitta a gare shi, nasan yau kika fara jin muryarsa kullum sai kin bukaci jin shirin".
Ishatu dai mike wa ta yi tsaye tana fadin."Lokaci ya tafi da yawa, gaskiya yau nasha barci har karfe hudu muna barci babu wanda ya tashe mu?".
"To waye zai tashe mu? Bari na gaya miki daga safiyya zuwa maghriba idan zaki kai kina bacci nan gidan babu mai tashinki, amma da zaran karfe bakwai ta yi dole ki tashi domin fita kasuwanci".
Ishatu ta tabe baki kadan cike da mamaki a cikin ranta ta furta.
'wannan kuma wacce irin BAHAGUWAR RAYUWA CE?'.
Amma a fili cewa ta yi.
"To ni dai bari na yi sallah".
Takai maganar tana mai shigewa toilet, Hafsy na fadin.
"Yanzu zai fara gabatarwa Allah ki tsaya ki ji sai ki yi sallar daga baya".
Ishatu dai ko kulata bata yi ba ta shige toilet, Hafsy ta kara gyara kwanciya cike da nishadi tana sauraron zazzakar muryar matashin saurayin Asif Kabir Malami mai shekaru Ashirin da takwas a duniya haifaffan garin kano, Mahaifinsa Kabir Malami sunyi aure da mahaifiyarsa auren saurayi da budurwa dukkan su a nan kano danginsu suke, sun gabatar da soyayya mai tsafta kafin ta kaisu ga aure, Mahaifiyarsa mai suna Fatima wacce suke kira da Umma a yanzu ta haifi yara biyar tare da mijinta.
Abubakar Sadiq shi ne babba suna kiransa (Yaya Bukar) sai Ummu-Salma da suke kira (Ummu) sai Azif sannan kannensa guda uku Jabir da Mukhtar sannan auta Fatima wacce suke kira zuhura.
Ya Bukar yanzu haka yana da digree na biyu yana aiki a Jami'ar BUK dake nan Kano, ya yi aure matarsa daya Mamy da yaransa guda uku maza biyu da mace, haka Ummu sai da ta gama karatunta kafin ta yi aure, ta auri wani likita mai suna Hassan Kasim gidansu nan unguwa uku tana da yara biyu Saddiqa da Abbakar, sun samu tarbiyar mai kyau a gun iyayensu kama daga ilmin addini har izuwa na boko, domin mahaifinsu Kabir Malami ya fison karatun addini fiye dana bokon ma, Azif bayan kammala digree dinsa ne ya nemi aiki a nan gidan Redion Express Kamar yanda ya bukata kuma yake da buri dama can Allah ya bashi, cikin ikon Allah kuma aka bashi rana daya wacce zai dinga gabatar da nasa shirin bayan wanda yake yi na news a duk safiyyar ko wacce rana da karfe takwas na safe.Ko da Ishatu ta fito tuni anyi nisa cikin shirin, bata bi takan Hafsy ba ta shimfida abin sallah domin gabatar da ramuwar azahar da la'asar.
***
Kwanaki biyu suka shude wa Tsaraki yana baje kalaman Dan Zabuwa domin nazari da lissafi, kafin ya yankewa kansa hukuncin da yake ganin shi ne kadai mafita a gareshi.
Dan zabuwa kuwa tuni ya fara cire rai da tsammanin amincewar Tsaraki da yammancin ranar yana farfajiyar gidansa yana faman safa-da-marwa ya ji alamun shigowar mutum gidan da sauri ya waiga domin ganewa idanuwansa gaskiyar lamari, cike da murnar da farin ciki da suka kasa boyuwa a gareshi ya tarbi Tsaraki yayin da ya ja hannunsa zuwa dakin tsafi domin cika alkawarin da ya dauka ga Tsaraki.
Ya zaunar da Tsaraki gaban wutar tsafi kafin ya koma gefe shima ya zauna tare da dauko wani skeleton na kan mutum ya dora bisa wutar shi bai fada cikin wutar ba, haka kuma bai bar saman wutar ba, ya rufe ido yana wasu irin d'alasumai wadanda sune kadai suka san me hakan yake nufi.
Tsayin sa'o'i sun shude suna abu guda daya kafin ka ce wani abu dakin ya yi duhu baka ganin komai sai hasken wutar dake faman canja kala-kala tana huci har tsayin wannan lokacin Dan Zabuwa bai daina abin da yake yi ba, kafin wani lokaci garin ya yi duhu lokacin daf da maghriba ce amma sai ka ce irin tsakaddare ne ya yi, wannan skeleton na kan ya juya yana fuskantar Tsaraki tare da fesar da wani hasken wuta zuwa saitin kirjinsa yana shiga jikinsa.
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Fiksi SejarahKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa