BAHAGUWAR RAYUWA.

45 3 0
                                    

16

Wattpad@JannaQurratulayn.

Wunin ranar Ishatu ta yi shi ne cikin sabulewar jiki, baki daya tunani da fargaba sun kanainayeta, kusantuwar yammaci ke kara dugunzuma dukkan lissafinta, karfin hali ne kawai ya kara kaita daren lafiya.
      Dukkan wani abu da Shatu zata yi a daren ta yi, sai da ta tabbatar ta kulle kofar dakin da window sosai kafin ta yi addu'a ta tofe ko ina sannan ta kwanta.
     Bacci farki daya ta ji haurowar mutum kan gadon nata, firgigit ta mike kafin ya sake yin wani yunkuri ta kurma wani uban ihun da yafi na jiya, abu mafi ban mamaki kuma jin da ta yi Mom da Salima na faman buga mata kofa alamun kofar dakin nata har lokacin a kulleta take, tuni jikin Shatu ya fara k'yarmar sanyi, a guje ta sauko daga kan gadon kafin ta kai ga kaiwa bakin kofa ya riko hannunta gam, suka fara kokawa Ishatu na kokarin kwace hannunta sun shafe tsayin lokaci a haka, Shatu na ihu da kururuwar ya cikata, bata san sanda takai bakinta ta gantsa masa cizo a hannun ba, ya sake ta da sauri tare da rike hannun, Ishatu ta juya a fusace zata karasa bude kofar, sai ganin gyallin kaifin wuka ta yi na haske kwayar idanuwanta, cike da kakkarwar jiki ta fara ja da baya yayin da ruwan hawaye ya fara ambaliya akan fuskarta, ba ta yi aune ba sai ji ta yi ta fada kan gado, shi kuma ya yi tsaye akanta yana dariya, Ishatu ta runtse ido tare da saddakarwar mutuwarta.

  A daidai lokacin Mom ta sanya spare key din da Salima ta je dakinta ta dauko da gudu ta kawo mata,take Mom ta fara kiciniyar bude kofar, Salima ta banko kofar ya fara shigowa tare da kunna globe na dakin haske ya gauraye ko ina, har a wannan lokacin idanuwan Shatu na runtse tana kyarma, Salima ta girgizata tare da kiran sunanta, firgigit ta bude ido tana mai fadawa jikin Salima ta saki wani irin kuka mai cin rai, Dad da ya shigo yanzu a guje yana fadin.

  "Lafiya ! Meke faruwa ne?".

Mom ta dubeshi kafin ta ce.

"Ni fa ina tunanin yarinyar nan gamo take yi da aljanu, tun da gidan nan yake ba'a taba shiga dakin kowa ba ki gidan ba'a taba haurowa ba, sannan 'yan uwanka na zuwa su kwana nan dakin haka nawa 'yan uwan amma babu wanda ya taba fuskantar wannan yanayin, babban abin dubawa ma ba'a shiga dakin Salima sai nan dakin?".

Dad ya gyada kai kafin ya ce.

"Maganarki da kamshin gaskiya, amma koma me ake ciki mu bari har zuwa da safe sai a yi wa tufkar hanci".

Ishatu da har lokacin tana kwance jikin Salima ta dago kai da sauri tana duban Dad cike da kallon tuhuma yayin da kwakwalwarta ke nazarin muryarsa tana jin tamkar ta taba sanin muryar, a fakaice take nazartar hannunsa saboda tunawa da ta yi ta ciji wancan mutumin, amma babu wani abu makamancin hakan da ya nuna alamun cizo a hannun nasa, Ishatu ta yi kasa da kanta har lokacin ruwan hawaye bai daina bin kan kuncinta ba, tsoro sosai ya gama shiga jikinta, duk rashin imanin Manya bai tana nuna mata wuka da sunan zai kashe ta ba, amma tana da tabbacin wannan shirye yake ya ga bayanta matukar bata bashi abin da yake bugata a tare da ita ba.

Mom ta umarce su da su koma dakin Salima kafin gari ya waye, kowa ya nufi makwancinsa, Ishatu dai bata ki kwanciya ba, amma yanda ta ga dare haka ta ga safiyar wannan rana, yanda ta wuni jiya haka yauma ta wuni jiki a sabule, duk tunaninta yana ga neman mafita a gareta, saboda Mom har ta fara zargin halin mutanen yau Ishatu ke shirin nuna musu, domin duk wata hujja na tabbatar da inda ake haurowa gidan har a shiga dakinta babu ita, hankalin Shatu idan ya yi dubu ya tashi har wata rama ta danyi na rashin kwanciyar hankali.

Yauma kamar kullum bayan sun gama hirar da suka saba kowa ya nufi makwancinsa, domin Mom ta ce ta koma dakinta da kwana zata saba da hakan, may be dan bata saba kwana ita kadai ba ne ya sanya take jin tsoron, ko da Ishatu ta shiga dakin nata kasa kwanciya ta yi, sai faman safa da marwa take yi ita kadai a dakin, yayin da ruwan gumi keta zarya tun daga goshinta har zuwa dan yatsan kafarta duk kuwa da sanyin AC dake kadawa kadan-kadan, lokaci zuwa lokaci takan kai dubanta jikin agogon bangon dake kafe dakin nata, tana lissafin lokaci, karfe daya daidai agogon bangon ya buga ta tabbata yanzu kowa ya yi bacci, domin har ta haddace lokacin da mutumin ke shiga dakin nata karfe biyu ne kullum, yau kuwa ta kudura a zuciyarta ba zata yi gangancin riskar wannan lokacin ba, domin ko bazai kashe ta ba, tana da tabbacin zai iya cimma burinsa akanta, cikin sanda ta bude kofar dakin nata tana tafiya ba tare da ta sako takalmi ba gudun tonuwar asirinta da zaran anji takun takalminta, mukullin dake rike kam a hannunta wanda ta sata a dakin Mom tun safe ta zare tare da bude kofar falon a hankali ta fi ce tana tafe tana aikin waige-waige, cikin ikon Allah har ta isa harabar gidan babu wanda ya jita,labewa ta yi, tana mai karewa kofar gate din kallo mai gadi na can dakinsa may be bacci yake yi, a hankali ta ajiye key din nan harabar wajen flowers, ta cigaba da taku cikin sanda har Allah ya sada ta da bakin kofar gate din, jikin karamar kofa ta nufa ta zare sakata a hankali tare da tura kofar tana sanya kafarta waje ta janyo kofar ta rufe, ganin ta da ta yi waje ya tabbatar mata tabar gidan su Salima har abada kwalla ce ta fara kokarin kawo mata, gudun ka da wani ya ganta ko a biyo bayanta ya sanyata takawa da gudu a kokarinta na barin unguwar baki daya.

   Sosai ta yi gudu wanda ita kanta bata san a wannin data shafe ba tana yinsa, sai ganinta ta yi babban titi babu kowa ga gajiya na damunta, wani guri ta zauna domi hutawa ta hada kai da gwiwa tana kuka tare da kewar su Salima tana mai yi musu fatan alkhairi a fili ta fara fadin.

  "Hakika alkhairi ba zai yi kaura daga wannan ahali  ba har karshen duniya, kun yi min taimakon da har bayan raina bazan taba mantawa da ku ba, kun bani ci da sha wajen zama, kun tufatar dani tare da bani ilmin da nasan koni wacece a duniya, iya hakan ma ya isa, bana so na zamto silar da kwanciyar hankali zai yi kaura daga gareku, addu'a ta ba zata taba yankewa ba a ko da yaushe, idan da rabon zamu sake gana a duniya zanfi kowa farin ciki , idan babu kuma ina rokon Allah ya hadamu a ranar gobe Allah ya yi sakayyar mafificin alkhairi a gareku".

Ishatu na kaiwa nan ta share ruwan hawayen da ya zubo kan kuncinta, kafin ta mike tana mai cigaba da tafiya a hankali cike da sassafar, can ta hangi damdazon mata tsaye bakin titi a hankali ta karasa dan nesa dasu kadan tana nazartar yanayin su, sosai ta yi mamaki ganin yanda manyan motoci ke tsayawa a gabansu suna shigewa, can wata dake gefe ta waigo da dubanta inda Ishatu ke tsaye ta zuba musu ido, kafin ta dauke kallonta ta dubi ta kusa da ita da fadin.

"Kin ga wata baiwar Allah can, da almu taimako take bukata?".

"Sai ki ba da himma ai sarkin tausayi, irin haka ne zai jaki ga taimakon aljanu".

"Ke fa Zee dadina da ke kenan, bakinki ba ya fadar alkhairi ko kadan, idan zaki ki zo muje gareta".

"Ni kam babu inda zanje sai kin dawo".

Wacce aka kira da Zee tana gama fadin hakan ta matsa can gaba kadan tabar budurwar tsaye, ganin da gaske ba zata ba ya sanyata karasawa zuwa ga Ishatu cike da sallama, Ishatu ta dago kai tare da amsa sallamar, kafin budurwar ta dubeta da fadin.

"Sunana Hafsat ana kirana Hafsy, ko mene sunanki?"

"Ishatu".

Ta bata amsa a takaice.

"Ishatu !".

Hafsy ta kira sunan cikin cigar maimaici, kafin ta cigaba da fadin.

"Ko mene ya fito dake cikin wannan daren?".

Da mamaki Ishatu ta dubeta jin irin tambayar data jefeta da ita, kafin Ishatu ta bata amsa ta cigaba da fadin.

"Duk fa yarinyar da kika ganta anan ba yarinyar arziki ba ce, amma ke yanayinki kadai ya isa sanarwa mutum ba kwanciyar hankali ce ta fito da ke da ga gida ba".

Sai lokacin Ishatu takai dubanta jikinta, ta tuna kafarta babu ko takalmi bare wani mayafi wanda zai suturta mata jikinta, da sauri ta ware dan kwalin dake daure kanta ta yi lullubi da shi, kasancewar riga da zani ne na atamfa a jikinta, Hafsy ta yi murmushi kafin ta cigaba da fadin.

"Kina bukatar taimkona Ishatu?".

Ishatu ta yi shiru kadan, tana nazari kafin takai dubanta wajen sauran 'yan matan babu kowa bakin titin, da sauri ta amsa da.

"E ina bukata".

Saboda tsoron idan ta bari itama tabar wajen nan bata San yalin da zata shiga ba, Hafcy ta sake murmushi a karo na biyu kafin ta mayar da kallonta gefan titi na jiran wanda take da yakinin zai zo, gefe guda kuma Ishatu kallon Hafsy take yi, musamman na irin shigar dake jikinta, domi ita a yanda take yanzu  sanyi take ji, bare ita da ko dan kwali babu akanta sai wani irin attachment da ta sha, ga wasu shegun riga da wando wadanda suka bi jikinta sosai, Ishatu na shirin yin magana mota ta yi parking gefan su tare da yin horn aka zuge bakin glass na motar, Hafsy ta sunkuya kadan bayan wasu yan mintuna ta dago kai da murmushi ta dubi Ishatu kafin ta ce.

"Bismillah Ishatu shiga mu tafi".

Takai maganar tana mai bude mata gidan baya, Ishatu ta yi tsaye sororo tana nazari da tunanin. '

'Ta shiga motar ko ta barsu su tafi kawai? Domin bata fatan sake fadawa hannun mugun iri'.

Tofa ! Amsa na gareku masoyan Ishatu, ku bata shawara tana nan tsaye zaman jiran jin shawarar da zaku bata.

SAKON GODIYA.

Sauki ya samu masoya, nagode da sosai gareku tun daga masu text har zuwa call Allah yabar zumunci da kauna, masu min addu'a a grp na ga sakonku nagode matuka.

  Sai gobe idan Allah ya kaimu yana nan tafe da yardar Allah Nagode Sosai.

BAHAGUWAR RAYUWA.
NA
FIRDAUSI S. ALIYU (QURRATUL-AYN).


BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now