BAHAGUWAR RAYUWA.

72 1 0
                                    

NWA®.

Na
QURRATUL-AYN.

Wattpad@JannatQurratulayn.

FITA TA SHIDA.

WASHE GARI.

Washe gari ma da garin ya waye Mai garin Maina bai gajiya ba wajen sake baza mutane domin kara neman inda Ishatu take, ciki kuwa har da Manya shi ne kan gaba afujajan da shi, fuskarsa na dauke da kwantacciyar damuwar da dukkan wanda ya ganshi ba sai ya tambaya ba yasan tabbas abin da ya sanya shi cikin wannan halin babba ne a gare shi.
            Dukkan tsayi da fadi, tudu da kwari na garin Maina babu inda basu duba ba karshe haka suka hakura suka rankayo izuwa cikin gari domin tabbatar da cewar ba'a ganta ba.

    Sosai Innah da Zainaba sunfi kowa shiga damuwa da wannan al'amari, musamman dawowar su Manya a yanzu bayan sanar da mutan fada kai tsaye Tsaraki gida ya shigo ya sanar da cewar ba'a ganta ba, tuni Innah dake tsaye ta fadi kasa sumammiya mutanen gida suka yi caa akanta da kyar aka samu ta farfado tare da sauke doguwar ajiyar zuciya, Zainaba kuwa can kuryar daki ta shige ta hada kai da gwiwa tana aikin rizgar kuka mai karyar da zuciyar ma'abocin sauraron sautin kukan a lokacin.

                                 ***

BAYAN KWANA BIYU.

       Sannu a hankali ta bude idanuwanta da suka yi mata nauyi, dishi-dishi take gani a lokaci guda kuma kanta ya cigaba da sarawa tamkar ana dokawa da guduma, hannu ta kai cikin jin kasala da mutuwar jiki ta dafe kanta da ke yi mata barazanar tarwatsewa a lokacin, sannu a hankali idanuwanta suka waye da hasken dake haskaka dakin kadan-kadan sai lokacin ta lura da yanayi na inda take ciki zuciyarta ce ta harba da karfi cikin azama ta yunkura da nufin tashi tsaye domin tabbatar da gaskiyar abin da giza-gizan idanuwanta ke yi mata nuni da shi, amma sai me ? Ji ta yi jijiyoyin kafafuwanta sun daure ta kasa sarrafa sauran gabban jikinta bare har ta samu kwarin gwiwar mikewa, bata san sanda ta kurma wani uban ihu ba a daidai lokacin da idanuwanta ya yi mata tozali da abin da ba bata yi tsammani ba, dago kanta ta yi da sauri fuskarta wanke da ruwan hawayen da ya jikata har gaban rigarta a sauke kallonta inda ta ji motsi gefanta kadan.

   Yana zaune tamkar wani gunki ya kafa mata idanuwan nan nasa masu ban tsoro, a hankali ta iya bude baki ta furta.

"Sakayyar da zakamin kenan?".

Murmushi ya yi mai kama da kuka yayin da ya mike tsaye ya tako izuwa gareta ya tsugunna daidai kanta kafin ya kau da kai gefe guda da fadin.

"Hakan naga ya da ce da na yi, kina tunanin zan iya hakura da cikar burina? Kina tunanin Manya yana lamuntar faduwa a gareshi?".

   Ya danyi shiru kadan yana dubanta kafin ya cigaba da magana.

"Ba laifina bane na zuciyata ne, domin a duk lokacin da zuciyata ta aiyana abu tunanina da kwakwalwata basa iya sauraronta bare har su canja mata ra'a yi, bazan lamunci nisantarki ba, kamar yanda bazan iya zuba ido ki zama mallakin wani ba fa sai ni, na yi tunanin mafita guda daya tun kafin Tsaraki ya furta dakatar da aurenmu na riga da nasan za'a yi hakan, kina tunanin zan gaza daukar mataki ne? Shatu ke tawa ce dole zaki rayuwa dani ta har a bada, idan kuwa kin ki zan cigaba da rainonki a nan matsayin FARKATA domin bani da zabin da ya wuce haka na jima da sanin cewar bakyasona amma hakan ba zai taba damuna ba domin Manya baya rashi bana kuma lamuntar faduwa a rayuwata ba kuma zan fara  akanki ba, domin ko baki tsaya kin rayu dani ba a yanzu baki da wata daraja da kima a cikin gari na Maina suna da asalinki sunriga da sun baci, bazan takuraki da ki aure ni ba, kamar yanda bazan hanaki auren wanda kike so ba amma ki sani yanzu dake da ka...!".

Tasss.! Tass.!! Sautikan saukar kara mari biyu ya gauraye wajen, a fusace manya ya kai dubansa ga Ishatu wadda ke faman tsuma da kakkarwar jiki tana girgiza kai har lokacin kududdufin idanuwanta bai daina ambaliyar ruwa ba, duban da ya yi mata da yanda idanuwansa suka kada jajir ya sanya 'yan hanjinta Kara daurewa, ji ta yi dama mutuwa zata kawo ziyarar bazata a wannan lokacin ta huta domin tasan sai ta gwammaci mutuwa akan hukuncin da Manya zai shuka mata na rashin imani, mamaki take da tunanin yanda aka yi ta samu zarrar iya marinsa.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now