Na
QURRATUL-AYN.FITA TA SHA UKU.
KANO.
Kwana uku a jere kullum Mai gidan kudi sai ya zo Ladi ta aiketa kai kaya a leda wanda Shatu bata taba sanin abin da yake ciki ba.
Yau ma kamar kullum yazo a bakar motarsa, lokacin rumfar ta cika dankam har da Ya'u da abokansa, Ladi ta baiwa Shatu leda viva takai masa, kasancewar abin ya fara zame mata jiki bata ko damuwa, ta fi ce daga rumfar tare da kai masa yauma haka ya miko mata rafar kudin ta sanya hannu takarba tare da godiya, da alamu sauri taye yi bai tsaya batun janta da hira ba yaja motarsa yabar wajen Shatu ta kamo hanya ta dawo cikin rumfar, tare da cigaba da harkokin gabanta.
Can ta dubi Bilkisu da fadin.
"Wai ina Furaira ne? Yau kwana uku ban kuma sanyata a idona ba?".
"Tun yaushe Ladi ta mayar da ita daya gidan abincinta".
Takai maganar tana mai yatsina fuskarta, kafin ta matso kusa da Shatu sosai tana fadin.
"Saboda ganin kusancin da ke tsakaninku ya sanya ta kaita can gidan, bansan wanda ya kai mata tsegumin ba".
Shatu bata sake tanka komai ba ta yi shiru, tana nazarin maganar Bilkisu.
'kenan tafi so kowa ya yi rayuwarsa shi kadai? Ko ni ce take yi wa haka? Babu komai zan yi biyayya a komai ma domin taimakona take yi'.
Daga haka ta yanke tunanin nata tare da mikewa ta cigaba da harkokin gabanta, amma duk da hakan zancen Furaira na cinta a rai sosai, ta so a ce taga fuskar Mai gidan kudi ko da sau daya ne a rayuwarta.
Duk wannan shige da ficen da take ta yi Ya'u na nan zaune bai tafi ba, har yamma likis abin ya bata mamaki matuka, ta karaso gareshi da fadin.
"Lafiya kake yau Ya'u?".
"Lafiya kalau, me kika gani?".
"Gani na yi har tsayin wannan lokacin kana zaune, abin da ban taba ganin yi ba".
Shiru ya yi tsayin lokaci kansa a kasa yana nazari, kafin ya dago ya dubeta da fadin.
"Magana nake son yi dake".
Shatu ta janyo daya daga cikin kujerun wajen mafi kusa da ita ta zauna, tana mai fadin.
"Ina jinka, Allah yasa dai lafiya?".
"Lafiya kalau insha Allah, tambaya ce dama kawai zan yi a gareki, mene ke tsakaninki da wancan mutumin?".
"Wanne mutumi kuma?".
"Wanda kike kaiwa sako kullum".
"Ohh Mai gidan kudi ! Babu abin da yake tsakanina da shi, Ladi ke aike na kai masa sako kawai".
"Amma yake baki kudi masu yawa, alhalin babu abin da yake tsakaninmu?".
"Gaskiya babu komai a tsakaninmu, farko da ya bani bana karba Ladi ta ce na dinga karba ina kawo mata".
Ya'u ya yi shiru yana nazarin maganganunta, itama shirun ta yi tana sauraron abin da zai ce kuma.
"Shatu ko kusa zamanki anan bai da ce ba, sai dai ban sani ba ko kema a shirye kike domin zubar da kima da mutuncinki?".
"Ko kusa Ya'u ban baro gida da dangina akan yawon duniya ba,sai dan gujewa abin da gobe zata haifar, amma duk da hakan bana fatan nabi wata hanya wacce bata da ce ba".
"To sarkin iyayi ! Itama ka zo ka hure mata kunnen ne, Ya'u ka dainamin irin haka, sai ka zama wani mummuni kamar kai din na kwarai ne, sau nawa nake jin labarin kana ziyarta 'yan matan Tudun hayi can gidana, amma ka zo nan kana wani kumbura da iskar banza".
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Historical FictionKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa