NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
ASHIRIN DA HUDU.
NA
QURRATUL-AYN.***
Idanuwan Ishatu suka yi tozali da wannan matar da ta taimaka ma ta da ruwa, da murmushi matar ke dubanta kafin ta ce.
"Baiwar Allah daga ina haka, Kuma ina za ki je?".
"Bansan inda zanje ba".
Matar ta sake dubanta da mamaki kafin ta cigaba da magana.
"Amma me ya fito dake daga gida?".
Tambayar ta daki kunnuwan Ishatu, kafin ta dago kai a karo na biyu ta ce.
"Na fito ne daga wani waje mai nisa, kuma bansan kowa ba anan".
"Kina bukatar taimako na?".
Ishatu ta yi shiru, matar ta cigaba da fadin.
"Tashi muje gidana ki huta, nan kan hanya ne".
Takai maganar tana mai riko hannun Ishatu domin taimakonta wajen tashi, da kafa suke tafiya saboda gidan nata bashi da nisa daga bakin titin, suna isa kofar wani madaidaicin gida matar ta sanya makullli (key) ta bude kofar gidan tana fadin.
"Bismillah nan ne gidana".
Ishatu ta sanya kai tabi bayan matar kai asama tana mai karewa gidan kallo kafin su isa ga falon gidan ta baiwa Ishatu umarnin ta zauna, ita kuma ta fita zuwa wajen tsakar gidan jim kadan sai gata dauke da tire ba abinci ta ajiye mata a gabanta tana fadin.
"Bismillah abinci".
Ishatu ta yi murmushi, matar kamar ta shiga zuciyar Ishatu itama murmushin ta yi kafin ta ce.
"Ni da zuciya daya na taimake ki, ni ba mai cutarwa ba ce baiwar Allah ki ci abinci ki huta, amma kafin nan sunana Zainab ke kuma fa?".
Ambaton Zainab da matar ta yi sai da zuciyar Ishatu ta harba, sosai kuma ta ji matar ta burgeta, kafin ta bata da amsa da fadin.
"Ishatu".
Ta bata amsa a takaice yayin da ta sauka daga kan kujera ta zauna gaban abincin ta fara ci a hankali saboda rashin sabo da fargabar abinda gobenta zata haifar, tunaninta ya katse a daidai sanda ta tsinci maganar Zainab cikin kunnuwanta.
"Idan kin gama ga daki can sai ki shiga ki yi wanka ki sallah zan kai miki kaya yanzu na ga dare na yi alamu kuma sun nuna kina bukatar hutu".
Suka saki murmushi a tare, yayin da Zainab ta mike ta nufi wata kofa a falon da alamun shi ne dakinta, jim kadan ta fito hannunta dauke da wata doguwar riga ta nufi dakin da ta yi wa Ishatu nuni da shi dazu yayin da Ishatu ta bi bayanta, Zainab ta dubeta da murmushi kafin ta ce.
"Ba dai har kin gama ba?".
"Na koshi wallahi nagode sosai".
"A haba karki damu babu komai kinji, yanzu dai ki huta domin kinga tara na dare da safe ma gaisa sosai".
Bata jira jin abin da Ishatu zata ce ba ta fi ce daga dakin, Ishatu tabi dakin da kallo sosai komai ya tsaru kai tsaye kofar da take tunanin bandaki ce (Toilet) ta nufa, kafin wasu mintuna ta fito daure da towel alamun wanka ta yi, doguwar rigar kawai ta sanya tare da daukan hijab ta sanya ta nufi inda abin sallah ke shimfide ta tayar da kabbarar sallah.
Khalid kuwa mai gadinsa ya sanya a gaba suka karade unguwar nan kaf wajen neman Ishatu amma ko sahun kafarta basu gani ba, a gaggauce ya koma cikin gidan tare da daukar waya ya dannawa Samir kira, Hafsy da ke kusa da wayar ta dauka kafin ta yi yunkurin yin magana Khalid ya tari numfashinta da fadin.
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Tarihi KurguKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa