BAHAGUWAR RAYUWA

74 2 0
                                    

Na
QURRATUL-AYN

Wattpad@JannatQurratulayn

FITA TA UKU.

WASHE GARI.

Ishatu bata san sanda bacci ya yi awon gaba da ita ba a wannan daren tana aikin tunani, mummunan mafarkin da ya jiyarceta a cikin bacci shi ne musabbabin silar farkawarta, a firgice ta mike tana waige-waige jikinta sharkaf da ruwan gumi tamkar wacce ta yi gudun famfalake, shi gowar Zainaba a lokacin shi ne ya yi sanadin fargar da ita gari ya waye, dubanta Zainaba ta yi da fadin.

"Tun dazu nake zarya Inna na fadin ka da na tashe ki domin kin gaji".

Ishatu ta dafe kanta dake yi mata barazana tamkar zai tarwatse, Zainaba ta dubeta cike da kulawa kafin ta ce.

"Lafiya kike kuwa Ishatu?".

"Lafiya kalau Zainaba, bari na wanke ido mu tafi, har an fara taruwa ko?".

"Tun yaushe kuwa, guri ya cika fam babu amarya".

Ishatu ta mike cike da karfin hali ta dauki butar duma wacce suke amfani da ita ta zagaya bandaki, mintuna kadan ta fito ta tsiyaya ruwa a hannunta ta wanke fuska da hannu da kafa ta dawo daki tana fadin.

"Karki gaji bari na yi shafa".

Ta janyo man shanu da suke shafawa tare da kwalli da wata farar hoda a dunkule ta goga a jikin wani abu ta shafa, tare da zane fuska da kwallin babu laifi tafito sosai, matsalar dai zanen kwallin dake kan fuskarta, Zainaba ta dubeta cike da zolaya kafin ta ce.

"Wannan kwalliya karki janyo Manya ya ce gobe a daura aure".

Ishatu ta bayyanar da murmushi kan fuskarta ba tare da damuwa data mayarwa da Zainaba amsa ba, ita kanta Zainaba tasan dama ba lallai ta tanka matan ba, mikewa suka yi a tare suka fito farfajiyar gidan nasu mata dankam sai dake-dake suke da wakoki ana ta hira da shewa, Iya Larai dake fitowa daga cikin daki tana mika da dukkan alamu da ga bacci ta farka lokacin, idanuwanta ta sauke kan su Ishatu dake shirin wucewa ta gabanta ta ja dogon tsaki tana mai rero wakar habaicin da take yi wa Ishatu a ko da yaushe.

"Ba girman gidan ba.
Mace ta yi kwantai ake guda.
Ta bige da auren biri-biri.
Ta yi kwanan bakin ciki.
Iya na can neman sulen daka..".

Zainaba ta yi kwafa zata juya, Ishatu ta riko hannunta da nufin su wuce kawai, amma sai da ta juya ta tanka mata.

"Dadin abin kema kin haifa, waya sani ma ko taki 'yarce zata kafa kafaffan tarihin zaman gida a garin Maina".

"Ahir dinki Zainaba, bakinki ya sari danyan kashi wallahi, aniyarki ta biki".

"Aniya sai dai tabiki algungumar mace mara sanin darajar na kasa da ita da, Allah ya rabani da bakar kunamar matar uba, an girma hallau ba'asan an girma ba..!".

Iya Larai ta zaburo har zanin sakin dake daure a jikinta na shirin faduwa kasa saboda daurin kirjin dake jikinta, Ishatu ta yi saurin janye Zainaba suka fice da gudu, lokacin har matan gidan sunyi ca akan su, Innar Zainaba na faman yi mata fada, nan suka bar Iya Larai tana kumfar baki, kowa dake yasan halinta su Zainaba na ficewa kowa ya koma harkar gabansa, saboda ita maca ce mafadaciya da shuka mugun iri a rayuwarta, ta iya shirya magana kuma dole Baban Ishatu ya yarda, kome ta fada a gurinsa daidai ne ko da kuwa ba daidai din ba ne.

"Kin fiye jan magana Zainaba, yanzu idan nabar gidan haka zaki dinga biye mata kuna wannan abin".

"Ni fa saboda ke da Iyata nake daga kafa wallahi, ina zan iya jure wannan cin kashin na Iya Larai wannan sai ku da Allah ya bawa hakuri, me ake da irin wannan hakurin da za'a dake ka a hanaka kuka kuma?".

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now