NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
NA
QURRATUL-AYN.ASHIRIN DA UKU.
Wayar shi dake a jiye gefe kusa da shi ta fara rurin neman a gajin gaggawa duba daya ya yi mata kafin ya dauka yana fadin.
"Bismillah ku shigo".Ishatu ta baza ido tana tunanin su waye zasu shigo kuma? Bugun kofar da aka fara yi ne ya yi sanadiyyar kara mai da hankalinta kacokam bakin kofar, Khalid ya mike a hankali tare da karasawa bakin kofar ya bude musu maza ne suka shigo su uku dauke da manyan kwalaye suka a jiye a falon bayan sun gaisa da Khalid suka kara fi ce wa mintuna kadan suka dawo da wasu kwalayen ita dai Ishatu ido ne nata ta zubawa sarautar Allah.
Sai bayan da suka gama shigo da kayan ya dubesu da fadin."Ga dakin can".
Nan da nan suka shige da kwalayen sai lokacin Khalid ya dubi Ishatu yana fadin.
"Kayan dakin za'a canja miki, kafin mu fita siyo kayan sawa".
"Duk wannan hidimar saboda me?".
"Saboda kin ce ba za ki yi amfani da tsohon kaya ba".
"Aka ce maka zama na zo yi kuma?".
Da mamaki Khalid yake dubanta, ita kuwa sai sannan ta lura da barin zancen da ta yi, a fakaice ta wayance da murmushi.
"Guduwa za ki yi kenan?".
Tambayar ta zo mata a bazata, kafin ta bashi amsa da.
"Aa tsokanarka na ke yi kawai".
Khalid guntun murmushi ya yi wanda da ganinsa bai wuce kan lebansa ba.
"Za ki aure ni?".
Ta ji kalmar ta saukar mata tsakiyar kai tamkar saukar tsakuyoyi, da mamaki takai dubanta gare shi kafin ta iya daga labbanta da suka yi mata nauyi ta furta.
"Aure kuma Khalid, aure fa ka ce?".
Kai ya gyad'a mata tare da lumshe ido saboda tsoro da fargabar yanda zata dauki zancen ya hanashi yin magana, ita kuwa daga wannan tambayar tsuke bakinta ta yi, domin rasa amsar bashi a lokacin, hakan ya sanya shiru ya ziyarci falon kowannen su da abinda yake sakawa cikin ransa.
Tsayin a wanni suka shude har bacci ya sace Ishatu a lokacin kafin ma'aikatan su fito suna yi wa Khalid sallama sun gama komai, sai lokacin ta farka ta yi mamakin baccin da ta yi, Khalid kuwa tare suka fi ce da ma'aikatan da yiyuwar sallamarsu zai yi.
Ganin hakan ya sanya Ishatu mikewa da sauri ta nufi dakin, baki ta saki ganin yanda aka kawata dakin lokaci guda, da kwalaye Suka shigo gidan amma an tashi wasu set na gado masu shegen kyau, abin sosai ya burge Ishatu matuka."Ko ina aka kai sauran kayan oho?".
"Ta sama suka tashi".
Da sauri ta waiga bayanta jin muryarsa da ta yi, murmushi ya yi kafin ya ce.
"Wasa nake yi miki, kina barci aka fi ce da su".
Guntun murmushi ita ma ta yi, saboda ko kadan ba ta yi tsammanin a fili take maganar ba.
"Dakin ya yi kyau ko?".
Banza ta yi masa tana kokarin ficewa daga dakin ya katseta da fadin.
"Da alamu anan zamu ci amarcin mu ni ma dakin ya burge ni kuma".
Bata waigo ba ta cigaba da tafiya abinta kamar da ga sama ta tsince shi gabanta kafin ta yi yunkurin ratsewa ta gefansa ta wuce, a falo ya cimmata yana fadin.
"Dan Allah Ishatu karki ce a'a hakan zai cutar da zuciyata ne da gaske na yarda na amsa ina SONKI ina son auren ki".
Ishatu ta ja ta tsaya tsakiyar falon Kalamansa sun daureta da jijiyoyin jikinta, da kyar ta iya da ga kafafuwanta ta isa kan kujera ta zauna har tsayin wannan lokacin bata tanka masa ba haka kuma bata dubi inda yake ba.
Shi ma neman guri ya yi ya zauna tare da kafeta da idanuwa zuciyarsa na kuna da suya shi a burinsa ko da sau daya ta furta wata kalma amma taki hakan, kamar daga sama ta jita cikin jikinsa a fusace ta waiga tare da tureshi ta mike tsaye ta kafe shi da idanuwanta kafin ta ce.
YOU ARE READING
BAHAGUWAR RAYUWA
Fiction HistoriqueKubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa