chapter 13&14

15 0 0
                                    

💖🌷NANCY Y'AR  K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._

_story and writing_

      By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE  13_14

____ Hajiya ce tace" akwai wasu kud'a d'e da take  bina sunkai , dubi d'ari uku , zaro ido Duduwa tayi, saboda  har tafara tunanin kalar gidan dazata siya bayan an biya ta kud'inta,

Hajiya ce tafara wani 'irin tari kana wani , miyau _wato yau mai kumfa yafara biyo baya , tana gamawa rai yayi halin sa, kowa na hospital d'in saida ya tausaya mata bare yaran da Hajiya tabari , wani 'ihu Duduwa ta kurma tana cewa, na shiga uku bani da gata sai Allah, ganin kukan 'nata yayi yawa ne yasa doctors d'in sukayi waje da ita,


Anty Humaira ce tadin ga kiran waya tana gayawa y'an uwa rasuwar Hajiya , hak'ika mutuwar ta ta6a kowa saboda Hajiya bata da son duniya ,

😭Allah kasa muyi k'ya k'yawan k'arshe amen 🤲.

Bayan rasuwar Hajiya da kwana biyu, y'an uwan Hajiya suka ce zasu tafi da su Humaira garin su,
Duduwa bata gama tabbatar da , rasuwar Hajiya ba sai lokacin da wani dattijo wato d'an uwan Hajiya ya kira ta, yana cema ta yanzu kulle gida zasuyi saboda , umarnin Hajiya zasu bi,

Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo mata , duk da kud'in da take ganin kamar inta samu zata warke , amma yanzu jikin ta yayi sanyi sosai,

Washe gari ta tattara kayan ta tana neman gidan haya , cikin ikon Allah tasamu wani mutumi da yake kusa da gidan su yana dashi a can wata anguwa ta' talakawa ana kiran anguwar Riga y'ar kasuwa ,

Tambayar shi kud'in hayar tayi , cemata yayi dubu hamsin shekara d'aya ,  bayan sunje gidan tagani tace" mai yama ta uzuri saboda ba'a bata kud'in taba , cikin 'nuna rashin yarda yace" sai dai tabari 'in aka biyata sai ta koma ,

Gidan da mutumin ya kaita gidane mai kyau ma'ana 'akwai siminti kuma akwai bayi a ciki ga kitchen a waje bayi a d'aki ,

Mata biyu ne a cikin gidan kuma duk zasu girme ta d'aya tana da miji d'ayar kuma karatu ne ya kawo ta saboda bazata iya zaman hostel ba,

A yau ne akayi bakwai d'in Hajiya, an sallami Duduwa kud'in da Hajiya ta buk'ata 'a bata, alhamdulilah uncle yabata dubu d'ari uku da hamsin , kuka Duduwa takeyi sosai saboda 'a ganin ta sunyi mata hallacci,

*Wayoo kud'i 😫 Anty Nancy bani aron two thousands🤨*

Bayan sun su Anty Humaira sun k'ara bata kaya sabba bi dakuma gyale da hijab , sosai suka yiwa juna fatan sake had'uwa , daganan Duduwa ta tattara akwatin ta zuwa anguwar da takama haya , bayan ta biya wanan mutumi dubu hamsin ,

Da shigar ta gidan taci karo da wata datijuwar mata da 'a shekaru zatakai sittin a duniya , gaisheta Duduwa tayi kana ta nemi d'akin da 'ya zamo nata ,

Tunda tazo birni bata tunanin komawa k'auye saboda wahala zatasha 'a can ,

Tana zaune tana tunani , taji wayar ta na neman agaji , duba number tayi ganin Khalil yasata sauke gwau ran nunfashi , daga can 6an garen shi yace", kya kyawa yakike yasu momy ?cikin sanyin jiki tace lafiyan su lau , daganan yafara janta da hira , bata wani sake sosai ba , ganin haka Khalil yace"kodai baki da lafiya ne ?eh tace "daganan yayi mata fatan samun sauk'i sukayi ssallama,

Washe gari ta 'tashi da wani matsa nancin ciwon kai , saboda kukan data sha jiya da daddare , ganin wata jaka mai kwalin lifton har , uku yasata duba sauran kayan dake ciki suga na da bonvita dakuma biskit na shan shayi, in bazata manta ba Anty Humaira ce tabata leledar....✍️✍️✍️.

_mom Islam ce_

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️

NANCY ƳAR ƘARYAWhere stories live. Discover now