chapter 21&22

15 3 0
                                    

💖🌷NANCY Y'AR  K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._

_story and writing_

      By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE  21_22

____Bayan ta wuce cikin gidan tasami muta nen gidan a zaune suna hira,da wanan tsohuwar matar dakuma wanan budurwar, bayan tayi sallama sun amsaata sannu tayi musu ta shige cikin d'akin ta , kamar jira sukeyi ta shige suka fara gulmar ta , wanan tsohuwa da 'ake kira da baba Dije tafara cewa kinga yarinyar nan duk lokacin da zata fita saita dawo da leda k'atuwa , to wai ma ina iyayen ta ne? ita dai wanan budurwa mai suna Nafisa batace komai ba saboda yawan magana ko gulma bai dame taba, baba Dija data gama surutanta ta wuce d'aki ."

Nancy ce zaune a d'aki tana sak'a da war wara , saboda 'a yanzu ne lokacin da take buk'atar iyaye acikin al'amuran ta, 'amma gashi tazo tayi watsi da iyayen ta , tana cikin tunani ne taji wayar ta na ruri, d'auka tayi had'i dayin sallama , cikin sa'ssanyar murya tace" Khalil nazo gida lafiya kaifa? ka koma gidanne¿".

A kasalan ce yace" kya kyawa bazan iya bacci ba muddun bansaki a idona ba , zaro ido tayi kamar yana ganin ta cikin sigar lallashi tafara magana , kamar mai shirin yin kuka   tace"dan Allah ka huta mana nifa ina cikin kwanciyar hankali, k'ara marai raicewa yayi kana yace kodai baki san zuwana ne , da sauri ta katse shi tana cewa ina ai ban isaba 'amma please kabari sai zuwa gobe,
Babu inda ya iya haka ya hak'ura 'amma badan yaso ba, ita ko Nancy tunani ne yayi mata yawa tarasa wanne zata kama, washe gari tayi shawarar bude account saboda 'ajiyar kud'in ta 'a halin yanzu tanada dubu dari hud'u saboda ranar dasukaje gidan su momyn Khalil ta zuba mata kud'i a cikin ledar dakuma 'atamfofi da kayan makeup."


Washe gari ta shirya bayan tagama breakfast , tad'au hand bag d'inta tanufi bank ,saboda akwai masu bayani bata sha wuyar fahimtar komi ba, da dubu hamsin tadawo gida , bayan tayi sallahar azhar ne ta kwnta a madai daiciyar katifar ta' takuma fad'awa kogin tunani ."


Gashi Khalil yace zai zo gidan su yau ,to ita bata san yaya zatayi da rayuwar taba, wata dabara ce tafad'o mata ,shiryawa tayi ta nufi gurin kayan ta akwati k'arami ta d'auka dayake cin kaya kala goma ."

Azama tayi ta nufi gurin da ragowar kud'inta suke ta sasu a hand bag d'in ta 'ta  fito bayan ta kulle d'akin ta nufi gurin, mutanen gidan tayi musu sallama , Nafisa ce tace" Nancy kibani number ki mana ko madinga gaisawa , amma dai ba dad'e wa zakiba? Nancy tace"eh gaskiya bazanfi two weeks ba ."

Da isar ta  bakin titi ta nufa ,tayi sa'ar samun mota da wuri bayan ta isa tashar motoci ne taji ana cewa saminaka ,saura mutum biyu motar ta cika ,
Bayan tabiya kud'in motar ne , tana shirin zama taji wayar ta na ruri , amsawa tayi had'e da  sallama bayan sun gaisa ne yake tambayar ta 'akan tayimai kwa tancen anguwar su, cikin yanayin damuwa tace gani a tashar mota zani garin su kakar mu ,saboda jikin 'nata yak'i ankoma da ita gida, cikin sauri yace kina wacce tasha ne?".

Ina tashar saminaka tabashi amsa , cemata yayi to kijira ni ganin'an zuwa yanzu , to kawai tace mai , bayan wasu lokuta  saiga Khalil nan ya iso ......✍️✍️✍️.

_Afuwan👏kunsan dai banida lafiya shiyasa kukaji ni shiru love yau all my fan's_

_Mom Islam ce_

*Please share*
*Comments*
Vote✔️

NANCY ƳAR ƘARYAWhere stories live. Discover now