chapter 27&28

22 4 2
                                    

💖🌷NANCY Y'AR  K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._

_story and writing_

      By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE  27_28

___Jikin Umma ne yayi sanyi tana tunanin to idan tabi Duduwa ita gurin wa zata zauna , kamar Nancy tasan tunanin Umma, matsowa tayi ta kama hanun Umma kana tace" indai gurin zama ne Umma baki da matsala , jikin Umma babu k'wari ta 'amince da bin 'Nancy ABUJA , aikuwa Nancy najin haka ta rungume Umma tana murna , mik'ewa tayi ta fice zuwa d'akin ta nada ta kunna wak'a jirgin so ,ta Umar m Sharif , tadinga tik'ar 'rawa , tsgai ta rawar tayi kana tafara maga tana cewa, ai tunda Umma tace zata bini angama saboda 'auran Khalil babu fashi muddin iyayen Khalil suka san 'ni y'ar talakawa ce to na shiga uku, amma yanzu tunda Umma ta 'amince no problem zan san inda zanyi , tunda inada kud'i Kuma zan d'inga tatso Khalil ,tana cikin maganar ne taji Umma na k'awala mata kira ,ficewa tayi a guje taje kiran Umma".

Umma ce ta dubi Nancy tace ki fad'amin gaskiya , mene ne dalilinki nason inbiki?"zaro ido Nancy tayi a zuciyar ta tana cewa 'ai nad'auka mun wuce gurin , Umma ce ta katse mata tunani da sabuwar tambayar da takuma jefo mata, ganin bata da mafi ta yasata fara kuka tana bawa Umma hak'uri akan abubuwan da suka faru bata fad'a mata ba ta bata labarin mutuwar Hajiya dakuma kudin da haliya tace abata , dakuma 'alkairin Khalil da momyn shi."


Salati Umma tayi tace" to yanzu a ina kike zaune ? Nancy ce tace" gidan haya nakama, shine naga zaifi kyau tuwa mukoma tare , Umma tayi na'am da shawarar Nancy, dan haka  suka fara had'a kaya dan barin gari ."

Washe gari  Nancy ta kwashi kayan da tasiyowa Umma dakuma wanda momyn Khalil ta bata takai gurin d'inki kayan kala bakwai ne  tace" ayiwa umman ta d'inkin zamani."

Nancy ce zaune tana tinanin yanzu ta gama da fannin Umma saura, na Khalil , saboda idan har ta dawo to zai ze zo, gai da maman ta dan haka dole ta nemi mafita , number mutumin da yabata hayar gidan da take ciki  , ringing d'aya ya d'aga ,  daga can 6an garen yace" dawa nake magana ? Nancy ce tace "nice wace take haya 'a gidanka Nancy, washe baki yayi kana yace" lafiya dai ko?eh lafiya tace" mai ,can kuma ta nisa tace dama so nakeyi ka samar min gida mai kyau tsararre me tails , washe baki yayi kana yace "akwai gidaje sosai , kinga inada wani a WUSE 2 shi price d'insa dubu d'ari biyar ne ,akwai wani a A Y A shi kuma price d'insa dubu d'ari uku , sanan akwai wani a WUSE 2  shi kuma price d'insa dubu d'ari buyu da hamsin ."

Tunanin ragowar kud'in ta tayi yanzu sau ran dubu d'ari hud'u , cemai tayi ina son 'na WUSE 2 d'in amma kasan banfi wata biyu a gidan kaba, zaka bani ragowar kud'in , mutumin ne yace" karki damu shi na WUSE 2 d'in kibada dubu d'ari biyu ,inyaso sai 'in cika da ragowar kud'in ki godiya tayi mai suka yi sallama ."

Washe gari Nancy ta kar6o kayan Umma'a gurin d'inki ,Umma tayi farinciki sosai akuma sanya mata 'albarka, Nancy ta hana Umma d'aukar kayan ta saboda bata san Umma tasa Khalil ya ganota wasu ,sababbin hijab guda uku ,tabawa Umma, sun gama had'a kayan da zasu buk'ata sabo da washe gari zasu koma 'ABUJA.....✍️✍️✍️.

_Mom Islam_

*Please share*👏

NANCY ƳAR ƘARYAWhere stories live. Discover now