💖🌷NANCY YAR KARYA 💖🌷.
Story and writing
By
ZAINAB HABIB
{Mom Islam }_Mom Islam tadawo🚴
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 31 & 32
,,,,,,,,,Ragowar kud'inta ta d'iba tacewa umma zataje siyo kayan gado , zata fita taji wayarta na ruri ,tsayawa tayi ta 'amsa kiran ganin Khalil ne yasata mumishi tace ”ranka shidad'e dafatan kana lafiya ?lafiya Lou yace ”mata daganan yace ”to ganifa 'a hanyar zuwa gidan Ku ,zaro ido tayi tacemai wallahi yanzu bana gida ,ummace keson sauya kayan d'aki shine naje bakin titi zantafi gurin mai kayan ,Khalil ne yace ”to kibar ganinan zuwa yanzu saimu wuce ,wani tsalle ta doka ta tsaya tana jiranshi ,mintiuna kad'an sai gashi yayi parking ,saida ya matso da motar dai _dai saitin ta tukun ta shige suka wuce ,suna zuwa ,tacewa mai kayan gado nakeso da katifa nawa ne ,mai kaya ne yace ”kinsan kud'i kud'ine wanne kika za6a ,wasu masu tsadar gaske ta nuna ,gaya mata kud'in yayi zaro ido tayi, tana tunanin idan kud'inan suka k'are yazatayi ?cewa mai kayan tayi to gaskiya kud'in data bani basukai ba yanzu kabani na dai _ dai kud'ina ,Khalil ne yace ”am kabamu gadon data nuna dakuma katifa da bedside duka dai kayan dakasani harda dining chair ,zaro ido Nancy tayi tace ”walhi kud'i ne tsugugu kabar wanda yasamu ,ko kulata baiyi ba yasa 'akasa kayan a mota yasa Nancy tabasu address din gidan ,bayan tabasu shikuma Khalil yace ”to Shiga mota muje itadai binshi kawai takeyi amma hidimar tafara yawa ,gurin masu kayan kallo sukaje yasiya musu TV jibgege da sauran kayan aikuwa farinciki bai 6oyu a fuskar taba ,rungumeshi ne kawai batayi ba."
Gida suka nufa ,wasu masu yimai aiki yakira yayi musu kwatancen gidan su Nancy 'yace ”suje ankawo kaya susa komai yayi kyau ,babu damuwa sukace daganan yakashe wayar ,suna shigowa 'anguwar yayi parking motar shi ,Nancy ce tafara hawaye ,hankalin Khalil ya tashi ya dubeta yace ”Nancy meke faruwa ?please gayamin ,cikin wani salo tace ”bansan da bakin dazanyima godiya ba ,hak'ik'a ka can canci godiya to nikam ina ganin godiyar ma tayi kad'an ,murmishi Khalil yayi yace ”no karki damu, abu d'aya zakiyi ki biyani shine ki aureni ,farr tayi da ido takuma kashemai 'ido d'aya tace ”kullum ina mafarkin hakan ,nandai sukayi hirarsu ,yace ”zai shiga ya gaida su momy ,to Nancy tace ”barinje in sanar mata ,to yace ”daganan ta shige gidan samun umma tayi ta shimfid'a tabarma 'cikin azama ta isa gurin Umma tace ”umma Khalil nefa zai shigo gaisheki ,gyara hijab umma tayi tace ”to kicemai yashigo man ,Nancy ce tace ”umma ina lefin yashiga ciki ?umma ce tace ”nima fitowa nayi a cikin d'akin tunda masu gyara suka shigo ,amma 'a ina kika sami mak'udan kud'in siyayyar nan ?dariya Nancy tasa tace ”umma walh amma dai kibari zuwa 'anjima zanbaki labari barin shimfid'a masa sallahya, fita tayi tace ”ka shigo OK yace ”ya bud'e bayan booth yayi ya ciro wata k'atuwar leda ya shiga da ita ,umma da ganinshi tafara washe baki tana mai sannu da zuwa ,bayan ya zauna ne ya sunkuyar da kansa k'asa 'alamun girmamawa yace ”ina yini umma, lafiya lau tace ”yasu maman 'naka ?tana lafiya kuma tace ”a gaisheki ina 'amsawa umma tace ”Nancy ce tafito d'auke da ruwan gora dakuma cin cin ,lokacin umma na shirin mik'ewa tayi gaba tabarsu ,zama tayi nesa dashi tayi shiru ,kallonta yayi yace ”to wa kika kawowa¿kai mana ,tabashi amasa ,Khalil ne ya sha ruwan ya d'auki cin cin biyu yaci, daga nan yace ”nikam zan tafi ga wannan kibawa umma ,godiya tayimai ta rakashi har bakin mota tana d'agamai hannu."
Washe gari dadyn Khalil na hanya ,hidima momy take shirya masa sosai yau dakanta take girki ,gidan sai tashin k'amshi yakeyi , Khalil ne yashigo yake cewa momy dady fa yakusa sauka, saura 30 minutes momy ce tace ”ai nagama mutafi ,airport suka wuce ,lokacin jirgin 'na gaf da sauka ,Khalil ne yanemi guri yazauna yana cewa momy lokacin fa yayi ,bai gama rufe baki ba saiga jirgin yana sauka, jama'a ne suka tattaru kowa na jiran wanda yazo tarya ,momy sai dad'a bud'e ido takeyi ,aikwa ta bud'e a dai _dai 'idanunta sukayi tozali da dady da sauri taje ta rungumeshi ,shiko Khalil sai alokacin ya ga dadyn , dady ne yace ”ba'a girma ko ?"dariya sukasa ,wata farar yarinya ce budurwa kya kyawa tana sanye da riga da wando ,na Jens ta d'aura rigar sanyi a kwankwason ta ,rik'e take da hannun dady tana yiwa su momy murmishi...
Momy ce tace ”bak'uwa mukayi ne ?dady ne yace ”Suhailat ce ko kin mance ta ,momy ce tayi shiru alamun tunani ,Khalil yace ”please kuzo mu wuce ,shigewa motar sukayi Khalil yana driving d'insu ,Suhailat ce taketa satar kallon Khalil, shiko baisan tanayi ba ,da isarsu gida hira ta 6ark'e aka wuce dining cin abinci ,dady ne yace ”my son zoka cikawa Suhailat plet ,dariya sukasa dukkan su shikuwa Khalil jiyayi yarinyar bata kwanta masa ba...
Abincin yafara zuba mata momy kuma na zubawa dady ,Suhailat ce tace ”brother kabarshi haka ,banacin abinci over ,wanan ma tare zamuci ,zaro ido Khalil yayi ganin tana magana ko kunyarsu dady bataji ba ,wani kallo yayi mata itako murmishi ta mayar masa,dady na lura da yanayinsu itako momy hankalin ta nakan dady."
Dady ne ya kalli Khalil yace ”to da 'abar abincin ya lalace ai gara kuci tare ko ? shiru Khalil yayi ,yasa cokali suka faraci Suhailat na cikin cin yanga dubawar dazatayi taga babu komai duka ya cinye, 6ata rai tayi tace”sai kuma nace maka na k'oshi ko¿" Khalil ne yaga su momy sun tashi ,wata muguwar dariya yasa ya bud'e food flaks ya zubo mata abincin da yawa ,zaro ido Suhailat tayi tace ”kad'an fa zanci danma inason jollof mai kifi ne ,ko kulata Khalil baiyi ba ya zaro bell d'in wandonshi yace ”wallahi ko kici abincin anan kokuma na zzaneki."
Allah ya zubawa Suhailat tsoron bulala haka ta fara tura 'abincin tana tsayawa zai ce saita ci kuma yace” bayason ,nishin kuka haka taci abinci mai yawa da k'ayar take tafiya rasa wane d'aki zata shiga tayi ,parlor ta koma ta kwanta 'a kujera .
Bayan anyi sallahar la'asar ne kowa na parlor dady ne yace ”Khalil ya kasuwa ?alhamdulilah yace ”daganan dady 'yace ”banyi muku bayanin Suhailat ba ko ?amma ke momyn Khalil ai kinsanta saidai kin manta da ita, momy ce tace ”eh to ina buk'atar tuni ,dady ne yace ”kin mance brother na ABDURRAHMAN ?"shiru tayi tana kallon Suhailat can kuma tace ”yanzu itace ta zamo haka tabb lallai girman d'an mutum babu wuya ,dady ne yacewa Khalil to ga Suhailat nan tunda taganka 'a photo tace”saita biyoni zatazo ta ganka ,humaid ne yace ”to nagode ,murmishi take jifanshi dashi amma ko kawota 'a gabanshi baiyi ba .
Washe gari ta tashi da wani matsanancin ciwon kai ,momy ce tacewa Khalil yazo ya kaita hospital cikin fushi ya shigo d'akin da yazamo nata 'yace ”inkinyi ra'ayi zaki 'iya tashi munafuka kawai ,dariya ma yabata duk da ciwon kan daya matsa mata bai hanata darawa ba ,k'ufula yakuma yi ya zo kusada ita ya kaimata rank'washi a kanta jin zafin rank'washin yasata kurma ihu ,da sauri momy ta fito daga bedroom d'inta ta shigo d'akin ,ganin Khalil a tsaye yasa momy cemai to maiya faru naji kina ihu ,cikin shagwa6a tace ”momy nakasa tashi ne.....✍️✍️.
Mom Islam ce 😘