💖🌷NANCY YAR KARYA💖🌷.
_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_
_________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 39_40
,,,,,,,,,Sanye yake cikin bak'in yadi mai laushi ga shek'i ,fuskar sa na sanye da bak'in glass wanda ya rufe kyawa wan idanunsa,gyara tsayuwar ta tayi tace ”Khalil !!! lumshe murmishi yai tare da ”cewa mai kyau kin manta dani ko?" hawayen da take k'ok'arin tarewa ne sukayi nasarar zubo mata ,ya ilahi yafad'a lokacin da ya bud'e murfin motar yana shirin fitowa ,ji yakeyi kamar ya rungume ta ko zuciyar sa zata yimai dad'i ,juya masa baya tayi tana share hawayen fuskar ta ."
Takowa yakeyi cikin tak'ama ya iso gurin ta ya sunkuceta tana k'ok'arin sauka 'amma babu hali sbda Khalil d'in ba rago bane , yasata a mota key yai wa motar suka bar wajen ,sunyi tafiya mai nisa babu mai magana sai sanyin AC dake kad'awa had'e da had'a d'en turare mai k'amshi , guraren da Khalil ke shiga tunda tazo Abuja bata ta6a shiga ba ganin yana shirin shiga wani katafaren guri mai kamada Zoo yasata ware ido bata daiyi mgna ba ,da shigarsu gurin aka Khalil yaciro kud'i yabada 'aka basu wani kati ,yana tafe tana binsa 'a baya ,mutane ta hango iri _iri har dasu turawa da sauransu kowa kagani a gurin tafe take da saurayin ta wasu na d'aukar hoto wasu kuma na wasa da flowers wasu kuma na gurin cin abinci , wani guri taga Khalil ya shige yana yimata nuni da tayi sauri, da shigarsu ta hango kayan ciye ciye wanda tasani da wanda bata sani ba ,Khalil ne yace ”zoki za6i abinda ranki keso ,shiru tayi tana kallon shi ,k'arar wayar shi ce yasata kuma maida hankali gurin kallon shi ,tsaki yayi yace ”ke wace irin dak'i k'iya ce menace miki jiya don't worry zanbaki mamaki ba lefinki bane ,ya kashe wayar ,kuka Nancy tafara ,ta fice a guje tana kuka ,Khalil ne yasami guri ya zauna yana cewa wlhi Suhailat karkiyi tunanin farinciki zaki tarar a gidana lol."
Wasu y'an mata ta hango sanye suke da dogayen wanduna na jeans dasuka kama jikinsu ,d'ayar ce tace ”dan Allah sis zoki rakani gurin wacan beautiful d'in inason muzama k'awaye ,tashi sukayi suka nufi gurin da Nancy ke zaune tana kuka tana ganin mutane sun doso gurin ta tafara share hawayen fuskar ta, sallama sukayi ,bayan ta amsa musu ne suka fara janta da hira kasancewar sunga bata cikin walwala , tad'an sake dasu sosi d'ayar ce tace ”ni sunana Jamila ita kuma lil sis sunanta Karima ,masha Allah Nancy tace ”tana k'are musu kallo sbda tasan dukkansu ba 'ajinta bane jikinsu ma ya nuna daga inda suka fito ,Karima ce tace ”to baki fad'a mana sunanki ba ,murmishi Nancy tayi tace ”sunana Nancy nice name Karima tace lokacin da take ruk'o hannun Nancy ,amma Nancy naga kamar kina cikin damuwa ko ,eh tace ”can k'asan zuciyarta batason susan halinda take ciki ,amma lokaci guda taji ta yarda dasu ,kwashe labrin soyyayar su da Khalil tayi dakuma labarin Suhailat tabasu babu abinda ta 6oye musu , murmishi sukayi suna cewa to yanz ai kece da laifi because dayace dadynsa ya....hango Khalil tayi yana shirin tahowa gurinsu .....✍️.
Zanyi typing anjima 'amma innaga sharhi 🥰.
Banga sharhi sosai ba shiyasa kukaga rubutun kad'an👌kudaure ku sanbad'o sharshi nima in daure in sanbad'o muku