Chapter 23&24

17 2 0
                                    

💖🌷NANCY Y'AR  K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._

_story and writing_

      By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 23_24

____DA isowar sa yafara dube dube, ganin bai san motar data shiga ba, yasa shi ciro wayar shi a cikin aljihu, number ta ya danna ,yana cikin kiran 'ne ya hango ta cikin wata mota dake kusa dashi, lokaci d'aya ida nuwan su had'e ."


Sakkowa tayi daga cikin motar jiki a sanyaye tazo kusa dashi , kana tace" barka dazuwa ,yauwwa yace" mata 'a tak'ai ce , bayan shirun daya wanzu tsaka ninsu , Khalil ne ya katse musu shirun ta hanyar 'ruk'o hannun ta , jin wani yanayi a tare dasu yasa ko wannen su idanun su 'sukawo ruwa 'alamar hawaye ,
K'ok'arin janye hannun ta tayi daga na Khalil shikuwa kamar jira yakeyi wasu hawaye masu zafi suka zubo daga kuncin sa , bazata iya jure ganin kukan saba yasata juya baya ."

Jitakeyi 'inama 'ace mijin tane data nuna mai soyayya marar misaltuwa , ganin tsayuwa tana neman ga gararsu ne yasa Khalil juyo da ita tana fuskan tar shi , ganin idanun shi sun koma launin ja yasata cemai kaga mota tacika ni ake jira zan tafi saimun sake had'uwa, a san yaye yace" Nancy menayi miki dahar zaki gujeni ?gashi kin d'auki k'atuwar jaka , mir mishin yak'e tayi kana tace" soyayyar ka tana cikin zuciyata karka damu bazan dad'e ba insha Allah."

Murfin d'in motar ya bud'e kana ya d'ibo wasu ledoji manya guda biyu , mik'owa Nancy yayi , cikin farinciki ta k'ar6a tana yimai godiya sabuwa waya 'ya mik'a mata , zaro ido tayi tana cewa"to wanan ta hannuna inyi yaya da ita? ranshi a 6ace yace"oho nidai nasiyo kuma dole kiyi using da ita, cikin zuciyar ta tafara tunanin menene using ? ganin kar asami matsala yasata cewa to nagode Allah yak'ara bud'i ."

Amin yace"kana yace " please karki dad'e bata iya  sake kallon shiba ta shige mota ".

Khalil sai da yaga tashin su sanan ya shiga motar shi jiki a sanyaye , tana cikin mota yakira ta yakai sau goma duk saboda yaji muryar ta , bayan ta sauka ne ta 'tari mai adai daita yakai ta 'anguwar su ,bayan yafad'a mata kud'in tahau suka wuce , suna cikin tafiya ne wani yaro mai suna Ahmad lokacin tana k'auye shine abokin wasan ta , yana ganin ta yafara cewa" oyoyo DUDUWA tadawo ."

Runtse idanun ta tayi kana tafara cewa wallahi dana sani daban dawo wanan k'auyen ba kowa yahau samaka ido , a haka dai tak'arasa zuwa gida ".

Da shigar ta suka had'a ido da umma ,  wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar Nancy , dagudu ta rungume Umma  tana cewa oyoyo umma na , k'arasawa d'aki sukayi daganan , suka shiga hirar yaushe gamo."

Nancy ce take cewa Umma nikam ina Dillaliya ne? nisawa umma tayi kana tace "Allah yayiwa dillaliya rasuwa!!!.

Cikin yanayin kid'ima Duduwa tace" yaushe kenan umma? bayan umma ta share hawayen da suka zubo mata tace" bayan kun dawo babu jimawa tafara ciwo sai dai tace "min zaki kasance cikin kwanciyar hankali a gidan da kike , Duduwa tayi kuka sosai , umma batayi yun k'urin hanata kukan ba , sai da tayi mai 'isar ta kana tayi shiru."

Bayan sunyi sallah ne taci farfesun da umma tayi mata , ta d'auko kayan tsarabar da tazo dasu , atamfofi ne guda biyar dakuma takalma biyu da hijab ,umma tayi murna sosai harda hawaye, kayan da Khalil ya siya mata ta d'auko dan batasan meye a ciki ba ."

Madara ce ta gwan gwani guda biyu manya sai millo dakuma biscuit da butter babbar roba , d'ayar ledar kuma kayan makeup ne dasu English wear riga da skirt dogo har k'asa sai riguna musu tsada sai kuma atamfa guda biyu."

Mik'awa umma tayi ,Umma na ganin haka tace" waye yabaki wanan ?"....✍️✍️✍️.

_Mom Islam ce_

*Please share👏*
*Comments*
Vote✔️

NANCY ƳAR ƘARYAWhere stories live. Discover now