Zarrah

804 25 0
                                    

*_Zarrah_*


*_Fauziyya Tasiu Umar_*
       *_Oum Hairan_*


*_17-18_*

Miqewa yayi yana shirin shiga daki ta riqoshi ta baya tace “wai da gaske kunne na yakeyi kaine kake fadawa Mimee zakayi aure Aseem da gaske hakane? Please tabbatar min domin nasan tudun dafawa"  kama hannunta yayi ya zaunar da ita yana binta da kallo yace “ba kamar yanda kowanne aure yakw nawa yake ba Mimee idan kika tashi hankalinki ke kikaga dama da kanki zan Aure ne domin ramuwa da daukar fansa,  idan baki manta ba nataba baki lbrn wata yarinya data mareni ta fasamin yatsa kwanakin baya,  to itane zan aura,  a zahirinta ba ajina bace kuma ba tsarata bace ni kaina inajin kunyar hadaka ta da ita ina qyaqqyaminta wlh don an daina cinikin bayi ne da siyo miki ita zanyi matsayin baiwa ki rinqa morarta


Dakatar dashi tayi da sauri tace “shut up Aseem banason yaudara da zalimci ni zaka wulaqanta ashe dsma abinda ake fadamin gsky ne Wayyoh Aseem meye nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...." Rufenta baki yayi yana girgiza mata kai yace “kada ki kawo komai a ranki ba haka nake nufi ba har abada kece zabina kece burina kuma kece zuciyata wlh da gaske yarinyar nan don ke na aurota nasan zata taimaka miki


Sake dagansa hannu tayi ta miqe da gudu ta nufi dakinta ya bita da sauri  daqyar ya samu ya shawo kanta bayan yayi mata manyan alqawura masu  wuyar cikawa yana qara rantse mata baso bane zaisa ya auri Asmah kawai gayya ce to ganin yanda ya zage yana rarrashinta yasata sakin jiki amma duk da haka kishin mijinta yana cinta a ranta duk da tayi ammannar bai isa ya wulaqantata ba kodon soyayyar da mahaifiyarsa takeyi mata dole yabi umarnin uwarsa saboda haka ta yanke shawarar binsa ta qasa zata hadashi da hajiyansa tasanta sarai bata hada hanya da takala balle  kuma ta bari a kawo mata yar  matsiyatan qarshen zamani matsayin suruka da wannan tunanin suka fita ko a hanya aikin rarrashin mimee yakeyi suna shiga harabar gidan  yaji gabansa yana faduwa so yayi ya juya amma INA ya makara yana daga Kansa ya hango hajiyansa saman bene ta zubawa motarsa ido dole tasashi fita yabi bayan Mimee data shige gdan a qofar falon sukayi karo da Hajja ta daukeshi da mari ya dafe  gurin  da tafukan hannunsa yanajin zugin marin  saman jar fatarsa yana dagowa ta sake daukeshi da mari tana kumfar bakin  cewa yanzu Aseem har kayi qwarin da zaka nemi aure  batare da ka sanar dani ba saidai naji a wajen qannenka....."
Hawaye Mimee ta goge tace “ai dole bazai fada miki  ba Hajja wai  ya rasa dawa zai hadani kishi saida yar  talakawa...." Dafe qirji  Hajja tayi tace “na shiga uku ni  Saratu yar  talakawa Aseem ina  ka samota me suka Baka suka sauya maka tunani  ni  zaka wulaqanta yanzu yaushe ma akayi aurenka da Maryam da har zaka tattagowa kanka aure  kuma auren ma memakon kaci gaba sai kawai kaci baya to wallahi baka  isaba dole ka hqr da wannan dan  iskan auren naka  ka zauna da matarka dana  zaba maka"


Shidai  tunda yayi qasa da Kansa bai dagoba sai yanzun yace “wlh Hajja ba haka bane kawai...." Buge masa baki tayi tace kawai Ubanka ka kiyayeni Aseem zanci ubanka wlh dama na lura shine yake  daure maka gindi  shi ko ubanme ya hanashi auren mace sama da dayan sai kai da quruciyarka zaka dorawa kanka wahala to indai na isa  dole ka janye ban amince ba bakuma zan amince ba"
Juyawa tayi  ta shige parlournta ta barshi tsaye itama Mimee tabi bayanta a sanyaye ya juya ya fice daga gdan yanajin zafin abinda Hajja tayi masa yanzu meye laifinsa don anyi masa ba daidai ba yayi shirin daukar fansa  zaayi masa wata  fassara ta dabam bandama  abinsu shi meye zaici da wannan banzar yarinyar da bata isheshi kallo ba"


Da wannan tunanin ya nufi gdan Jabir yake  fada masa abinda ke faruwa sosai shima Jabir ya jinjina abin ya dubesa yace “to kai tunda abin baiyi nisa ba ka hqr mana kasan dai  halin Hajja shi kansa  Dad hqr yakeyi da ita" girgiza kai yayi yayi murmushi yace “nifa babu abinda zaisa na janye akan qudurina saidai kowa yayi hqr kamar  yanda nake  haqurqurtar da zuciyata ta karbi auren idan na janye dama  haka Asma'uh da nahaifiyarta sukeso farin ciki  zasuyi nikuma ba burina  suyi farin  cikin ba saboda haka kawai aci gaba da tafiya a haka tunda Dad ya karba  mgnr kowa ma kada  ya karba" da wannan tunanin ya miqe ya nufi gdan Yayarsa Aseemah itace kadai me sauqin yanayi a wajenta yake  tunanin samun mafita game da auren nasa yana zuwa ta tareshi da fara'a tana tsokanarsa nan yake  zube mata abinda yake  ransa sosai tayi murna ta tayashi fatan alkhairi yayi shiru kamar  bazaice komai ba sannan ya dago yace.
“Banasonta Sister na rasa meye yasa na dage  wajen Neman auren ta yar  talakawa ce  Allah ina  qyaqqyamin kaina inajin kunyar nunata matsayin mata talauci yayi musu kanta nifa badon  quduruna a kanta ba da tuni na hqr ko na samu nutsuwa"


Zubansa ido Aunty Aseemah tayi har saida  ya rufe  baki tayi ajiyar zuciya tare da murmushi tausayin Asmah yafi komai narkar da zuciyarsa duk da tasan cewa qarya Aseem yake  yace bayasonta domin tasan zuciyarsa idan babu burbushin son babu abinda zai darsa masa son auren ta matsalar kafin ya aminta ya yarda  yanasonta tasha wahala kawar dakai tayi tace “kaje kayita addu'a qila rabone tsakaninku kasan  ba kowa ne yake da Baiwar gane  abinda yakeso a qaramin lkc ba" sosai ta rinqa basa  shawara wata  yakan dauka wata  kuma ya watsar da ita domin yasan bazai iyaba"
Baibar gdan ba sai bayan magrib ya nufi gdansa har lkcn Mimee bata dawo ba dakinsa ya shiga yayi wanka  ya dawo ya kwanta  a parlour ya kunna kallo.


**********

Tunda suka koma  gda  batada aiki  sai tunani  damuwa taqi damunta babban abinda yafi damunta shine yanda Sadiq ya manta da ita ko a hanya suka hadu sai ya kawar mata dakai  koma ya buleta da qurar sabon lifan dinsa wannan Abu nayi mata ciwo gashi batada Wanda zata zauna tayi hira dashi taji dadi duk da zuwa yanzu sun daidaita da yan'uwanta so ta lura suma  yan son zuciya ne har garama Dijangala ita ta fahimci akwai matsala tana tausayawa Asmah sosai musammam da taga kowa saurayinta yana zuwa gurinta suyi hira itakam Asmah Aseem tun  ranar da aka sallamosu daga asibiti bai qara takowa gdansu ba saidai ya aiko Jabir duk ta rame  abinka da mara  jikin dama babu abinda kake  gani sai dogon hancin da idanu duk rawar kannan  da fitsarar  Asmah tayi laqwas ko mgn wahala takeyi mata ana haka aka kawo lefen su Dija samarinsu sunyi qoqari sosai babu laifi a matsayinsu na talakawa kwana biyu tsakani aka kawo na Asmah ranar har wanda  basa  mgn dasu saida  suka shigo ganin wannan lefe na al'ajabi


Lkcn bikin saura sati guda amma shiga shagalin biki itadai Asmah tunda aka fara bikin tana kwance a dakin da akayi musu na yaran gda  batada aikin daya wucce kuka  duk da fitsararta tasan haqqin Miji akan mace sosai yanzu indai ta bari aka daura auren nan shikenan ta zama nama duk yanda yaga dama  haka zaiyi da ita? Hakan ba qaramin karyar mata da zuciya take ba ana saura kwana biyar  tana gdan maqotansu tana kwance kasancewar ba Lfy ce ta isheta ba yaro  ya shigo  yace “wai ana kiran Asma'uh a waje" ajiyar zuciya tayi ta gyara kwanciya Jiddarh tace “ki tashi kije mana kinsan  shima wannan dan  Aiken ba qaunar jira yakeyi ba"
Tsaki tayi tace “kije kawai" sanin halinta ne yasata miqewa tace “bazakiyi mana buqulu ba yanzu haka kudin partyn  aka kawo mana" Dija nayi mata dariya ta fice itadai bata tanka ba sai game da takeyi da wayar Hajar Matar gdan da suke yammatancinsu, da sauri  sukaga Jiddarh ta nufo  parlourn ta zauna tana Mayar da numfashi saida  ta gama saita nutsuwarta tace “aikin babba ne Ma'uh yau me gayya me aiki ne yake tafe wlh yanacan saici mazu yakeyi kije yana jiranki" sosai taji qirjinta ya buga ta dago idanunta da suka kawo ruwa tace “don Allah kije kice  masa bananan" zare ido tayi tace “ban isaba wlh ki tashi kawai kije" sharewa  tayi ta koma  tayi kwanciyarta daqyar tasheta shima saida  Innah ta aiko da kanta sannan ta tashi tasa qaton hijjab dinta ta fito idanunta na fitar da ruwa ta nufi wajen ta jima tsaye kafin ya danna mata horn ta nufi inda  motar  take ya bude mata kamar  taqi shiga sai kuma ta tuna maganganun Innah haka ta zauna ya mayar da qofarsa ya rufe  ya juyo ya zuba mata ido tayi qasa da kanta tana wasa da yatsanta hawayenta na zuva saman santala santalan yatsunta,



Sun jima A haka kafin taji yaja  Wata doguwar ajiyar zuciya ya furzar da iska yace “meye yayi saura?" Jan numfashi tayi me hade da majina kukan da take ta qoqarin hadiyewa ya qwace mata yayi saurin zubanta ido tare da kamo hannunta qirjinsa na bugawa da qarfi kukan yana masa kuda a kunne yace “ya....ya salam meye kuma na kukan?" Sake rushewa tayi da kuka  gabadaya ya diririce baisan sanda ya hadata da jikinsa ba ya rungumeta sosai ta rintse idonta da qarfi ta sake qarawa kukanta sauti tace “nas....shiga ukuna wayyoh Innata ka sakeni don  Allah banas....." Numfashinta taji yana qoqarin daukewa ta shidewa tayi saurin bude idonta tsoronta ya nunku jikinta ya dauki rawa tunda take bata taba  ganin dan  iskan bayyane irin Aseem ba  Shikam babu abinda yakeyi sai tsotsar lips dinta daqyar ta hada  qarfinta ta tureshi tana jan  zuciya tare da sanya hijjab dinta ta rinqa dirzar bakinta tana kuka me taba  zuciya tace “Allah ya isana  mugu kwarto kawai......"

*_Oum Hairan_*

ZARRAHWhere stories live. Discover now