Zarrah

937 44 6
                                    

_*Zarrah*_


_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*


_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_*43-44*_

Mgnr ce ta maqale lkcn daya turo qofar ya shigo yanda yagansu a firgice ya bayyana masa lallai akwai abinda yake faruwa, engine idanunsa ya sauke akanta cikin farin glass din dake maqale a idanunsa fuskarsa babu alamun cewar ya taba dariya yace “idan kin gama kukan kizo office dina" juyawa yayi ya fice Jiddarh ta sauke numfashi tace “Allah saida gabana ya fadi da naga ya shigo please tashi kije amma ki aro juriya kada ki bari ya gane kinada matsala yanzu kawai ki dage da addu'a idan hakan ya kuma faruwa saimu san abinyi"
Jinjina kai tayi ta miqe ta dauki jakarta ta fito daga lab din ta nufi office dinsa ta qwanqwasa yabata izinin shiga yana zaune fuskarsa wasai da annuri kamar ba shine na dazun ba ya zubanta ido yana karkada biro a bakinsa yana tariyo yanayin daya kasance dz ita daren jiya, mayar da qofar tayi ta rufe ya sake saita zamansa ya aje biron hannunsa kujera taja ta zauna tare da sunkuyar da kanta hakanan ta tsinci kanda dajin matsananciyar kunyar kallon da yakeyi mata ya fahimci hakan shiyasa ya dauke idonsa daga kanta yace “kukan me kikeyi dazu?"


Dagowa tayi idanunta ya fada cikin nasa hakanan taji zuciyarta ta qara karyewa hawaye na shirin zubo mata yayi saurin dora hannunsa a bakinsa yace “waike yaushe zaki fara ganewa cewa bana qaunar kuka cewa nayi meye yasa kike kuka dazun?" Qasa tayi da idanunta cikin in'ina tace “na....nace maka bazan iyaba banida lfy kaqi kabarni na kwanta" murmushi yayi yanda tayi mgnr a shagwabe yabashi nishadi yace “nasan bakida lfy kawai naji zuciyata bata nutsu da zamanki a gdaba shiyasa nace ki taho nan nasan baki karya ba ki shiga wannan dakin akwai katifa ki kwanta ki huta amma ki tabbatar kinci abinci zanzo na dubaki"
Sosai taji dadin hakan domin wata muguwar kasala takeji a jikinta miqewa tayi ta shiga dakin abin mamaki dakine kamar a gda harda TV da freegde katifar an dameta da bedsheets, rufe qofar tayi ta cire hijjab dinta ita sai yanzu ma ta ga ashe rigar jikinta ma airmless ce doguwa ta hutawa, zama tayi ta bude tarkacen ledojin dake gurin kayan ciye² ne sunfi kala goma tea kawai ta hada tasha da plantain  ta miqe ta shiga bathroom ta hada ruwa tayi tsarki ta qarajin qwari ta dawo ta kwanta babu bata lkc kuwa bacci ya dauketa tanajin sanyi yana ratsata.


Bata farka ba sai uku ta wucce ta tashi a gurguje tayi alwala tayi sallah ta zauna tana lazumi taji ya murda qofar ya shigo ta dubi inda yake tsaye taji wani dam a qirjinta kawai ta kawar dakai ta maze abinta ganin yands tayi wlatsi da iskarsa ne yasashi matsawa ya tsaya akanta yace “me kika jorner electric kafin ki fito?"
Dagowa tayi ta dubeshi tace “ni kuma?" Jinjina mata kai yayi ta girgiza kai tace “aa ni ban jorner komi ba tasowata kenan a gado ksce na fito" jinjina kai yayi yace ok tashi muje" miqewa tayi ta dauki jakarta tabi bayansa suna tafe yana qwafa har suka shiga mota ya juyo ya dubeta yace “dazun aka kirani aka fadamin gobara ta tashi a part dinki komai ya qone....." Dafe qirji tayi cikin tashin hankali suna kallon juna hawaye ya zubo mata tace “garin yaya?" Yarfa hannu yayi yace “har yanzun abinda nakeson ganowa kenan" jan motar yayi suka tafi gabadaya jikinta yayi sanyi babu abinda takeyi sai hawaye tunaninta asararta kayan lefanta har sukaje Hausawa babu kalmar data shiga tsakaninsu yana sauketa ya juya ya tafi ta shiga gdan batayi ko sallama ba ta fada dakin Inna tana ganinta tasan ba lfy ba tace “subhanallahi ke kuma meye hakadin daga ina kike?"


Guri ta samu ta zauna tana share hawayenta tace “naje practical shine yanzu yaje daukoni yace wai gobara ce ta tashi a part dina babu abinda ya dauku" salati Inna tayi tace “yau naji sabuwar masifa gobara kuma Asma'uh garin yaya? Share hawayenta tayi tace “nima  bansani ba Inna ni kayan lefena ma nakeji duk fah ban dinka ba...." Daquwa ta watsa mata tace “qaniyarki dan gdanku shi bakiga asarar da yayi ba shima kukan kikaga yanayi saike baure sarkin kuka maza tashi kiyi alwala kiyi sallah kizo ga kunun tsamiya kisha"
Miqewa tayi ta fita inna nabin tafiyarta da kallo a ranta tana raya to dama haka tafiyarta take ko kuwa ciwo taji? Itadai bata tambayeta ba harta gama zamanta dare yayi sunata hirarsu da kishiyoyin Inna sukajiyo sallamarsa caraf suka amshe ya shigo suka gaisa ya dubeta yace “ki taso mu tafi dama nayi tunanin gyaran zai dauki zuwa gobe so amma dai an samu wata mafitar" Inna ce tace “to ubangiji ya kiyaye gaba amma abu baiyi dadi ba" miqewa tayi ta dauko tuwo a kula tace masa “qila ma tun safe bakasamu kaci abinci ba ga wannan naga kanason tuwo" yaji dadi sosai don kamar ta sani ta fada rabonsa da abinci tun shayin safe da yasha asmah ce ta karba ya ajiye kudi masu yawa Inna ta qwala masa kira yayi saurin ficewa ta kuwa ce “wlh bazamu karba ba Asma'u ki bashi abinsa mun gode nidai fatana a zauna lfy"


ZARRAHWhere stories live. Discover now