Zarrah

900 38 4
                                    

_*Zarrah*_


_*Fauziyya Tasiu Umar*_


_*Elegant Online Writter*_


_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_Am sorry Fans zan danyi mgn akan wani lamari ne, Yau na samu wani lbr daya sani a tunani, wai labarin zarrah labarin wani littafi ne da yayi tashe a lkcnsa, so duk ma wanda yake tunanin hakan inason ya sani Fauzah bata taba karanta littafi da suke mgn akai ba saboda haka duk abinda yayi kama da wancen arashi ne kawai aka samu amma ba copy nayi ba, daidai gwargwado da bazata nake rawa ban yarda na zama yar kanzagin wata ba ina fatan me fahimta zai fahimci cukurkudaddiyar Hausar._

_*51-52*_


Hakanan suka dauki hanya suka taho gabadaya yanayinsa yasawa Asmah tuntuni da kokwanto wannan wacce irin murna yakeyi da cikin daba nasaba anya babu ayar tambaya akansa kuwa? To amma idan hakane ya akeyi hakan take faruwa kuma da yaushe ne lkcn da hakan take faruwa? Tambayoyi ne da batada amsarsu dole sai binsa da ido kawai takeyi duk abinda ya gani yace mata zaki ci ko zakisha itadai kada masa kai kawai takayi a haka har sukaje gda.
Suna tsayawa ta sauka a motar ta nufi cikin gdan ko tuwon bata dauka ba sabida kokwanton daya sanya mata sosai yake tasirantuwa da ruhinta, a parlour suka tarar da mimee taja ta tsaya tare da ce mata "sannu Aunty Mimee ya jikinki?" Harara ta bita da ita tare da tsaki Safna qanwarta ce ta amsa da cewa "jiki da sauqi Aunty Asmee ya naki dazun Dr yake fadawa Jabir bakida lfy kema" sunkuyar dakai tayi tace "lahhh dan ciwon kai ne fah kuma namaji sauqi ina fawwaz?" Sunan danta kenan "yana gdansu Jabir da zan taho na biya shine ya maqalewa hajiyansa" murmushi tayi ta bude part din nata ta shige lkcn da yake shigowa ta mayar ta rufe shima zama yayi suka gaisa da Safnah tace "meye a kular ne Dr shafa sumarsa yayi yace "Tuwon Asmah ne munje gdansu shine tace tanaso muka taho dashi" daga haka ya miqe Safnah na cewa "Ahhh Lallai to Allah ya inganta...."


Buge bakinta Mimee tayi tace "ya inganta me?" Saurin cafewa Naja'at tayi tace "au kenan dake sauna ce baki gane me Allah zai inganta ba lallai ma Aunty Mimee to aini tun zuwan da nayi kwanaki na kawo miki aikin da kika kasa aiwatarwa na lura yarinyar nan ciki ne da ita dana fada miki kika kamamin dariya kina cewa batada wani ciki har cewa kike Aseem yayi miki Alqawarin bazai tsba kusantar taba har yanace miki shi qyanqyaminta ma yakeji" kasaqe mimee tayi tanajin bayanin kafin ta jinjina kai tace "aikuwa kwanaki na shiga part dinta zan aje kurtun asirin nan najita a bathroom tana kwara amai kambu aikam akwai bura uba a gdannan dole yau ayita ta qare wlh bazan yarda da cin amana ba"
Miqewa tayi a fusace tama manta da ita mara lfy ce ta nufi part din Asman lkcn suna tsaye rikici ya balle ta sashi a gaba tana masa kukan ita ya fadanta gsky meye hadinsa da cikin jikinta da yake rawar qafa akai, inda shikuma yayi kicin kicin yaqi sauraronta saima bala'i da yakeyi mata akan tace bszataci tuwon ba shikuma ya kafe tunda dansa yanaso saitaci.


Shigowar Mimee ne yasasu dubanta takaiwa Asmah raruma ta kauce da sauri aje flat din hannunsa yayi ya nufesu da suketa kallon kallo ya riqe mime yace "meye hakadin bakida hankali ne?" Shaqeshi tayi tace "eh bani dashi Aseem kace ma ni mahaukaciya ce bazan damu ba amma dai kasani ban manta da alqawarin da kayimin na har ka qare rayuwarka da wannan banzar matar taka bazaka hada shimfida da itaba Aseem ya akayi ta samu ciki idan har hakane matar da kace kana qyanqyaminta meye yakaika haike mata harda tsarabar ciki?....." Rufe mata baki yayi yana kallon Asmah da zuciyarta take zafi take tafasa tun fara mgnr ta mimee yace "kinga Mimee ba abinda kike zargi bane kije zamuyi mgn anjima....." Katseshi asmah tayi da cewa qarya ne Mimee abinda kike zargi ne cikine dani wata uku da sati daya kuma wlh mijinki nake zargi da biyo dare ya lalubeni ya dirkamin shi domin kuwa yanda yake rawar qafa yake fadawa duniya cewar inada cikinsa kawai ya isa shaida ba damuwata ka tsaya ka fadamin yanda akayi kayimin ciki ba aa kaje ka sanar da matarka yanda akayi kaci amanarta idan kayi mata bayani sai na dora maka da Allah ya isa kuma wlh kaji na rantse zaman gidanka muddin baka fahimtar dani yanda akayi ka haihu a ragaya ba to na gamashi har gaban abada"


ZARRAHWhere stories live. Discover now