Zarrah

854 31 7
                                    

_*Zarrah*_

_*Fauziyya Tasi'u Umar*_

_*Elegant Online Writer*_


_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_


_*47-48*_


Shigewa tayi daki  ta mayar da qofarta ta kulle yayi murmushi yaci abincinsa yayi hani'an ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya zauna a parlourn qasa ya kunna kallo yana kallon qwallo Mimee ta fito taci  uwar kwalliya ta nemi guri kusa dashi ta zauna tana satar kallonsa mgn takeson  yimasa amma yanda ya hade rai yayi kicin kicin waya  ya dauka  ya kira layin  Asmah ta fito daga wanka tanasa rigar bacci ta gama shafe  jikinta da turare dagawa tayi ta kara a kunnenta yace “ki shiga dakina ki dau komai fice system dita  ki kawo min" hararar wayar tayi ta aje ta hade gashinta ta daure ta sakeshi a baya hijjab tasa ta shiga ta dauko  masa system din ta nufi parlourn tana baza uban  qamshi  janyo qofar tayi ba qaramin faduwa gabanta yayi ba ganinsu zaune da Mimee a parlor jan  qafarta tayi daqyar ta nufi parlourn  tana ganin yanda Mimee ta wani tabe baki.
Rusunawa tayi ta miqansa a ladabce yakai hannu  tunanin ta karba  zaiyi kawai ya janyota jikinsa ya hadata a jikinsa ya tura hancinsa a wuyanta yace “bakijin zafine Baby ki cire  hijjab dinnan" kallon idonsa tayi da tsananin mamaki kashenta ido yayi ya zame mata hijjab din yana kallonta gabadaya jikinta ya mutu  shima jin nasa jikin yakeyi a mace yakai hannunsa saman wuyanta yace “kinyi min kyau kamar  Sarauniya....." Miqewa Mimee tayi taja  uban  tsaki tayi ciki tare da banko  qofa  ajiyar zuciya Aseem yayi ta janye jikinta ta miqe yayi saurin sake janyota ya miqe shima ya dagata cak  ya nufi part dinta da ita ta janye tana qoqarin direwa ya sauketa yace.


“Saboda kinga  inajanki a jiki zakike yimin hauka ko kauce ki bani guri shashasha kawai" jan  jiki tayi ta fice daga dakin ta nufi nata ya fada gadon ya kwanta  yana miqa ya rasa baqar jarabar dake damunsa akan yarinyar yakasa jurewa yau dinma so yake yajita a jikinsa

Juyi yayi ya janyo pillow ya rungume a ransa yanason tashi yakai mata ziyara yana kuma tsoron ta rutsashi hakanan dai ya kwana a daddafe da safe ta shirya domin zuwa practical ta shiga kitchen ta hada  break tana karyawa ya shigo kitchen din bai kulata ba ya dauki cup ya hada  tea ya zuba soyayyen dankali  ya fita parlour ya zauna yaci ya qoshi ya miqe zai fita itama ta fito ya dubeta kawai ya watsar itanma  bata saurareshi ba ta nufi daki ta dauko  hijjab dinta tasa ta fito ga mamakinta taganshi tsaye tabi ta gefensa zata wucce ya riqo hannunta ya juyota ta qarfi yace “ba a koya miki  gaisuwa bane a gdanku?"
Kawar dakai gefe tayi tace “inajin" baiyi tunanin amsar da zata bashi ba kenan ta janye hannunta ta fice daga parlourn nata  ta shiga babban parlour gimbiyar tana zaune a dinning tanata danna bread da farfesun naman kaza Asmah ce  tace mata “barka da sfy" bata amsa ba  dama batasa a ranta zata amsa ba ta fice da Sauri shima ya fito ya wucceta, takaici ya cika Mimee ta miqe tace “kan ubancan wato gadi ma zanyi musu a gdan duk sun fice sun barni wlh nima  ficewa zanyi" dakin ta nufa ta zaro mayafi ya fito tana kada  mukulli lkcn motarsu ta fice, kowa sai huci yakeyi zuciya fal  qunci sunayin parking ta bude motar  ta fice.


Ta nufi Lab Jiddarh ta gani zaune ta miqe da Sauri tace “inata kiran  wayarki bata shiga meye ya hanaki zuwa jiya" zama sukayi tace “ki bari kawai abubuwa sun faru da yawa  jiya yini nayi banida lfy  yau kam da sauqi" jinjina kai Jiddarh tayi tace “ai jiya naje nayiwa Inna magana tace zatasa a karbo miki  magani, hamdala tayi sukaci  gaba da hirarsu da aikinsu wajen hudu ya shigo yana kiranta ta miqe tanacin magani Jiddarh tabita da ido shidinma ya fahimci hakan yace “menene?" Tsuke fuska tayi tace “babu komai" murmushi yayi yace “idan kin gama ki fito mu  tafi" komawa tayi ta dauko  Jakarta Jiddarh tace “kinga ki saki ranki  yanzu bada bane kina tare da kishiyarki komai kikayi idonta akai"
Kawar dakai tayi ta fice yana Mota yana jiranta ta shiga suka tafi suna  isa ya bude ya fito ya bude mata ta fito yaya.


ZARRAHWhere stories live. Discover now